IMAMANCI (1)
Wasu suna jifan Annabi (saww) da cewa ya bar duniya ba tare da ya aikata wasu muhimman abubuwa da suka zamar masa wajibi ya aikata ba, misali ana cewa Annabi (saww) ya bar duniya bai haɗa Alƙur’ani ba, wato haka ya bar Alƙur’ani a warwatse ba tare da ya haɗa shi, sai bayan ya yi wafati ne a lokacin halifosin da suka zo bayansa, su ne suka yi tunani suka ga hatsarin da yake tattare da rashin haɗa Alƙur’ani, sai suka haɗa.
Wannan magana babu ƙamshin gaskiya ko kaɗan a cikinsa, somin kuwa wannan Alƙur’ani wanda yake hannun al’ummar musulmi shi ne dai Alƙur’anin da Allah ya saukar fiyayyen halitta Annabi Muhammad ( saww) kuma Annabi bai bar duniyannan ba sai da ya haɗa shi kamar yadda muke gani a yanzu.
Sannan ana cewa Annabi (saww) ya bar duniyannan ba tare bar musu khalifa ba, don haka ya bar al’ummarsa kara zube ba, ba tare da ya sanya musu, wanda zai zama khalifansa ba.
Wannan maganar ita ma bata da kƙanshin gaskiya ko kaɗan, domin kuwa babu shakka ayoyi da riwayoyi, da kuma litattafan tarihi sun tabbatar da cewa lallai Annabi (saww) ya bar mana khalifansa kuma shi ne imam Aliyyu ɗan Abu Ɗalib (as)
Attachment | Size |
---|---|
58687218daca3e2209abca3b42676d90.mp4 | 21.02 MB |
Ƙara sabon ra'ayi