Ibn Taimiyya da tauhidi Siffofin Allah (4)
A cikin littafin Ibn Taimiyya mai suna Alfatawal hamawiyya shafi na 15 Allah na zama a kan al’arshi yana zaune,... Allah ya da gaɓɓai, kamar ido da hannuwa da kafafuwa, illa iyaka kawai hannuwansa ba irin na sauran mtane bane.
Wannan magana tasa bata da ma’ana, domin indai har ka ce Allah yana da hannu, amma kuma ka ce ba kamar sauran hannuwa ba, to kamar ka ce ba ƙafar baya ba cinya, domin kowane mutum hannusa ba irin na kowa bane, musamman ma a wannan zamani za a fahimceta sosai inda ake ɗaukar hoton yatsu, inda yatsan kowane muyum babu wani yatsa da ya yi kama da shi.
Amma dai duk hannu hannu ne, to ashe cewa Allah yana da hannu, ba irin sauran hannuwa ba ba sbhi da wata ma’ana, kuma bai wanke wannan gurbatacciyar aƙida ba ta tashbihi.
Attachment | Size |
---|---|
300bea1d2afa5030d4e54dac70782584.mp4 | 20.01 MB |
Ƙara sabon ra'ayi