Shafin yada labarai na Macedonia Online ya bayar da rahoton cewa, wasu daga cikin fitattun 'yan jarida akasashen austria da kuma Italiya sun fitar da bayanai na hadin gwiwa da ke yin kira ga gwamnatocinsu da su dauki matakin haramta addinin musuluncia wadannan kasashe na turai.
Karla Amina mai magana da yawun cibiyar musulmi ta kasar Austria ta bayyana cewa, abin da wadannan 'yan jarida suka yi ya saba wa tsarin mulkin kasar Austria, domin kundin tsarin mulkin kasar ya amince da addinin muslunci a matsayin halastaccen addini a kasar.
Masu kiyayay da addinin muslunci a cikin kasashen turai suna ta kara kaimi wajen ganin an soke addinin muslunci a cikin kasashensu, tare da kora ko kuma takura ma musulmi, tun bayan kaddamar da hare-haren birnin Paris, inda lamarin ya kara tsananta bayan kai harin birnin Brussels.
Ƙara sabon ra'ayi