Amsar Jagora Ga Wasikar Shugaban Kasar Iran Kan Fara Aiwatar Da Yarjejeniyar Nukiliya

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana farin ciki da jin dadinsa dangane da nasarar da al'ummar Iran suka samu sakamakon tsayin daka da kuma tinkarar takunkumin tattalin arziki na zalunci da aka sanya musu da kuma tilasta wa masu adawa da Iran ja da baya a yayin tattaunawar nukiliyan da ta gudana.

Jagoran ya bayyana hakan ne cikin wasikar da ya aike wa shugaban kasar Iran, Sheikh Hasan Ruhani, a matsayin amsar wasikar da ya aike masa a jiya Litinin (18-01-2016) don sanar da shi fara aiwatar da yarjejeniyar nukiliya da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, inda Jagoran yayi ishara da wasu lamurra guda 5 da ya kamata a lura da su.

Abin da ke biye fassarar wasikar Jagoran ne:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Dakta (Hasan) Ruhani

Mai Girma Shugaban Kasa.

Bayan sallama da fatan alheri.

Ina mai bayyana farin ciki na saboda nasarar da tsayin dakan al'ummar Iran masu girma a gaban takunkumin zalunci ya haifar, bugu da kari kan kokarin da masanan nukiliyanmu suka yi wajen ciyar da wannan fasaha mai matukar muhimmanci gaba da kuma kokari ba kama hannun yaro na tawagar masu tattaunawa, lamarin da ya tilasta wa daya bangaren da ake tattaunawa da shi din, wadanda wasunsu ma sun shahara wajen adawa da al'ummar Iran, ja da baya da dage wasu daga cikin wadannan takunkumi na zaluncin. Ina mika godiya ta a gare ka da kuma tawagar masu tattaunawar da shi kansa mai girma Minista (ministan harkokin waje) da dukkanin wadanda suke da hannu cikin wannan lamarin.

A gurguje ina kiranka zuwa ga la'akari da wadannan lamurran:

Na Farko: A sanya ido sosai wajen ganin daya bangaren (da aka tattauna da shi) ya cika dukkanin alkawaru da nauyin da ke wuyansa gaba daya. Maganganun wasu jami'an Amurka cikin kwanaki biyu zuwa ukun da suka gabata, abu ne da ke sanya shakku cikin niyyarsu.

Na Biyu: Ina sake tunatar da dukkanin jami'an gwamnati cewa za a iya magance matsalolin tattalin arzikin da kasar nan take fuskanta ne ta hanyar kokari ba kama hannun yaro sannan kuma cikin hikima a dukkanin bangarori karkashin siyasar tattalin arziki ta gwagwarmaya da dogaro da kai. Dage takunkumi, shi kadai, kawai ba zai iya magance matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta da kuma kyautata rayuwar yau da kullum ta al'umma ba.

Na Uku: Ya kamata a kafafen watsa labarai a yi la'akari da cewa nasarar da aka samu din ba cikin sauki aka same ta ba, an sadaukar da abubuwa masu girma. Rubuce-rubuce da maganganun da (wasu suke yi) wajen kokarin rufe ido kan wannan hakikar da kuma nuna godiya ga bangaren kasashen Yammaci, lalle ba su yi mu'amala ta gaskiya da al'umma ba.

Na Hudu: Shi kansa wannan gwargwadon abin da aka samun, an same shi ne albarkacin gwagwarmaya da tsayin dakar tinkarar sansanin ma'abota girman kai da son amfani da karfi. Don haka wajibi ne dukkanin mu mu riki hakan a matsayin wani darasi mai girma cikin dukkanin lamurra da abubuwan da suke faruwa a Jamhuriyar Musulunci.

Na Biyar: Ina sake jaddada cewa bai kamata a gafala daga yaudara da rashin cika alkawarin gwamnatocin ma'abota girman kai musamman Amurka a wannan batu da ma sauran batutuwa ba.

Ina roka maka da sauran jami'an gwamnatin kasar nan dacewa da kuma taimako na Ubangiji Madaukakin Sarki.

Sayyid Ali Khamenei

29, Dey, 1394

(19, Janairun, 2016)

Ƙara sabon ra'ayi