Shi'awa da Shi'anci - 2
Gabatarwar Majma'u Ahlil-bait (a.s)
Abin da koyarwar Ahlul-baiti (a.s) ta gadar, kuma mabiyansu suka kare shi daga tozarta shi ne ya hada makaranta da koyarwa da ta game dukkan rassarn ilimin musulunci, wannan makaranta ta yi kokarin tarbiyyantar da mutanen da suka iya kamfata daga wannan kogi na ilimi mai bubbuga, kuma ta gabatarwa wannan al'umma manyan malamai da suka rabauta da wannan hanya ta Ahlul-baiti (a.s) suna masu gamsar da duk wata tambaya da ake da ita a dukkan mazhabobi da fikirori a cikin kasar musulunci ne ko a wajenta, suna bayar da mafi karfin dalili da jawabi mai gamsarwa a tsawon karnonin da suka gabata.
Majma'a ya gaugauta domin kariya ga wannan sakon wanda ma'abota addinai da fikirori suka yi ca a kansa, yana mai biyayya ga tafarkin Ahlul-baiti (a.s) mabiya makarantarsu shiryayya wacce ta kwadaitu wajan raddin dukkan kalubale da ake fuskanta a ko da yaushe.
Darussan da littattafan malaman wannan mazhabi na Ahlul-baiti (a.s) suke kunshe da shi ba su da tamka, domin suna kunshe da kariyar ilimi da suke sun doru kuma sun ginu bisa hankali da hujja da dalili tare da nisantar duk wani bangaranci mai muni da nesantar son zuciya, kuma suna magana da malamai da masana ma'abota tunani da maganar da hankali yake gamsuwa da ita kuma kubutacciyar fidirar halitta take karbarsa.
Majma'a ta yi kokarin gabatar wa dalibai hakikanin sabuwar marhala ta wannan darasi mai wadata ta hanyar wasu bahasosi da talifofi da masu bincike na wannan zamani mabiya koyarwar Ahlul-baiti (a.s), ko kuma wadanda Allah (s.w.t) ya yi musu baiwa da fahimtar wannan koyarwar ta Ahlul-baiti (a.s) suke wallafawa, hada da yada wannan littattafai da ake neman fa'idantuwa da su daga malaman Shi'a na da, kuma wadannan littattafai sun kasance mabubbuga da madogara mai kayatarwa ga masu neman gaskiya, domin a samu budi da fahimtar abin da wannan koyarwar take son isar da sakonsa ga duniya gaba daya a wannan zamani da hankula suke samun kamala da cika, ake kuma samun karin sadarwa da alakoki da sauri.
Kuma muna gabatar da godiya ta musamman ga Sheikh Ja'afarul Hadi saboda wallafa wannan littafi da ya yi, da kuma dukkan 'yan'uwan da suka bayar da gudummuwa wajen ganin an buga shi, haka nan muna godiya ga Sheikh Hafiz Muhammad Sa’id Nijeriya da ya fassara wannan littafi daga larabci zuwa harshen Hausa.
Kuma dukkaninmu muna burin ya zama mun gabatar da abin da zamu iya na kokari domin sauke wani bangare na nauyi da yake kanmu game da ubangijinmu wanda ya aiko manzonsa da shiriya da addinin gaskiya domin ya dora shi a kan duk wani addini, kuma Allah ya isa mai shaida.
Majma'ul 'alami li Ahlil-bait (a.s)
Bangaren wayewar Al’adu da Ci gaba
Mun dauko daga Face Book: page; (Haidar Center Enlightenment)
MAWALLAFI; SHEIKH JA'AFARUL HADI
MAFASSARI; HAFIZ MUHAMMAD Sa'id
hfazah@yahoo.com
Masu tsarawa da kula da shafin:
Aliyyu A Abdullahi
Zainabu Husain
Ƙara sabon ra'ayi