Asasin Rayuwar Tare
Asasin Rayuwar Tare
Asasin rayuwar tare da iyali yana da muhimmanci matukar gaske domin shi ne kashin bayan rayuwarsu. Soyayya da kauna ita ce asasin rayuwar tare tsakanin iyali domin samun rayuwar nutsuwa da aminci wacce zata kai su ga kamalar da ta dace. Idan rayuwa ta kasance babu kauna da girmama juna to ba ta da wata kima, bai ma kamata a kira ta rayuwa ba.
Ma'aurtan da suka cire soyayya da kauna daga cikin gidansu, suka mayar da shi kamar fagen yaki ta yadda babu wata alakar soyayya sai tsawa da kin juna da gaba da fada da juna, to wadannan ma'aurata ba zasu iya samar da yanayin soyayya da kauna a rayuwarsu ba. Don haka ne muka ga Musulunci ya zo da wasu hanyoyi da sharuda da ya gindaya don gyara rayuwar ma'aurata, kuma duk ma'auratan da suka yi riko da su zasu ga daidai a rayuwarsu, amma wadanda suka yi watsi da su zasu samu wahalar rayuwar tare.
Riko da wadannan dokokin da sharudan wani abu ne muhimmi ga rayuwar ma'aurata, domin Musulunci ya na kin zaman gwagwarci da rashin aure, don haka bai yarda da guje wa aure don gudun sabani ba. Musulunci yana ganin aure a matsayin wani lamari ne mai tsarki da daraja, don haka ne yake kwadaitar da yin sa, a lokaci guda kuma babu wata hanya da ya gindaya don ci gaba da samuwar 'yan'adam sai ta hanyar aure. Sabili da haka ne ya yi umarni da riko da hanyoyin da zasu sanya rayuwar aure ta zama mai dadi da lafiya da aminci, da tausayi da kauna ga juna.
Kima da daraja da rayuwar aure take da shi ta fi karfin sabanin da yake tsakanin ma'aurata, don haka da bukatar ma'aurata idan sun samu wani sabani su tattauna matsalar da take tsakaninsu don maganin ta da samar da yanayi mai dadin rayuwar tare su da 'ya'yansu.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Text Only or ; 1-WhatsApp 2-Tango 3-Viber (+234 803 215 6884)
Ƙara sabon ra'ayi