Jaridun Masar Sun Soki Shirin Saudiyya Na Shiga Kasar Syria

Jaridar al-Aharam ta Kasar Masar ta yi suka da kayyausar murya akan barazanar da Saudiyya ta yi na aikewa da sojoji zuwa kasar Syria
Jaridar ta yau talata ta kunshi rubutun Emad Eryan ya yi suka akan batun da aka bijiro da shi na aikewa da sojan kasa zuwa Syria, duk da cewa kawo ya zuwa yanzu kawancen kasashen duniya ya kasa rusa kungiyar Da'esh.
Emad Eryan ya ci gaba da cewa; Aikewa da sojoji zuwa kasar Syria yana tattare da hastari, kuma zai kara tsunduma yankin cikin rudani.
Kasidar ta kuma ci gaba da cewa; Wajibi ne a kawo karshen yin amfani da rikici da zummar cimma wata manufa ta kashin kai.
A kwanakin bayan ne dai Saudiyyar ta sanar da cewa za ta aike da sojojinta na kasa zuwa kasar Syria da sunan fada da kungiyar Da'esh

Ƙara sabon ra'ayi