Ibn Taimiyya da tauhidi Ma’anar al’arshi , a Alukr’ani

 
 
A ainahin lugar larabci al’arshi yana nufin gado, amma da yake shi,larabci yana da salo- salo, da hanyoyi na yin Magana, idan wata kalma tana da wata ma’ana ta asali, wacce ake ce mata(الحقيقة) , to idan aka yi amfani da ita ba lallai ba ne ya kasance cewa ana nufin wannan ainahin kalmar ba, misali a kalmar zaki ana amfani da ita ne a kan Zaki na asali, wato wannan jarumar dabbar da take a daji, amma idan aka sami wani mutum jarumi sadauki, sai a siffanta shi da zaki na ainahi, sai a kira shi da zaki, ba wai don shi dabba bane, a a saboda shi jarumi ne, don haka sai ya kasance idan aka ambace shi da zaki to haka yana zama yabo a gareshi, wannan kuwa shi ne tsarin da yaren labci yake a kansa.
Idan muka lura da wannan magana da kyau za muga cewa Allah (T) yana cewa: (haƙiƙa mu ne muka saukar da Alƙur’ni da yare na larabci), to tun da kuwa Alƙur’ani balarabe ne,! To ashe kuwa yana kan tsarin yadda larabawa suke magana.
Don haka duk ayoyin da Allah yake cewa: ( Allah ya  daidaita a kan al’arshi), ba yana nufin shi Allah jiki ne da yake zaune a kan wani gado ba, domin shi Allah mawadaci ne, ya wadata a buran zama, ko keɓanta a wani waje.
Saboda haka idan muka dubi waɗanan ayoyi da kyau za mu ga cewa; suna nufin Allah shi ne mabuwayi, mai iko a kan duk halittarsa, komai yana ƙarƙashin mulkinsa.</spa

AttachmentSize
File d27bf40c2d631a8dd8d5ed702c5379ef.mp434.32 MB

Ƙara sabon ra'ayi