Kamfanin dillancin labaran Reuters daga birnin Yawunde ya nakalto rundunar tsaron kasar Kamaru a jiya Juma'a na cewa, a cikin wani samame na hdin gwiwa tsakaninsu da takwarorinsu na Najeriya da suka kaiwa mayakan kungiyar Boko Haram sun samu nasarar hallaka 92 daga cikinsu.
Har ila yau dakarun hadin gwiwar sun samu nasarar ceto mutane 850 daga cikin mazuna kauyen Kumshe na tarayyar Najeriya.
Sanarwar ta ce sojojin kasar Kamaru 2 sun rasa rayukansu sanadiyar tashin wani bam a yayin da suka kai wannan sumame.
Idan ba a manta ba tun a shekarar 2009 kungiyar boko haram ta fara kai hare-haren ta'addanci a Tarayyar Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da raba wasu milyoyin fararen hula da mahalinsu, a shekarar da ta gabata kungiyar ta fadada kai hare-harenta zuwa wasu yankuna na kasashen Nijar, Kamaru da Chadi dake makobtaka da Tarayyar Najeriya, wanda hakan ya sanya kasashen suka dauki matakin kafa rundunar hadin gwiwa domin murkushe kungiyar.
Har ila yau a shekarar da ta gabata, kungiyar ta Boko Haram ta yi mubaya'a ga kungiyar 'yan ta'adda na IS mai fafutukar kafa daular musulinci a kasashen Siriya, Iraki da kuma Libiya, lamarin da ya sanya kungiyar ta sauya salon kai hare-harenta zuwa kunar bakin wake.
Ƙara sabon ra'ayi