Niger: Boko Haram sun hallaka fararen hula 3 a jihar Diffa
Kimanin fararen hula 3 ne suka rasa rayukan su sanadiyar harin kunar Bakin wake da 'yan boko haram suka kai cikin wata motar siffiri a jihar Diffa
A kalla fararen hula uku ne aka kashe wasu da dama kuma suka ji rauni a wani harin kunar bakin wake da mayakan kungiyar 'yan ta'adda Boko Haram guda byu suka kai a wannan Talata kusa da garin Diffa,dake kudu maso gabashin Nijar, kusa da kan iyaka da Najeriya.
'Yan kunar bakin wakn biyu sun tayar da bom din dake jikinsu yayin da suke cikin wata motar sufurin jama'a a kan hanyar dake zuwa Diffa, da nisan kilomita 20 daga garin Booso mai iyaka da tarayyar Nijeria.
Duk da irin jami'an tsaron kasa da sama dake sintiri a wannan yanki, a hakan bai hana 'yan kungiyar boko haram din kai wannan harin ba
kimanin shekara guda kenan da jihar ta Diffa ke fama da rikicin kungiyar Boko haram, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da dama.
Ƙara sabon ra'ayi