TARIHIN SAYYIDA FAƊIMA (AS) (11)
Yunus ya ci gaba da cewa: Sannan Imam sadiƙ ya sake cewa : shin ka san saboda menene tafsirin sunan Faɗima? Sai sai na ce: Bani labari ya shugabana! Sai Imam ya ce: an yantata daga sharri (babu wani sharri da zai sameta.
Yunus ya ce gaba da cewa: Sannan Imam Ya ce: ba don Amirul Muminina ya auri Faɗima ba da ta kasance bata da wani kufu'i – tsaran aure har zuwa ranar alƙiyama).
Wasu daga laƙabobinta:
Batulu (wace bata yin jinin haila) البتول
Shahidiya
Mafificiya
Haura'ul insiyya (Matar aljanna a cikin mutane)
Mai tsoran Allah Mai tsantsar tsarki
Mai yawan ilimi
wacce aka zalunta
Wacce aka kwacewa Haƙƙinta
Zaɓaɓɓiya
Abar taimko
Mai karamci
Rabautacciya
Shugaba.
Attachment | Size |
---|---|
11656-f-hoosa.mp4 | 34.94 MB |
Ƙara sabon ra'ayi