SAKIFA 1

SAKIFA 1

Imamanci da Khalifanci bayan wafatin Annabi   suna nufin wani aiki ne kuma nauyi ne daga Allah, irin aiki da nauyin da ya rataya a wuyan Annabawa, kuma wannan aikin mai zarcewa ne har  karshen duniya.                        

Kokum muce Imamanci da khalifanci na nufin jagoranci da shugabancin al`umma ta fuskar al`amuran addini da  duniya kamar tsayar da addini, kare shi, nuna yadda za`a aikata shi, bada fatawa kan duk abin da ya shafi mas`aloli da hukunce-hukuncen shari`ar musulunci, da kuma tafiyar da al`amuran gwamnatin muslunci da duk abin da ya shafi al`umma, domin alaka tsakanin Khalifanci da Annabcta shi ne: Khalifanci ci gaba ne da isar da sakon da Annabi ya zo da shi, da kuma kare shi daga gurbacewa.                       

Sharudan da suka wajaba Imami ko khalifa bayan Annabi ya cika su ne: ya kasance MA`ASUMI mai Ilimi daga Allah, kuma ba mutane ke da hakkin zabir Imami ko khalifa ba, kamar yadda ba su da hakkin su zabi Annabi, Allah kadai ke da hakkin ya zaba kuma ya nada wanda ya dace da jagoranci tare da kiyaye wannan addinin da kuma isar da shi inda bai je ba. A nan ne aka sami sabani babba tsakanin Shi`a da Sunna.                                                 

Shin Annabi ya nada khalifa, ko yayi wafati ne ya bar al`umma babu jagora?

A cikin Alkur`ani Allah(swt) ya umarci mutane cewa:

{Allah ya wajabta muku cewa idan mutuwa ta zo wa dayanku, in ya bar wani alkhairi to yayi wasiyya da-ma`arufi- kyakkyawa ga iyaye da makusanta wannan kuwa hakki ne a kan masu takawa}. Lallai babu wani alkhairi da ya wuce wannan sako na addini da Ma`aiki Annabi Muhammadu (saww) ya zo da shi daga Allah,

AttachmentSize
File 13136.f.hoosa_.mp435.13 MB

Ƙara sabon ra'ayi