Harin 'yan ta'adda kan matatar man A Libiya

Kakakin Matatar Man Bida dake Birinin Bangazi ya sanar da kaiwa matatar mai din hari

 

 

Kamfanin dillancin Labaran Reuteus ya nakalto Ali Alhasi mai magama da yawun kamfanin matatar Man Bida dake Birnin Bangazin Libiya ya sanar da cewa mayakan kungiyar 'yan ta'addar ISiS cikin motoci 12 a daren jiya Assabar sun kai hari a matatar man, yayin gumurzu tsakanin masu gadin matatar man da mayakan 'yan ta'addar ISIS din, masu gadin matatar biyu ne suka rasa rayukansu.

 

Ali Alhasi ya kara da cewa a karshen al'amarin, masu gadin matatar man sun samu nasarar dakile harin.

 

Kungiyar 'yan ta'addar Da'ishi ko ISIS na da dubun dubatan mayaka a kasar Libiya, inda yanzu haka take rike da wasu yankuna na kasar, kuma hakan ya janyo cikas ga harakokin tsaron kasar.

Ƙara sabon ra'ayi