Sojojin Syria Suna Ci Gaba Da Samun Nasara A kan 'Yan Ta'adda
Sojojin Syria suna ci gaba da kara samun nasara a kan mayakan kungiyoyin 'yan ta'adda a arewacin gundumar Latakia.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, sojojin anSyria sun fatattaki mayakan 'yan ta'adda na kungiyar Daesh daga yankin Jabal Naubah, wanda daya ne daga cikin muhimman yankuna da 'yan ta'addan suke samu dauki da gudunmawa daga gwamnatin Turkiya.
Sojojin sun ci gaba da nausawa zuwa sauran yankuna na yankin Latakia da ke hannun 'yan ta'adda na Daesh da kuma wadanda ke hannun wasu 'yan ta'addan na Nusra Front.
Rahoton ya ce an kashe da dama daga cikin 'yan ta'addan tare da kame wasu, kuma za a sanar da sunayensu da kasashen da suka fito.
Ƙara sabon ra'ayi