Sakon Jagora Imam Khamenei Ga Maniyyata Hajjin Bana (1437-2016)
Ya 'yan'uwa musulmi maza da mata a duk fadin duniya.
Aikin Hajji a wajen musulmi wani lokaci ne abin alfahari da daukaka a idanuwan halittun Allah, haka nan wani lokaci ne mai haskaka zukata da kuma kankantar da kai a gaban Allah Madaukakin Sarki. Hajji dai wata farilla ce saukakka daga Ubangiji kana kuma ta al'umma. A bangare guda umurnin nan na: "Sai ku ambaci Allah kamar ambatarku ga ubanninku, ko kuwa mafi tsanani ga ambato" (Suratul Bakara 2:200), da kuma "Kuma ku ambaci Allah a cikin kwanuka kidayayyu" (Suratul Bakara 2:203), sannan a bangare guda da maganar Allah Madaukakin Sarki cewa: "Wanda Muka sanya shi ga mutane alhali kuwa mazauni a ciki da bakauye daidai suke" (Suratul Hajj 22:25), dukkanin su suna nuni ne da bangarori daban-daban kana kuma marasa karshe na aikin Hajji.
A yayin wannan farali maras tamka, tsaro na lokaci da waje da ake da shi yana haskaka zukatan mutane tamkar wata bayyananniyar alama da kuma tauraruwa mai haske sannan kuma da fitar da Mahajjaci daga killacewar rashin tsaron da azzaluman 'yan mulkin mallaka suka haifar da a koda yaushe ya ke barazana ga dukkanin bil'adama, sannan kuma da taimaka wa dan'adam wajen ya dandani dadin kwanciyar hankali da tsaro na wani kayyadadden lokaci.
Hajjin (Annabi) Ibrahim wanda Musulunci ya gabatar wa musulmi a matsayin wata kyauta, ya kasance wata alama ta daukaka da kusaci da Ubangiji da hadin kai da kuma girma. Haka nan kuma yana tabbatar wa makiya da masu bakar aniya irin girma da daukaka ta al'ummar musulmi da kuma dogaronsu ga karfi na Ubangiji na har abada, kamar yadda kuma yake bayyanar da tazarar da take tsakanin musulmi da tushen fasadi da kaskanci da rauni da azzalumai da masu tinkaho da karfi na duniya suka tilasta wa bil'adama.
Aikin hajji na Musulunci kuma ma'abocin tauhidi wata alama ce ta "masu tsanani ne a kan kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu" (Suratul Fath 48:29). Lalle waje ne na barranta daga mushirikai, kana kuma na soyayya da hadin kai tsakanin muminai.
Wadanda suka takaita aikin hajji zuwa wata tafiya ta ziyara da yawon shakatawa sannan kuma suka boye kiyayyar da suke yi da al'ummar Iran muminai ma'abota juyi da sunan "ana kokarin siyasantar da aikin Hajj" su din nan kananan Shaidanu ne kaskantattu da suke tsoro da karkarwa don kada manufofin Babbar Shaidaniya –Amurka- su fada cikin hatsari. Mahukuntan Saudiyya wadanda a wannan shekarar suka kange (mutane) daga tafarkin Allah da Masjidul haram da kuma hana muminan alhazan Iran masu girma daga isa ga Dakin Abin Kauna, su ne kaskantattu kuma batattun mutane wadanda suke tunanin cewa ci gaba da zamansu a kan kujerar mulkin zalunci ya damfara ne da kare azzalumai ma'abota girman kan duniya da kuma hadin gwiwa da Sahyoniyawa da Amurka da biya musu bukatunsu. A wannan tafarki kuwa ba sa jin kunya aikata duk wani ha'inci da cin amana.
