Jayayya Tsakanin Ma'aurata
JAYAYYA TSAKANIN MA'AURATA
Soyayyar da take tsakanin miji da mata shi ne abin da zai rike rayuwarsu ya sanya ta dawwama, mutane sun sassaba kuma haka nan ne Allah ya halicce su, kuma yin aure ba ya iya rushe wannan bambanci, don haka ke nan akwai bukatar wani abu da zai zama kamar madaurin tsintsiya tsakanin mata da miji don dawwamar da dankon kauna da hadin guiwa wurin ci gaban rayuwa mai armashi.
Ma'aurata suna bukatar saukowa daga matakinsu don samun daidaito da juna, domin idan kowanne ya dage kan matsayinsa da maslaharsa kawai ba tare da kallon dayan ba, to wannan yana nufin rayuwar aure ta yi daci. Don haka suna bukatar haduwa a tsakiya ne da riko da abin da aka yi tarayya a cikinsa, da kuma samar da yanayin da zai bayar da soyayya da kauna mai karfi da zata kasance madauri tsakaninsu kuma dankon zaman tare.
Rayuwa ba lamari ba ne mai daci kamar yadda wasu suke gani, idan muka yi rayuwa mai hadafi da take dogaro da koyarwa mai kyau to zata kasance mafi dadin abu. Sau da yawa zamu ga masu kauce wa koyarwa mai inganci a rayuwa suna samun sukewa daga rayuwa suna fatan rabuwa da juna, daga karshe sai ya kasance ba su da wani zabi sai ko dai su rabu ko kuma rayuwarsu ta ci gaba cikin azabtuwa.
Rashin fahimtar ma'anar rayuwa yana daga cikin abin da yake sanya sabanin ra'ayi da jayayya mai tsanani tsakanin miji da mata, wani lokacin farkon haduwar saurayi da budurwa ba su san juna ba, ba su san ma'anar rayuwar tare ba, kuma sun yi aure ba tare da cikakken sanin juna ba, sai ya zama kowannensu yana da wani ra'ayin da yake ba gaskiya ba ne game da abokin zamansa. Da zarar an yi aure an samu 'yan watanni kadan sai hakikanin kowannensu ya bayyana ga juna, daga nan kuma sai a fara sabani da jayayya da fada da zage-zage har daga karshe sai a kai ga rabuwa baki daya.
Muna iya daukar misalin tsafta yayin da kowannensu idan zai je wurin dayan kafin aure sai ya kure adaka ya ci ado, kuma tayiwu wannan tsaftar ce take burge kowannensu, amma bayan aure da 'yan watanni sai ta bayyana ga dayan cewa abokin rayuwarsa babban kazami ne mai lamba daya, daga nan ne sai sabani kan wannan lamari ya yi kamari har ya kai ga matakin da shi mai tsafta ba ya iya jure zama da abokin zamansa, daga nan ne kuma sai wannan matsalar ta haifar da wasu matsalolin da ba a yi tsammaninsu ba, sai kuma daga karshe a shiga danne hakkin wanda ake jin haushi, sai soyayya ta yi karanci, sai a ci gaba da rayuwar bakin ciki da juna ko kuma a kai ga rabuwa. Idan muka dauki kowace matsala (wadanda suna da yawan gaske) zamu iya dora ta kan irin wannan sikilen don sanin me yake faruwa da wasu matsaloli suke kunno kai tun a sabon aure.
Domin fito da abin a sarari muna iya kara bayar da misali na biyu na kalmomin dadi da soyayya da kauna da suke gaya wa juna kafin aure, amma da zarar an yi aure sai su koma masu gaya wa juna bakar magana kamar dai ba su ne jiya suke kalmomi irin na soyayya ba. Sau da yawa ko dai saboda wani abu da yake faruwa kamar kin miji da mata take yi a shimfidarsa, ko kuma wani abu na rashin kyautatawa da mijin ya ke yi, ko kuma saboda kawai rayuwar al'ada sandararriya da aka gada. Daga nan kuma sai a diga dan "ba" din fara nisantar juna da kyamar juna da gaba, daga nan ne sai rayuwa ta zama lami kamar miyar da babu gishiri cikinta, sai ta yi daci daga karshe ta gurbace, ko dai ta ci gaba a hakan, ko a samu hanyar gyara idan sun fadaka suna son gyara, ko kuma rabuwa ta zo.
