Auren Umar da 'yar Imam Ali

Manene gaskiya zance akan auran khalifa umar da zainab bintu imam Ali{as},wanda wasu mallamai sunna da shia suka rawaito?

Da SunanSa Madaukaki

 

Tambaya 34992: Me ye ingancin auren da Umar ya yi da Ummu Kulsum 'yar Imam Ali (a.s) da wasu malaman Sunna da na Shi'a suka ruwaito?

Takaitattar Amsa:
Batun auren Ummu Kulsum da Umar duk da wani lamari ne na fikihun addini sai dai a tsawon tarihi an mayar da shi wani lamari na siyasa domin nuni da yardar Imam Ali (a.s) ga halifancin Umar da cewar da bai yarda da shi ba da bai ba shi 'ya ba; daga nan ne kuma sai wannan lamarin ya koma kamar sauran lamuran tarihi da ba su samu tsira ba daga sanya hannu a kansu da 'yan siyasa masu mulki suke yi.
Wannan lamarin na auren Umar da 'yan Imam Ali wasu masu tarihi sun yi raddinsa da dalilan da suka kawo, wasu kuma sun karbi asalin yin auren amma sun yarda cewa lokacin auren ta kasance karamar yarinya ce, don haka an kashe Umar kafin tarewarta. Haka nan ma akwai sabanin ruwayoyi da suke da alaka da auren Umar da Ummu Kulsum ta fuskacin matani da sanadi da haddin da ya kai ga kokwanton lamarin da ba za kuma mu iya dogaro da shi ba.