Kusan shekara guda kenan a halin yanzu da faruwar abin da ya faru a Mina mai sosa rai, inda dubban mutane suka rasa rayukansu cikin tsananin rana da kishirwa a ranar Idi kuma sanye da tufafi na harami. Kafin haka da kadan, an kashe wasu mutane a Masjidul Haram a daidai lokacin da suke cikin ibada da Dawafi da Sallah. Ko shakka babu mahukuntan Saudiyya suna da laifi cikin dukkanin wadannan abubuwa guda biyu da suka faru, hakan kuwa wani lamari ne da dukkanin wadanda suka kasance a wajen da kuma masu sa ido, masu sharhi da kwararru suka yi ittifaki a kansa. Wasu manazartan ma sun tafi a kan cewa akwai ganganci cikin lamarin. Abin da babu kokwanto cikinsa shi ne cewa akwai sakaci da nuna halin ko in kula wajen ceto rayukan wadanda suka sami raunuka wadanda zukatansu suke cike da kauna a ranar idin babbar salla, harsunan su kuma suke cike da ambaton Allh da karatun ayoyin Ubangiji. Mujiriman jami'an Saudiyya masu kekasashshen zuciya sun kulle wadanda suka sami raunukan tare da gawawwakin wadanda suka rasu cikin kullallun kwantenoni inda suka kashe su a matsayin shahidai maimakon yi musu magani da taimaka musu kai ko hatta ma da ba su ruwa don jika bakunansu da suka bushe saboda kishirwa. Dubun dubatan iyalai daga kasashe daban-daban sun rasa masoyansu da sanya al'ummominsu cikin juyayi. A Iran kawai kimanin alhazai dari biyar ne suka yi shahada. Har ya zuwa yanzu zukatan wadannan iyalan suna cikin bakin ciki da juyayi, kamar yadda su ma al'ummomin wadannan kasashe suke cikin juyayi da bakin cikin.
Maimakon mahukutan Saudiyyan su nemi uzuri da nuna nadamarsu da kuma hukunta wadanda suke da laifi kai tsaye cikin wannan lamarin, amma cikin dukkan wauta da rashin kunya sun ki amincewa hatta da kafa kwamitin bincike na kasashen musulmi. Haka nan maimakon su tsaya a matsayin wadanda ake zargi, sai suka zama masu tuhumar wasu ma, inda cikin dukkanin lalacewa da rashin sanin ya kamata suka bayyanar da tsohuwar kiyayyar da suke yi da Jamhuriyar Musulunci da dukkanin wata tuta da aka daga ta fada da kafirci da girman kai.
Kafafen farfagandarsu kama daga 'yan siyasarsu wadanda dabi'a da mu'amalarsu da Sahyoniyawa da Amurka abin kunya ne ga duniyar musulmi, zuwa ga malamansu marasa tsoron Allah da cin haramun wadanda a fili suke fitar da fatawowin da suka saba wa Littafin Allah da Sunnan (Ma'aiki) da kuma kafafen watsa labaransu wadanda hatta ka'idojin aikinsu ba su hana su yada karya ba, sun ci gaba da kokarin nuna cewa laifin na Jamhuriyar Musulunci da kuma zarginta da hana mahajjatan Iran tafiya aikin hajjin bana.
Wadannan mahukunta masu kirkiro fitina, wadanda ta hanyar kirkira da kuma ba da makamai wa kungiyoyi 'yan ta'adda masu kafirta musulmi, sun sanya kasashen musulmi cikin yakin basasa, kisa da zubar da jinin wadanda ba su ci ba su sha ba da kuma zubar da jinin mutane a kasashen Yemen, Iraki, Sham (Siriya), Libiya da sauran kasashe. Wadannan 'yan siyasa marasa tsoron Allah suna mika hannayen abokantaka ga haramtacciyar kasar sahyoniyawa 'yan mamaya, a daidai lokacin da kuma suna rufe idanuwansu daga wahalhalu masu tsanani da Palastinawa suke ciki sannan kuma suna baza zalunci da cin amanarsu a kan garuruwa da kauyukan kasar Bahrain. Su kuwa wadannan shugabanni marasa addini da lamiri, wadanda suka haifar da abin da ya faru a Mina sannan kuma ta hanyar fakewa da sunan masu hidima wa haramai guda biyu suna keta hurumin haramin Allah da kashe bakin Allah Mai Rahama a ranar Babbar Salla a Mina, sannan kuma kafin hakan a Masjid al-Haram, su din ne a halin yanzu suke maganar bai kamata a siyasantar da lamarin hajji ba sannan kuma suna zargin wasu da aikata babban sabon da su da kansu ne suka aikata da kuma yin sanadiyyar faruwarsa.
