Daya Daga Cikin Shuwagabannin Kungiyar Seleka Ya Tsere Daga Inda Ake Tsare Da Shi
Babban mai gabatar da kara a birnin Bangi babban birnin Afrika ta tsakiya ya bada
Babban mai gabatar da kara a birnin Bangi babban birnin Afrika ta tsakiya ya bada sanarwan cewa daya daga cikin shuwagabannin kungiyar Seleka wanda ake tsare da shi don amsa tambayoyi ya tsere daga inda ake tsare da shi bayan wani harin da wasu mutane dauke da makamai suka kai hari inda ake tsare da shin.
Shafin yanar gizo na Afrika Times ya nakalto Ghislain Grezen guet yana fadar haka a yau Alhamis a birnin Bangi ya kuma kara da cewa Abdullahi Husain daya ne daga cikin shuwagabannin kungiyar Seleka wadanda suka kafa kungiyar tun asalinta. Mai gabatar da karan ya kara da cewa yawan masu dauke da makamai da suka kai hare kan wuren da ake tsare da Husain sun fi jandarmarin da suke tsare da ginin yawa. amma dai ba'a sami ko korzone ga masu tsaron ginin ba. A ranar talatan da ta gabata ne aka kama Abdullahi Husain sannan aka tsare shi don bincike
Ƙara sabon ra'ayi