Hare-Haren Jiragen Saman Yakin Saudiyya Sun Kashe Daruruwan Yara A Kasar Yamen

Hare-Haren Jiragen Saman Yakin Saudiyya Sun Kashe Daruruwan Yara A Kasar Yamen

Asusun Kula da Mata da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya {UNICEF} ya bayyana cewa; Yawan kananan yara da suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren wuce gona da iri da jiragen saman yakin masarautar Saudiyya suke kai wa kan kasar Yamen sun haura 900 a cikin shekarar ta da gabata ta 2015.

 

 A bayanin da Asusun Kula da Mata da Yara na Majalisar Dinkin Duniya {UNICEF} ya fitar a yau Litinin ya bayyana tsananin damuwarsa kan yadda ake ci gaba da samun hasarar rayukan kananan yara a kasar Yamen sakamakon hare-haren wuce gona da irin jiragen saman masarautar Saudiyya kan kasar.

 

Bayanin na UNICEF ya tabbatar da cewa; A cikin shekarar da ta gabata ta 2015 kananan yara akalla 900 ne suka rasa rayukansu a kasar Yamen, wanda idan aka kiyasta da shekara ta 2014 an samu nimkuwar adadin yaran da suka mutu har sau bakwai.

 

Har ila yau Asusun Kula da Mata da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa; Kashi daya cikin uku na kananan yara da aka kashe a kasar ta Yamen 'yan shekaru daya ne zuwa hudu a duniya, kuma a kawai jarirai a cikinsu.

Ƙara sabon ra'ayi