Lalle su ne babbar alamar ayar nan ta Alkur'ani mai girma da ke cewa: "Kuma idan ya juya sai ya yi gaggawa a cikin kasa domin ya yi barna a cikinta, kuma ya halaka shuka da 'ya'yan dabbobi. Kuma Allah ba Ya son barna. Kuma idan an ce masa: "Ka ji tsoron Allah, sai girman kai da yin zunubi ya dauke shi. To abin da yake mai isarsa Jahannama ce. Kuma hakika, shimfida ta munana" (Suratul Bakara 2:205-206)
Rahotanni suna nuni da cewa a wannan shekarar ma bayan sun hana alhazan Iran da ma na wasu kasashen zuwa aikin hajjin, sun sanya alhazan da suka tafi hajjin na bana karkashin gagarumin sanya ido ta hanyar amfani da na'urorin bincike da leken asiri na Amurka da Sahyoniyawa, inda suka sanya Dakin Allah mai aminci cikin rashin aminci ga kowa.
A saboda haka ya hau kan duniyar musulmi, shin gwamnatoci ne ko kuma al'ummominsu, su fahimci mahukuntan Saudiyya sannan su yi musu kyakkyawar fahimtar yanayinsu ta keta hurumin aabubuwa masu tsarki da kuma bautar abin duniya. Kada su bar wadannan mahukuntan su sha daga irin danyen aikin da suka aikata a duk fadin duniyar musulmi ba. Haka nan kuma wajibi ne su yi tunani sosai dangane da batun kula da haramomin nan guda biyu masu tsarki da kuma lamarin hajj saboda irin wadannan dabi'u na zalunci da cutar da bakin Allah (na wadannan mahukunta na Saudiyya). Nuna gazawa wajen sauke wannan nauyin zai ci gaba da sanya al'ummar musulmi da makomarsu cikin hatsari da matsaloli.
Ya ku 'yan'uwa musulmi maza da mata, tabbas a wannan shekarar alhazan Iran ma'abota shauki da tsarkin zuciya ba su sami halartar aikin hajji ba, to amma zukatansu na nan tare da alhazan da suka fito daga dukkan duniya, suna cikin damuwar yanayinsu, sannan suna addu'ar cewa kada Allah Ya sa wadannan la'anannun bishiyoyi na dawagitai ta samu damar cutar da su. Ku tuna da 'yan'uwanku maza da mata mutanen Iran cikin addu'oinku da ibadunku da munjatinku, haka nan ku yi addu'ar magance matsalolin da al'ummar musulmi suke fuskanta da kuma gutsure hannayen ma'abota girman kai da sahyoniyawa da 'yan amshin shatansu daga cutar da al'ummar musulmi.
Ina jinjinawa shahidan Mina da Masjidul haram na shekarar da ta gabata, da shahidan Makka a shekarar 1987, ina mai rokon Allah Madaukakin Sarki da yayi musu gafara da rahama da kuma daukaka matsayinsu, kamar yadda kuma na ke mika gaisuwa da sallama ta ga shugabanmu Bakiyatullah al-Aazam (rayukanmu su zamanto fansa a gare shi) ina mai neman addu'oinsa abin amsawa wajen tabbatar da daukaka ga al'ummar musulmi da kuma tseratar da su daga fitina da sharrin makiya.
Dukkanin nasarori suna wajen Allah ne sannan kuma a gare shi dukkanin dogaro take.
Sayyid Ali Khamenei
Zil Ka'ada, 1437 (Satumban 2016)
Ƙara sabon ra'ayi