Iran Da Ghana Sun Cimma Yarjejeniyoyi Da Dama
Kasashen Iran da Ghana sun cimma yarjejeniyoyi da dama tsakanin su, da suka hada da kasuwanci, cinikaya da noma.
bangarorin biyu sun cimma wannan matsayin ne a yayin ziyara da shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama keyi anan birnin Tehran, bayan ganawa da takwaransa na Iran Dr Hassan Rohani.
A jiyya ne shugaba Mahama ya iso nan birnin Tehran tare da rakiyar babbar tawagar 'yan siyasa da masu zuba jari na kasar sa
Ƙara sabon ra'ayi