Masarautar Saudiyya Ta Ki Mika Gawawwakin Mutanen Da Ta Kashe A Jiya Ga Iyalansu

 Masarautar iyalan gidan Saud ta ki mika gawawwakin mutanen da ta kashe a jiya su 47 ga iyalansu, daga ciki kuwa har da Sheikh Baqir Nimr.
Muhammd Nimr dan uwan Sheikh Nimr ya sheda wa kafofin yada labarai cewa, masarautar ta Saudiyya ta ki mika musu gawar dan uwansu da ta kashe, a maomakon hakan ma an sheda musu cewa an rufe dukkanin mutannen ne a wani wuri na daban.
A kokarin da take yi na wanken kanta kan kisan da masarautar Saudiyya ta yi kan Sheikh Nimr, gwamnatin Amurka ta ce ba ta ji dadin kashe ba, amma dai tana kira ga bangarorin gwamnatin Saudiyya da kuma 'yan adawar siyasa a kasar ad su kai zuciya nesa su sasanta, domin kada lamarin ya kai kasar ga shiga wani mawuyacin halin da ba zai yi wa kowa dadi ba.

Ƙara sabon ra'ayi