Sau tari irin wannan lamarin yana faruwa sakamakon ba su gaya wa juna gaskiyar yadda suke ba, wani lokaci an gina soyayya kan karya kafin aure, ga karancin fahimtar hakikanin juna, ko kuma ya kasance akwai wasu halaye marasa kyau da abokin tafiya ba zai iya jure musu ba. Kuma tun farkon fahimtar wata matsala maimakon su fuskanci hanyar gyara, sai kowanne ya yi kokarin binne aibin da ya sani game da dayan, sai dai duk lokacin da suka samu sabani to a wannan lokacin ne za a fara tone-tone.
Zamu iya ganin wasu abubuwa da suke kaiwa ga jayayya kamar haka: Rashim fahimtar ma'anar rayuwa – jahiltar juna – rashin fahimtar al'adun juna – kokarin salladuwa kan juna – sauke fushin da aka kwaso daga waje kan juna – rashin sanya hankali da amfani da fushi – rashin juriyar cutarwar juna – sanya dokoki kai tsaye ba tare da sanya tunani da hankali ba – nadamar yin auren da jin yaudara - hassada ga juna – munana zato – rashin yafe wa juna – rabuwa da wani namiji don ya zama musanyar miji – rashin jituwa da juna.
Akwai dalilan da suke sanya sabani da jayayya tsakanin ma'aurta wani lokaci karancin shekaru suna taka rawarsu a cikin rikici tsakanin ma'aurta sakamakon ba su da cikakkiyar masaniya game da rayuwa da yadda take, kuma suna fuskantar matsalar warware duk wani sabani da ya ke faruwa tsakaninsu, sannan kuma ba su koma wa manya ba don sanin yadda ya kamata su rayu ko su warware matsalarsu.
Wasu kuma suna da dalilai daban-daban, zamu ga a cikinsu akwai wadanda suke huce haushin tawayar da suke ji kan abokin zamansu, wasu kuwa karancin tarbiyya ne yake damunsu, wasu kuwa takama da nuna isa saboda suna da abin duniya a hannunsu, wasu kuwa suna jin matsayi da sarauta tare da su don haka sai suka dauka cewa kowa bawansu ne hatta da matansu, wasu kuma suna nan a matsayin yara a tunaninsu har yanzu ba su balaga ba a tunani.
A sakamakon jayayya da rashin zaman lafiya da yake addabar gidan aure wani lokaci sai a samu daya ya sallama wa abokin rayuwarsa saboda tsoro musamman idan mace tana jin tsoron saki, sai dai irin wannan rayuwar takan zama lami babu wani dandanon soyayya da kauna a cikinsa, sai ta koma kamar gurbataccen ruwa wanda ba ya shawuwa. Ko kuma dai kowa ya ki sallama wa abokin zamansa sai a yi ta rikici da fadace-fadace kowane lokaci, har ta kai ga ko dai rabuwa ko kuma rayuwa irin ta 'yan jahannama. Idan ba a rabu ba aka ci gaba da rayuwa kuma aka samu 'ya'ya, to a nan ne rayuwar yara take tasowa cikin mummunan yanayi da lalacewar tarbiyya.
Duk yadda muka sawwala dalilin jayayya da rabuwa tsakanin ma'aurata ba zamu iya iyakance su ba, wasu sun dauka idan mata suka fi karanci za a samu saukin rikici da sabani saboda karancin abu yana sanyawa a lallashe shi a yi tattalinsa, sai dai idan mun duba abin da ya ke faruwa kasar Sin inda maza suka fi mata yawa da Miliyan Ishirin da wani abu ga shi kuma akwai yawan saki da rikici tsakanin ma'aurata sai mu ce wannan lamarin ba haka yake ba. Wasu kuwa sun dauka idan sadaki ya yi tsada sosai wannan lamarin zai sanya a lallaba mata don haka saki da rabuwa da jayayya da rikici zai yi karanci ke nan, sai dai idan muka duba kasashen Turkiyya da Farisawa masu yawan saki alhalin suna da tsadar sadaki zamu samu wannan tunanin shi ma kuskure ne.
Don haka akwai dalilan da suke sanya jayayya da rashin jituwa tsakanin miji da mata, da idan mun duba zamu ga mafi yawanci suna faruwa ne sakamakon karancin soyayya da kaunar juna, ko kuma rashin sani hanyar warware matsala, ko kuma son rai da kin gaskiya, ko kuma matsalar rayuwa, ko bambancin al'adu. Idan muka san hakan to ke nan yana da muhimmanci mu san me ke jawo karancin soyayya, kuma yaya za a kawar da jahiltar rayuwa ta yadda za a iya warware duk wata matsala bisa ilimi, sai kuma kokarin kawar da son rai domin gyara rayuwar iyali.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Text Only or ; 1-WhatsApp 2-Tango 3-Viber (+234 803 215 6884)
Ƙara sabon ra'ayi