Karfafa matakan tsaro a kasar Libiya
An karfara Matakan tsaro a Tripoli babban birnin kasar Libiya
Yayin da ranar zagayowar juyin juya halin kasar ke kara kusantowa, Jami'an tsaron birnin Tripoli sun karfafa matakan tsaro a manyan titunan kasar, tare kuma da shirin ko ta kwana.
A bangare guda kuma har yanzu ana ci gaba da samu sabani wajen kafa Gwamnatin ceton kasar, inda ake ci gaba da matsin lamba ga wasu ministocin kasar da su yi murabus domin kafa Gwamnatin ceton kasa.
Wata Majiya ta kusa da Fathi Almujbiri gungu a Majalisar Shura na Shugabancin Gwamnatin Ceton kasa ta ce ya yi murabus daga kan mukaminsa.
Kuma wannan mataki da Almujbiri ya dauka na zuwa ne bayan kokarin da 'yan kasar ke yi na kafa Gwamnatin ceton kasar.
Ƙara sabon ra'ayi