Hirar 'yan jaridu da Shaikh Hamzah Muhammad Lawal

YAN JARIDU:Allah ya gafarta Malam me zaka ce dangane da wannan kudiri na gomnatin Kaduna na sanya dokan hana wa’azi a fadin jihar?
SHAIKH HAMZAH:A’uzu billahi minash Shaidanir Rajim,Bismillahir Rahmanir Rahim,Wasallallahu ala Muhammadin wa alihid Dayyibinad Dahirin wa As’habihil Muntajabin.A asali bai kamata a ce ita gomnati tana da wani alaka da al’amuran addini ba,kowane irin addini ne a cikin wannan kasar,saboda tsarin mulkin Nigeriya yace Demokradiyya ake yi.
Sannan daka cikin rukunan Demokradiyya akwai yanci na addini,sannan akwai yanci na alaka wato FREEDOM ASSOCIATION,sannan kuma akwai yanci na mutum yayi tunani akan abinda yake so yayi tunani.Kawai dai ita gomnati ba ta da danganta da addini,saboda haka bai kamata sun din ga shiga safgogin addini,wannan a mataki  ta daya kenan.
Amma a mataki na biyu,akwai cewa akwai kungiyoyi masu yawa a cikin kasar nan wadanda suke na addini ne da wadanda suke kuma ba na addini bane sunyi register da hukuma wadda aikin ta shine yima kungiyoyi wadanda suke ba na gomnati ba register.To!idan aka samu wasu gungu na mutane wadanda suke sun yi register da wannan hukuma wanda ake ce ma ta CORPORATE AFFAIRS COMMISSION ya zama an basu certificate,to babu wani wanda ya isa kuma yace kada su yi aiki,saboda kafin a ba mutum ko jama’a  register a wannan hukumar dole sai sun kai tsarin mulkin su.Tsarin mulkin nan kuma dole sai ita hukumar ta gani ta sanya stamp akan kowanne shafi shafi,tun daga shafin farko har zuwa karshe na wannan Constitution na su wanda yake nufin idan aka basu register an zartar da wannan tsarin mulkin kenan.To ba zai yiwu ba a zo a ce an samu wani QAIDI akan ayyukan ita wannan jama’a din ba,zai zama akwai karo sosai,kuma duk lokacin da aka samu karo tsakanin dokokin kasa gabaki daya da wasu dokoki rassa-kaman na jiha ko kananan hukumomi ko abin da yayi kama da wannan-to dokokin kasa ko dokokin tsarin mulki sune suke zama a birbishin wadannan dokokin.Kenan ya kamata ya zama a birbishin wannan kuduri wanda ake so a yi,na biyu kenan.
Na uku,abinda yafi muhimmanci sosai shine cewa kaman ance da Jamatu Nasril Islam ne da CAN wato Christian Association of Nigeria su zasu yi tantancewa.Wadannan basu cancanci su zama su zasu tantance wane ne ya kamata yayi wa’azi a addinin Musulunci da addinin kirista.Sannan basu isa su tantance wane ne malami wane ne ba malami ba a cikin addinin Musulunci da Kirista?Su wadannan din wato Jamatu da CAN su ma irin wadannan kungiyoyin ne da suka yi register da gomnati kuma babban aikin su shine kaman a ce su tattaro wadannan addinan guda biyu,aikin su ba shine cewa wannan Malami ne wannan ba Malami bane ko kuma wane ne ya cancanta yayi wa’azi wane bai cancanta yayi wa’azi ba,saboda haka asasi ba shine a basu su zama masu tantancewa ba.
Sannan na hudu –wannan duk gabaki dayan shi ina kallon shi ne ba da dangantaka cewa ni jingina ya zuwa ga wani waje ba,ina kallon shi ne a matsayin dokoki da kuma hankali –Mutum zai iya cewa kila babu laifi ya zama an samu hukuma wadda take kula da sha’anonin wa’azi da kuma sha’anonin masu malantaka a kasa,in ya zama cewa babu wani abu a ciki wanda aka boye,daya kenan.Sannan kuma in ya zama cewa kowanne mutane  ahalin su za a ba su tantance su.Abinda nake nufi a nan wurin shine cewa dole abin ya zama fili tukuna,na daya kenan.Sannan na biyu ya zama cewa idan kana Malikiyyah ne,ba wanda ya isa yace kai Malami ne a cikin Malakiyya ko kuma ka cancanci kayi wa’azi a cikin Malikiyya sai ba Bamalike,wannan a bangaren fiqhu kenan.