Bayyanannar Amsa:
Batun auren Ummu Kulsum da Umar duk da wani lamari ne na fikihun addini sai dai a tsawon tarihi an mayar da shi wani lamari na siyasa domin nuni da yardar Imam Ali (a.s) ga halifancin Umar da cewar da bai yarda da shi ba da bai ba shi 'ya ba ; daga nan ne kuma sai wannan lamarin ya koma kamar sauran lamuran tarihi da ba su samu tsira ba daga sanya hannu a kansu da 'yan siyasa masu mulki suke yi.
An samu sabani game da auren Umar da Ummu Kulsum kamar haka:
Na daya; wasu sun yarda da cewa an yi auren, sai dai bisa la'akari da lokacin auren tana karama matukar gaske don haka kafin ta kai ga shekarun balagar tarewa gidan miji ne sai aka kashe Umar, don haka ba a samu bikin tarewa ba ke nan .
Na biyu; wasu kuma suna ganin Ummu Kulsum tana da 'ya'ya biyu da Umar masu sunan Zaid, da Rukayya .
Na uku; wasu kuwa suna ganin sam wannan lamari ne da bai faru ba, kuma suna ganin cewa ba ma labarin wannan lamarin ko ingancinsa .
Zamu kawo wasu daga mahangai da ra'ayoyi a nan kamar haka:
1. Hisham dan Salim ya karbo daga Imam Sadik (a.s) yana cewa: Lokacin da Umar ya nemi auren Ummu Kulsum sai Imam Ali (a.s) ya gaya masa cewa ita fa karama ce. Sai Umar ya hadu da Abbas ya ce masa: Yaya nake ke nan, ko ina da wata matsala ne? Sai Abbas ya ce masa: Me ya same ka? Sai Umar ya ce: Na nemi aure gun dan dan'uwanka ne amma sai ya ki yarda, na rantse da Allah sai na cika ruwan zamzam. Kuma babu wani mutunci naku da zan kare naku sai na kawar da shi, kuma sai na kawo shedu biyu da zasu nuna cewa ya yi sata don in yanke hannunsa. Abbas ya zo wurin Imam Ali (a.s) ya gaya masa abin da ya faru tsakaninsa da Umar dan Khaddabi, ya kuma nemi ya bayar da komai hannunsa; Imam Ali (a.s) ya kuwa bayar da wannan lamarin a hannun Abbas . Bayan mutuwar Umar kuwa, sai Ali ya zo gidansa ya dawo da 'yarsa gida .
A wasu ruwayoyin na 'yan sunnan suna cewa; yayin da Ali ya ce wa Umar ita karama ce. Sai Umar ya ce: Na rantse da Allah ba wannan ba ne abin da yake damunka, mu mun san me yake damunka . Sai Umar ya zama ya yi jur'ar wannan magana ga Ali (a.s) da rashin girmama shi.
2. Allama Majlisi yana cewa: Nubkhati daga malamai dadaddu na Shi'a (ya yi zamani lokacin karamar fakuwar Imam Mahadi) yana cewa: Ummu Kulsum ta kasance karama ce, kuma kafin ta kai shekarun balaga ne Umar ya rasu . Kuma wannan shi ne abin da Zarkani bamalike ya fada .
3. Ibn Sa'ad ya kawo labarin Zaid da Rukayya 'yar Umar da cewa babarsu ita ce Ummu Kulsum 'yar Ali (a.s) . Kuma an karbo daga Imam Bakir (a.s) cewa; "Ummu Kulsum 'yar Ali da danta Zaid dan Umar ta rasu da ba a san waye ya riga mutuwa ba tsakaninta da danta, kowanne bai gaji kowanne ba, kuma sun yi wa biyun salla ne . Sai dai wannan ruwayar tana da rauni matukar gaske saboda saba wa ka'idojin ruwayar Shi'a .
4. Mas'alar auren Ummu Kulsum da Umar dan Khaddabi ba ta zo a cikin Buhari, Muslim, Masnad Ahmad, Masnad Bazzaz, da Tabarani da sauransu.
Sabanin ruwayoyin ya kai ga haddin da mutum zai yi kokwanto misali, wasu ruwayoyin suna nuna kawai Zaid ta haifa, wasu kuma su kara Rukayya , wasu su ce Fatima 'yar Umar ce ta haifa . Wasu ruwayoyin su ce Imam Ali ya gaya masa cewa karama ce, wasu kuma su ce ya gaya masa cewa ya ajiye wa 'ya'yan Ja'afar danuwansa da ya yi shahada ne .
6. A wata ruwayar kuma Umar ya zo wurin muhajirai ne ya ce da su: "Raffi'uni" kalma ce da take nufin ; Ku taya ni murna, alhalin kuwa manzon Allah ya hana amfani da ita. Ya zo a Masnad Ahmad cewa: Salim dan Abdullahi ya ce: Akil dan Abutalib ya yi aure da wata mata sai ya zo wurinmu sai ya ce: "arrafa wal banin" ana taya murna. Sai muka yi shiru saboda wannan kalma ce da ake amfani da ita a Jahiliyya, kuma manzon Allah (s.a.w) ya hana amfani da ita, sai dai a ce: "Barakallah fika wa baraka laka fiha", wato Allah ya yi maka albarka kuma sanya maka albarka cikinta .
7. A wasu ruwayoyin ya zo cewa Ummu Kulsum da danta Zaid sun mutu lokacin mu'awiya ne ?! Wasu kuma suna cewa Ummu Kulsum 'yar Ali ta halarci karbala ma, kuma tana cikin ribattun yaki , ba su kuma kawo batun neman auren ta ba .
8. Wasu kuwa suna cewa: Ummu Kulsum ta yi aure da Aunu dan Ja'afar bayan Umar, bayan mutuwarsa kuma sai ta auri Muhammad dan Ja'afar, bayan mutuwarsa sai ta yi aure da Abdullahi dan Ja'afar . Wasu kuwa suna cewa Aunu da Muhammad 'ya'yan Ja'afar sun yi shahada ne lokacin halifancin Umar a yakin Tastur wanda ya faru lokacin halifancin Umar.
Don haka babu wata hanyar da za a iya tabbatar da auren Umar da Ummu Kulsum; domin masu ruwayar suna daga wadanda ake tuhuma da karya da raunin Hadisi, kuma ta fuskacin matani tana da matsaloli da yawa.
Don dubawa sosai ana iya komawa:
2628 (auren halifa na biyu da Ummu Kulsum)

cirowa daga islamquest.net: Tarjama da Khulasarr: Hafiz Muhammad Sa'id 

Ƙara sabon ra'ayi