Chadi : An Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa Cikin Lumana

Rahotanni daga kasar Chadi na cewa an gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na farko a cikin kwanciyar hankali da lumana.

 

bayanai sun nuna cewa babu da wasu matsaloli na-azo- a- gani da aka fuskanta a yayin zaben a duk fadin kasar, kuma an samu fitowar jama'a yadda ya kamata.

'Yan takara 13 ne dai ciki har da shugaba mai barin gado Idriss Deby Itmo daya shafe sama da shekaru 25 kan karagar mulki suka fafata a zaben na jiya.

Shi dai Idris Derby, dan shekaru 63 na neman wa'adi na biyar ne domin ci gaba da mulkin wannan kasa.

Saidai Jagoran 'yan adawa Saleh Kebzabo ya ce, yana da shaidar gagarumin magudin da aka aikata a lokacin zaben.

A cikin kwanaki 15 masu zuwa ne ake san ran bayyana sakamakon zaben.

 

 

 

Ƙara sabon ra'ayi