A bangaren tarbiyya,in misali a ce kai dan Darika ne(Kadiriyya ko Tijjaniyya ko Naqshabandiyya ko Shaziliyya ko ma wacce irin Darika ce )dole ya zama ahalin wannan makarantar sune ya kamata su zauna su tantance ka su ce ee ka cancanta ko baka cancanta ba.Haka idan mutum dan Izala ne ko Basalafe ko abinda yayi kama da wannan shima dole ya zama cewa Salafawa ne ko Yan Izala sune wato body din su ko hukuman su ita zata tsaya ta kalli wadanda suke a karkashin Izala ko karkashin Salaf su tantance su su ce wannan ya cancanta yayi wa’azi ko kuma bai cancanta yayi wa’azi ba,a cikin Salaf ko wani ya cancanta ya zama Malam bai cancanta ba ya zama Malam ba a cikin Salaf,wannan shine na hudun abin da nake son fadi.
Ba zai yiwu ba misali a ce ni dan shi’a ne sai Basalafe ya zo ya tantance ni,zai yiwu ya tantance ni idan yayi amfani da ka’idojin shi’a,kaman yanda yake idan ni dan shi’a ne sai a ce in tantance dan Malikiyya a fiqhu,sai da sharadin in zan yi amfani da ka’idojin Malikiyya ba tare da son rai ba sai ya zama kaman ka zo ne da abin da ake ce ma ANSWER SHEET ka dabbaka akan shi,in ya zama wannan sheet din ya dabbaqu akan shi sai in zartar amma in ba haka ba,ba zai yiwu ba.
Sannan ban da haka kuma,na biyar kenan,akwai batun cewa da yawa daga cikin lokuta muna ganin cewa kaman misali a lokacin Ramadan a lokacin azumi ita Jama’atu da National Supreme Council of Islamic Affaires da duk wanda abin ya shafa a cikin al’ummar Musulmi akan kira Malaman da suke yin tafsir a Rediyo da Telejin da Masallatai da sauransu da sauransu kafin watan Ramadan din yayi su zo a yi masu tambihi a fadakar dasu akan cewa ba zagi ba habaici ba gugar zana da sauransu da sauransu,sai kawai mu ji sun zo cikin masallatan suna cewa ba wanda ya isa ya samu qaidi saboda maganar Allah suke fadi,wato wannan ra’ayin nashi ya kake ganin Kalmar Allah ne,in dan Izala ne ko dan Darika.In dan Salaf ne yace dole sai nuna waye Mushriki kuma wane ne Musulmin gaskiya,kowace aya ya zo sai ya dabbaqa ta ga wadanda yake ganin ba shi bane daga cikin Musulmi.In dan Darika ne haka shima yake yi.To! yaya za a yi da iren wadannan.
Sannan Sallar Tarawih da ake yi a watan Ramadan a Masallatai a cikin unguwanni ko tsakanin unguwanni suna hana mutane barci,idan suna da hakkin ibada,su ma mutane suna da hakkin barci saboda ba a tilasta wa mutane sallar nafila ba.Sallar nafila babu a doron kasan nan wanda ya isa ya tilastawa ko dankarawa mutane ita,cewa ba dole sai mutum ya tashi yayi ta saboda sunan ta nafila.In yayi sai ya sami lada in kuma bai yi ba shike nan,kuma in yayi ta shi kadai yafi lada saboda ba wajiba bace.Wajiba ita daman ba zaka yi tsammanin kila za ka iya yin riya ba saboda daman ta hau kanka.To amma wadda take kari ne,ita wannan tsakanin ka da Allah ne,tafi yiwuwan a yi riya a cikin ta saboda haka an fi so mutum yayi ta shi kadai ba ya zo Masallaci  domin in zo Masallaci yafi kama da kaman yana yin riya.To wa’yannan yaya za a yi dasu.
To banda wannan kuma na shida,wasu na bada misalin cewa a kasashe ai ana sa dokoki na mallantaka da na wa’azi da limamai da masallantai,har da masallatan yau da kullum ba ma masallatan juma’a.Wasu lokuta irin wadannan kasashen-kaman misalin Saudiyya –ana yin haka ne saboda a tabbatar ba a yi wani abu wanda ba Salafanci bane ko kuma Hambalanci ko wahabiyanci.To idan wannan ake so a kawo mana cikin wannan kasar,wato a yi amfani da gomnati sai a tilastawa mutane fahimta daya ta addinin musulunci ko kirista,wannan ba karamin hadari sai haifar ba,zai haddasa fitinar da ba ta yanzu, sai ya zama ya haddasa babbar fitina.
