Asasin Rayuwar Aure
Asasin Rayuwar Aure
Asasin rayuwar aure yana daga cikin abin da ya kamata ma'aurata su sani, domin rashin fahimtar hakan zai kai ga rashin cin nasarar ribar aure. Idan mun duba Kur'ani mai daraja da ruwayoyi madaukaka zamu ga sun yi nuni da wasu asasan aure kamar haka:
1- Soyayya da Kauna: Wannan su ne kashin bayan rayuwar aure mafi muhimmanci, domin rayuwar da ba ta da soyayya da kauna babu wata ma'ana da take da ita. Soyayya kauna ce tsantsa ba soyayyar lokaci-lokaci ba, wasu mazan ko matan suna nuna soyayya ga junansu ne kawai yayin da suka bukaci wani abu a gurin juna, kamar nuna wa mace soyayya yayin bukatar ta kawai a shimfida, to wannan ba ita ce soyayya ba. Soyayya tana zurfafa a cikin zuciyar masoyi da masoyiya abin kauna ta yadda ko da yaushe ba a gafala ko mantawa da abin so.
2- Taimakon Juna: Rayuwar ma'aurata tana dogaro ne baki daya kan taimakon juna a duk inda daya ya gajiya ko ya kasa, rayuwa ce ta yi wa juna hidimar da ta dace. Taimakon juna yana kara wa rayuwar ma'aurata kyau da ado, kuma hanya ce ta kara dankon zumunci da soyayya. Ta yiwu wani lokaci ya zama an raba aikin kowanne daga cikinsu sai dai amma wannan ba yana nufin a bar taimakon juna ba, misali namiji yana iya taimaka wa matarsa da yin wanke-wanke, wanke yara, yin wanki, sharar gida ko da kuwa wani lokaci zata iya yi.
Ta bangaren mace kuwa ita ma tana iya yin aikin gwamnati ko sa'ana, ko kasuwanci, a matsayin hanyar da mace zata iya taimaka wa miji, sai ta yi sana'ar da ta dace da ita ko da kuwa daga cikin gidanta ne. Kuma ta wannan hanyar tana iya dauke nauyin wasu abubuwan don kawata rayuwar taimakekeniya ko da kuwa ba su zama wajibi a kanta ba.
Sau da yawa wasu matan suka dauke nauyin rayuwar karatun ilimin 'ya'yansu, suka yi wa kansu sutura wani lokaci har da ciyar da kansu musamman yayin da mazajensu suka gajiya, kuma duk sun samu yin haka ne saboda suna da sana'ar da suke yi ko kuma suna yin aikin gwamnati. Sana'a ga mace wani bangare ne da zata samu damar taimaka wa rayuwar tare.
Amma wani lokaci aikin mace musamman idan ya kasance na gwamnati ne da kullum zai lizimta mata fita wurin aiki yana da nasa janibin da yake haifar da matsaloli tsakaninta da mijinta. A irin wannan lamarin yana da kyau su san mece ce matsalar, kuma a ina ya kamata a gyara, wace hanya zasu bi don kawar da wannan matsalar da take tasowa sakamakon aikin.
Wasu matsalolin suna zama kanana ne, amma wasu matsalolin manya ne, wasu matsalolin sun hada da lalacewar ayyukan gida sakamakon cewa matar gidan tana fita aiki, sai lamarin dafa abinci ya samu tangarda, ko tarbiyyar yara ta fara lalacewa saboda babu mai tsawatawa a kusa. Ko kuma ya kasance tana aiki tun safe har yamma, sai ta rasa sha'awarta, idan mai gida ya zo da dare sai ta ji duk kawai damunta yake yi.
Matsalolin da suka faruwa sakamakon mace tana zuwa aikin baki dayan ranarta suna da yawa, sai dai kowacce akwai hanyoyin da za a iya bi don warware ta, kuma yana da sauki idan suka karbi shawarwarin hakan. Sai dai wacce ta fi kowacce wahalar warwara ita ce wacce ta kai matakin da miji yake zargin matarsa da fasikanci wurin aiki. Wannan lamari ne mai wuyar sha'ani, mai wuyar magani, kuma aure da yawa ya mutu sakamakon irin wannan zargin. Kuma sau tari aka samu hakan ya doru ne bisa zargi kawai.
3- Fahimat Juna: A bisa ka'idar rayuwa duk lokacin da muka ce mu zo mu rayu to wannan yana nufin sai an samu sabani tsakanin juna a yadda ya kamata a rayu, don haka muhimmin abu a nan shi ne mu samu fahimtar juna ta hanyar sanin halayen juna da haduwa kan abin da yake muhimmi, amma inda muka rabu da juna to bai kamata a tilasta wa daya sai ya wurgar da abin da yake so ba. Kuma matukar abin da kowa yake so bai saba wa shari'a ba, to bai kamata a tayar da jijiyar wuya kan hakan ba. Wani namijin yana da irin abincin da yake so, ko irin tufafin da yake so, haka ma mace, a nan ya kamata ne a samu fahimtar juna da kiyaye wa kowane bangaren hakkinsa na zabar abin da yake sha'awa.
Wannan yana faruwa a bangarori masu yawa na rayuwar juna, don haka muhimmin abu shi ne a fahimci juna kan sabanin yadda kowa yake son rayuwa, sai kuma a hadu a inda aka yi tarayya a karfafi bangarensa. Idan misali suna da sabani a wata mazhaba to sai kowa ya riki mazhabarsa ba tare da daya ya tilasta wa dayan barin tasa mazhabar ko darikar ba. Sannan su guji sukan mazhaba ko darikar juna, sai su hadu a asalin Musulunci wanda ya hada su.
4- Hadin Kai: Hada hannu tsakanin ma'aurata domin ci gabantar da rayuwarsu yana daga cikin mafi muhimmanci lamari da zai kai su ga natijar yin aure mai kyau. Rayuwar tare tana bukata sabawa da haduwa da hadin kai don cin nasara, don haka yana da muhimmanci ga masu aure su fahimci hakan, sai su hada kansu a tunani, su kawar da ra'ayin "ni kawai da aibn da nake so". Su yi kokarin kawar da duk wani abu da yake kai su ga sabani, su karfafi duk wani bangare da zai kai su ga hadin kai.
5- Kiyaye Hakki: Duk lokacin da mutane suka hadu wuri daya to sai mun samu wani yana da hakki kan waninsa, kuma haduwar miji da mata yana daga cikin abin da yake da girma wanda a bisa ka'ida kai tsaye zai sanya wani hakki kan junansu. Idan kowannensu ya kiyaye hakkin abokin rayuwarsa to lallai ne zamu samu gida mai zaman lafiya da ci gaban rayuwar kauna, da samar da rayuwar addini mai karfi. Idan gida ya samu wannan yanayin to zai haifar da yanayi mai kyau na samar da al'umma mai tarbiyya.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Text Only or ; 1-WhatsApp 2-Tango 3-Viber (+234 803 215 6884)
Mun dauko daga facebook; (Haidar Center Enlightenment)
Ƙara sabon ra'ayi