Masar Ta Bukaci A Mika Mata Mutumin Daya Karkata Akalan Jirgin Sama
Gwamnatin Masar sun bukaci mahukuntan kasar Cyprus dasu mika mata mutumin nan daya karkata akalan jirgin nan na EgyptAir zuwa filin jirgin Larnaca a kudancin kasar jiya Talata.
Babban mai shigar da kara na Masar ne Nabil Ahmed Sadek ya mika wannan bukata ga mahukuntan na Cyprus dake tsare da mutumin mai suna Seif al-Din Mohamed Mostafa.
Mutumin wanda dan asalin kasar ta Masar ya bayana a gaban kotun Cyprus, kuma ana tuhumar sa da karkata jirgin sama da yin garkuwa da mutane.
Masu bincike dai sun ce lamarin baya da wata alaka da aikin ta'adanci.
Yan sandan Cyprus sun ce maharin dan shekaru 58 ya nemi izinin sauka filin jirgin Larnaca da safiyar jiya Talata, tare da baiwa fasinjojin da ke cikin jirgin kirar A-320 damar ficewa amma tare da yin garkuwa da wasu Turawa 5 bayan sun sauka a Larnaca.
Ƙara sabon ra'ayi