So!ita hukuma din-kaman gomna din-tun da ba ya san addini bane,to ya kamata ya zama yayi taka-tsantsan kuma yayi tunani.Tana iya yiwuwa akwai wadanda suke so su yi mashi gadar zare.Shi ya sani akan cewa yana da abokan hamayyan siyasa masu yawa domin ba yanda za a yi ya zama yana siyasa bai da abokanan hamayya,wannan wani abu ne wanda yake DABI’I,saboda haka ya kalla ya gani su masu bashi shawara a al’amuran addini yaya suke ?kuma ba wai sun san addini bane kuma su ma jahilan addini ne.Mai bashi shawara a bangaren addinin musulunci bai san komai a addinin musulunci ba saboda haka dole ne ya zama yana la’akari da wannan.Sannan dole ya lura da irin wadannan malaman wadanda suke tattare dashi wadanda suke so suyi mashi ingiza mai kantu wadanda suke ce mashi dole ne a kafa wannan dokan saboda a yi maganin shi’a da boko haram.Wanda yake nufi in daman dokan an yi ta ne musamman saboda wasu mutane,to ka ga shima abin ya fito fili kenan,daman abin karya ne,ana so ne a zo da wani abu haka ne a lullube amma ainihin abinda ake nufi din wani abu ne wanda gashi yanzu ya fara fitowa fili.
In ya zama dokan an yi ta ne kawai saboda wasu mutane na musamman shima zai zama ba adalci kuma wannan ba zai nasara ba saboda wa’yannan mutanen da aka nufa ba za su shiga ba,saboda haka a yi hattara a lura da kyau,wato abin da nake so nace maku shine cewa ba wai nace a yi ko kada a yi bane,amma dole ne ya zama komai ya fito fili,a ga cewa adalci ake yi kuma manufar kenan,babu wani abu a boye.
In zan baka misali guda daya kawai shine cewa idan za a tantance ni Malam ne ko ni ba Malam bane kuma na isa in yi wa’azi ko ban isa ba,to da ka’idoji nay a kamata a tantance ni ba da ka’idojin wani ba.Idan aka yi haka ba matsala,ba za a samu matsala ba sam.
YAN JARIDU :Allah ya gafarta Malam,a cikin Bill din da goma ya aika an ambaci cewa akwai wasu komiti guda biyu na tantance masu wa’azi,akwai  babba wato kaman a matakin jiha da karama wato kamar a ce a matakin kananan hukumomi.Sannan akwai wakilai daga dukkan bangarorin Izala da Darika amma babu Shi’a,to me wannan yake nuni?
SHAIKH HAMZAH:Ai shine nake fada maku,a dunkule abinda nake nufi a bayani na kenan.Na karanta Bill din kuma ina da copy dinshi.Ance Izala, ance Dariqa, ai matsalar ma itace cewa, Izala ba daya bace.Su wa'yanda aka ambata  ba a tantance ba saboda su Jahilai ne akan abinda suke magana akai. Akwai Izalar Jos, akwai Izalar Kaduna. Sannan a cikin Izalar akwai Malamai daban daban dukkansu kuma suna gasa da gaba da juna.
