Shi'awa da Shi'anci - 5

SHI'AWA DA SHI'ANCI

7-Sun yi imani cewa Allah ya aiko manzanni da adalcinsa da hikimarsa zuwa ga mutane gaba daya, tun daga farkon rayuwarsu a duniya, annabawa da manzanni da suka siffantu da isma da ilimi mai yalwa, da Allah ya yi musu baiwarsa ta hanyar wahayi, don shiryar da dan Adam da kuma taimaka masa domin kaiwa zuwa ga kamalar da aka zana musu. Da kuma shiryar da su zuwa ga biyayya da zata kai su zuwa ga aljanna, take kuma samar musu dacewa zuwa ga rahamar Allah da yardarsa. Mafi shaharar wadannan sun hada da annabawa da manzanni kamar: Adam, da Nuhu, da Ibrahim, da Isa, da Musa, da sauran wadannda aka ambaci sunansu da halayensu a cikin Kur'ani da Sunna madaukakiya.
8-Sun yi imani da cewa wanda ya bi Allah ya gudanar da umarninsa, ya tafiyar da dokokinsa a fagagen rayuwa to ya tsira ya rabauta, ya kuma cancanci yabo da lada, koda kuwa bawa ne baki. Kuma dukkan wanda ya saba wa Allah (s.w.t) ya yi kunnen uwar shegu da umarninsa to ya tabe ya halaka ya kuma cancanci zargi da azaba koda kuwa bakuraishe ne sharifi kamar yadda ya zo a hadisin Annabi madaukaki.
Kuma sun yi imani da cewa inda za a yi sakamako da lada ko azaba a ranar lahira ne wanda a cikinta akwai hisabi, da ma'auni, da aljanna, da wuta, wannan kuwa bayan wucewar kabari da barzahu. Amma tanasuhi wanda masu musun ranar kiyama suka tafi a kansa, to Shi'a suna musunsa domin ya lizimta kayarta Kur'ani mai girma da Sunna madaukakiya.
9-Sun yi imani da cewa karshen annabawa da manznnai kuma cikamakonsu mafificinsu, shi ne Muhammad manzon Allah (s.a.w) dan Abdullah, dan Abdul Mudallibi (a.s) wannan da Allah ya kare shi daga sabo da kurakurai. Ya kuma kare shi daga manyan sabo da kananansu da dukkan wani kuskure ko mantuwa da gafala, kafin annabta ne ko bayanta, a al'amuran isar da sako ko a waninsu. Ya kuma saukar masa da Kur'ani mai girma domin ya kasance littafin tsarin dokoki ga rayuwar dan Adam har abada, sai Manzo (s.a.w) ya isar da sako, ya bayar da amana da gaskiya da ikhlasi, ya kuma sadaukar da komai.
Shi'a suna da gomomin littattafai da suka wallafa game da tarihin rayuwar Annabi (s.a.w) da halayensa da mu'ujizozinsa. Koma wa littafin Irshad na Sheikh Mufid, da kuma A'alamul wara, da a'alamul huda na Dabrasi, da kuma biharul anwar na Majlisi, da kuma littafin arrasulul Musdapha na sayyid Muhsin khatami.
10- Shi'a sun yi imani da cewa Kur'ani mai girma da Allah ya saukar ga annabinsa Muhammad (s.a.w) ta hanyar mala’ika Jibrilu (a.s) kuma wasu daga sahabbai masu girma suka rubuta shi, wanda imam Ali (a.s) yana da fice a kansu a lokacin Annabi (s.a.w) kuma a karkashin kulawar Annabi da lurarsa gare su, da shiryarwarsa, da kuma hardace shi, da kiyaye rubuta haruffansa da kalmominsa da ayoyinsa da surorinsa, da kare su da kiyaye su, wanda suka nakalto shi kakanni da iyaye har zuwa yau, wanda shi ne musulmi suke karantawa gaba dayansu a cikin dare da rana ba tare da wani dadi ba ko ragi, ko canji ko jirkita. Kuma Shi'a sun yi rubuce-rubuce masu yawa game da wannan lamari, sai ka koma wa littattafansu matsawaita da magajerta. (Koma wa littafin al'Kur'ani na Zanjani, da tamhidul Kur'ani na Hadi ma'arifa da wasunsu).

Mun dauko daga Face Book: page; (Haidar Center Enlightenment)
MAWALLAFI; SHEIKH JA'AFARUL HADI
MAFASSARI; HAFIZ MUHAMMAD Sa'id
hfazah@yahoo.com

Masu tsarawa da kula da shafin:
Aliyyu A Abdullahi
Zainabu Husaini

Normal
0

false
false
false

EN-US
X-NONE
FA

MicrosoftInternetExplorer4

/* Style Definitions */
table.MsoNormalTable
{mso-style-name:"Table Normal";
mso-tstyle-rowband-size:0;
mso-tstyle-colband-size:0;
mso-style-noshow:yes;
mso-style-priority:99;
mso-style-qformat:yes;
mso-style-parent:"";
mso-padding-alt:0cm 5.4pt 0cm 5.4pt;
mso-para-margin:0cm;
mso-para-margin-bottom:.0001pt;
mso-pagination:widow-orphan;
font-size:11.0pt;
font-family:"Calibri","sans-serif";
mso-ascii-font-family:Calibri;
mso-ascii-theme-font:minor-latin;
mso-fareast-font-family:"Times New Roman";
mso-fareast-theme-font:minor-fareast;
mso-hansi-font-family:Calibri;
mso-hansi-theme-font:minor-latin;
mso-bidi-font-family:Arial;
mso-bidi-theme-font:minor-bidi;}

Ƙara sabon ra'ayi