Sannan in kazo salaf in ka kara shiga cikin Izalar sosai, to shima makarantu ne masu yawa da malamai masu yawa, kowa na gaba da kowa. Assalafi daban, Almisri daban, Algarqawi daban, Ibni Usman daban, wanene waye daban. In kazo Dariqa shima haka ne. ka gani?Akwai Qadiriyya, akwai Tijjaniyya, a cikinsu kuma duka akwai kungiyoyi daban daban, da sauransu. Har wa'yanda aka ambatan ma ba a fayyace ba, kila akwai wata manufa a ciki, sannan uwa uba ba a ambaci 'yan Shi'a ba, da ma'anar cewa ko su ba musulmi bane? Kenan, kila su za ai musu tasu hukumar daban. Ka tantance ko su malamai ne ko su ba malamai bane. Saboda me? Saboda aqalla su 'yan Qasa ne, Kuma ba Wanda ya isa ya hanasu su yada ra'ayoyinsu. Wannan ya tuna min da wani abu Muhimmi, Wanda da na manta da shi. A dokokin Addinin musulunci (kuma haka suke a dokokin hankali) duk ra'ayin da mutum yake da shi, matuqar da baki yake magana, to ana mishi raddine da baki. In yazo da shubhohi wa'yanda suke zasu ruda mutane, to su wa'yannan shubhohin za'a warwaresu da baki. Kamar Boko Haram yanzu misali: mu dauki Boko Haram, boko haram da ace basu dauki makamai ba, da ace kawai cewa sukeyi Babu Hukuma sai ta Allah, ba za'ai Dimukradiyya ba, ba za'a shiga boko ba, wannan Hukumar kafirace, da sauransu da sauransu, duk gabaki daya ba matsala. Sai kawai a fuskancesu, I'itiqadine sai kawai a fuksakancesu da I'itiqadi, da ra'ayi. In sukace; "QADHA RABBUKA ALLA TA'BUDU ILLA IYYAHU WA BIL WALIDAINI IHSANAN" Sai ace musu ga abinda ayar take nufi. Wato bayani da bayani, in sukace: WALAQAD BA'ASNA FI KULLI UMMATIN RASULIN ANI'I BUDILLAHA WAJTANIBU DAGUT" sukace ga kaza kaza, sai ai musu bayanin me wannan ayar take nufi. Matuqar mutum bai dauki makami ba. Abinda yasa su sun dauki makami, suna kashe Wanda baiji ba, bai gani ba. Asali suna cewa masu kayan sarki, yanzu sunayi a kasuwa, masallatai, ka gane? Coci coci, kan titi, ko ina da ko ina, to wannan shine kawai ake fuskanta ba wai ra'ayin kawai ba. Saboda haka ya kamata su gane akan cewa, lokacin da basu sa 'yan Shi'a ba a cikin ra'ayin nasu. Sunyi babban kuskure, saboda ko da sun dauka 'yan Shi'a ba musulmi bane, ko kuma karkatattune ko kaza, matuqar basu dauki makamai ba, to suna da haqqin zama dan Qasa, sannan suna da haqqin Ta'abiri akan ra'ayoyin su. In ana ganin ra'ayoyin ba dai dai bane, sai a fuskance su, shima da fatar baki. Sai a warware wannan shubhohin da ake tsammanin suna da, amma ace ba za su zama 'yan Shi'a ba, ko kuma ba za suyi addinin su yanda suka fahimta ba, ko ba zasu yada addinin su ba, wannan ba dai a constitution din Nigeria ba.
'YAN JARIDU: Duk da Malam ya riga ya bayar da shawarwari a cikin bayanansa na baya,zamu so mu ji karin shawarwari khasatan ga gomnati.
SHAIKH HAMZAH: Shawara, gomnati ko ba gwabnati ba, da nake so na ba kowa da kowa; itace cewa, a dauki kowa a matsayin shi dan qasa ne, qasa ta hadamu mu dukka. Ba wani batun wai aqida, eh aqida kowa yana da I'itiqadin abinda yake so zai zama a lahira. Ba Ina cewa ni ba musulmi bane. Ko kuma ni da wanda ba musulmi ba ba daya muke ba. Abinda nake cewa shine qasa ta hada mu, kuma muna zaune a cikin qasar akan asasin wata yarjejeniya. Sai wata yarjejeniyar tazo ta canza wannan. Abinda nake cewa a yanda ake a yanzu, ba wata yarjejeniya da ta canza wanda muke akai a yanzu. To saboda haka dole ne ya zama cewa anbar mutane sun zauna a matsayinsu na 'yan qasa, kada ya zama cewa wasu sun fi wasu zama 'yan qasa. In ana nuna ma wasu sunfi wasu zama 'yan qasa akwai matsala sosai, na farko Kenan;
Shawara ta biyu, wannan ta hada hukuma da ba hukuma ba, shawara ta biyu itace cewa; ka da a kuskura a yadda a cikin wannan qasar a fara yaqi na aqida, yaqin aqida-da shi'a sunna, izala, Dariqa, Kirista, musulmi. Abubuwan da akeyi a wasu kasashe, wadda dasisa ce wannan na manya manyan makiran kasashen duniya, kuma babban dalili, suna da dalilai masu yawa.Babban dalilin da yasa suke yin haka shine sayar da makamai, basu damu da jinin mutane ya zuba ba, akan Jinin mutane su suke rayuwa. Kwanan nan ga shi nan muna karantawa a jiridu akan cewa makamai suna ambaliya a cikin wannan kasar, to ko ta ina, da ana cewa su wanene suke shigowa da makaman, to yanzu kowane. Saboda haka kar a kuskura a yadda da cewa a fara yaqin aqida a cikin wannan qasar. Kar a kuskura a bari ababen da suke faruwa, muke jin labarinsu wasa wasa a qasashen waje su shigo cikin wannan qasar, in aka samu haka, to qasar zata tarwatse, dukka mutane zasu rasa mutuncinsu, sannan al'ummu da iyalai zasu dai-daice. In musulmine baki dayanmu ya kamata mu hadu mu zama musulmi, da banbance banbance mu. Addinin nan ba Wanda aka saukarma shi a cikin mu.Kuma ba wanda aka ba gadon tafsir na shi addinin. Kowa yana yin abinda ya fahimta ne na shi addini din.
Shawara ta uku: Ina ganin yana da mahimmancin gasken gaske, dukkanmu mu hadu a fuskar abinda akece ma "Attakfir" (Kafirta mutane) kuma wato irin wannan salafanci wanda yake tahowa daga Saudi Arabiyya, idan ina so in fadi qiri qiri,kuma anan wurin ina so har da wadanda ba Musulmi ba, ina so musulmi da wa'yanda ba musumlmi ba, musulmi gabaki dayansu shi'a da sunna, da wa'yanda ba Musulmi ba, gabaki dayan mu ya kamata mu yi wata qungiya, wadda zamu yanki wannan tunani na takfir, wannan yana da muhimmancin gasken gaske idan anyi hakan.
Sannan shawara ta karshe; itace cewa gomnati, gomnatin Nigeria, ba ma gomnatin Kaduna kawai ba. Yana da muhimmancin gasken gaske ta fahimta cewa ita bata san addini ba. Ita jahilace akan addini, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, qiri qiri, ya gane akan cewa shi bai san addini ba. Saboda haka ya daina yin katsalandan da karanbani a mas'alolin addini. Kuma kar ya dinga jajibo mana ra'ayoyi na addini, wanda yake bai san farkon su ba, bai san qarshensu ba. Yana so ya shigo mana da su sababbi.
Lokacin shugaba Goodluck, an zarge shi da yin kiristanci  a cikin tafiyar da gomnati, kuma Qad'an! Wato (tabbas kenan) Jonathan kwata kwata bai san addinin kirista ba, wannan tabbataccen abu ne (bai san addinin kiristanci ba), wasu ne wa'yanda sukai da'awar su malamai ne, suka dinga da'awar cewa shi crister ne, suka kewaye shi, suna murd'a shi da nuna mishi akan cewa kirista yake yi. Akan wannan asasin Goodluck Jonathan ya zama cewa har a manufofin shi na qasashen waje ba na Nigeria ba sai da ya dabbaqa wannan kiristanci  yabi yahudu, ya hana falasdinu zama qasa, wannan ya sa6ama manufofin qasashen waje na Nigeria.Tunda aka girka Nigeria har zuwa lokacin Jonathan tana tafiya akan wani qaidi daya ne, a manufofinta na qasashen waje, shine na 'yan ba ruwanmu, da kuma Imani da dokokin majalisar dinkin duniya. A lokacin Jonathan ne wannan ya zama ya rushe. To kada Muhammadu Buhari shi kuma yai na daya 6angaren, ya zama wato shima jahilin Addini, kamar yadda Jonathan yake. Sai ya sami wasu wa'yanda suke da'awar cewa sun san addini su kewaye shi, sai a dinga haddasa ma mutane fitintinu kala kala. Kar ya kuskura ya sanyamu mu shiga yaqin ta'addancin duniya. Wata rana a fara daukan sojojin Nigeria ana kaisu Libiya, ana kaisu Pakistan, ana kaisu Afghanistan, ana kaisu "Ila ahkirihi" sannan wannan shiga da yayi cikin komba da qawance na yaqi da ta'addanci na Saudiyya, wannan babban kuskure ne kuma zai iya warwaruwa, don ba dokar Allah bace. In yaga dama zai iya warwarewa. Ya ishe shi darasi ya fahimci cewa Iran ba ta ciki, Iraq ba ta ciki, Afghanistan ba ta ciki, Malaysia ba ta ciki, Indonesia ba ta ciki.
Manya manyan qasashen Musulmin duniya ba su a ciki,sun ji ne kawai ance suna ciki, suka ce basu yarda ba, me yakai shi ? Zai iya haddasa mana fitintinu masu yawa wannan.
Wannan shine iyakan shawarwarin da nake so in baku.

Ƙara sabon ra'ayi