Shahid Mutahhari da mahagarsa akan addini.

 Shahid Mutahhari da mahagarsa akan addini.

 Shahid Mutahhari da mahagarsa akan addini.AllahءMusulunciءAddiniءMohammadءAliءshiءmahdiءtvshiaء

A duk lokacin da ake tunawa da zagayowar shahadar Ayatullah Mutahhari ana ambaton ayyukan da ya yi masu kima. Ana girmama shi ba saboda muhimman ayyukan da ya gabatar ba kadai hadda ma yadda ya ke bayyana matsalolin da su ke damun al'ummar musulmi.Shahid Mutahhari yana a matsayin kyakkyawan misali ne kuma abin koyi ga dukkan mazanarta musulmi. Mutum ne ma'abocin ilimi da hikima masanin falsafa da sanin Allah kuma babban marubuci. Littatafansa suna a matsayin wata kofa ce ta isa ga birnin ilimi da hikimomi ga masu neman ilimi.Daga cikin abubuwan da rubuce-rubucen mutahari su ka fi maida hankali akansu akwai sa'adar jinsin dan'adam adoron kasa ta hanyar yi wa addini kyakkyawan sani. A cikin rubuce-rubucensa yana kafa dalilai na ilimi da hankali akan cewa musulunci shi ne hanyar rayuwa mai daraja ta koli. Ayoyin kur'ani masu yawa suna bayyana addinin musulunci a matsayin cewa shi ne rayuwa ta hakika wacce Allah ya gabatar da shi ga jinsin biladama. A cikin aya ta 24 a suratul Anfal ya zo cewa:"Ya ku wadanda ku ka bada gaskiya ku amsa kiran Allah da manzo idan ya yi kiran ku ga abinda zai kyauta rayuwarku."A dalilin haka amsa kiran Allah da manzonsa ne abubuwan da su ke sa rayuwa ta yi kyawu. Za kuma a iya cewa musulunci ya kawowa biladam wata kyauta ce mai girma da kima wacce idan sun yi aiki da ita za su ji dadin rayuwarsu ta duniya da kuma samun tsira a lahira.Shakka babu musulunci shi ne mai samar da rayuwa managarciya mai dorewa. Shahi Mutahhari yana cewa: "musulunci tamkar rana ne wacce ba ta taba faduwa." A mahangarsa dole ne addini ya kasance a cikin fagen rayuwa domin farfado da shi. Dole ne ya zama mutane suna tafiyar da rayuwarsu ta daidaiku da kuma ta zamantakewa bisa addini.Mutahhari mutum ne da ya yi imani da cewa addinin musulunci ya amsa dukkan bukatun da mutum ya ke da su na halitta. Abisa wannan mahangar ne Muttahari ya kafa dalilai kwarara wajen rusa yadda wasu manazarta ke danganta samuwar addini da jahilci. Ko kuma a matsayin matakin farko na ci gaba dan'adam. Muthhari yana da kwararan dalilan da ya tabbatar da cewa komai yadda danadam ya samu ci gaba a rayuwa to bai wadatu daga buran addini ba.Bukatar mutum da addini ta tsallake ta daidaiku zuwa ga al'umma. Kamar yadda daidaikun mutane su ke da bukatuwa da addini haka nan al'umma. Tolstoy wanda marubuci ne dan kasar Rasha ya bada jawabin tambayar da aka yi masa akan imani inda ya ce:"Imani shi ne abinda mutum ya ke rayuwa tare da shi a kowane lokaci wanda kuma shi ne jarin mutum."Mutum yana da tunane-tunane masu yawan gaske da su ka hada da dawwama har abada. Wannan tunanin da ya ke a tare da mutum yana haifar masa da wani tunanin akan yadda zai gujewa karewa. Yana son sunansa ya dawwa aduniya. Idan ace rayuwar mutum na wani dan kankanen lokaci a doron kasa za ta kare da mutuwa to wannan rayuwar tashi ba ta da wata kima. Abinda ya ke baiwa mutum jin dadi shi ne addini wanda ya ke tabbatar masa da cewa zai dawwama cikin ni'ima a lahira idan ya yi aikin kwarai a doron kasa."Addinin musulunci a wurin Shahid Mutahhari yana kunshe da kyawawan halaye da kuma dokoki. A wannan lokacin kuwa abu ne da ya fito fili cewa addini ba tare da kyawawan halaye ba, ba shi da madogara mai karfi. Musulunci addini ne da ya ke kiran shimfida adalci da samar da daidaito da yanadamtaka."Abin takaici ne cewa kwakwalen mutane sun sami gagarumin ci gaba amma a lokaci guda zukata sun yi rauni."Musulunci addini ne wanda yake amsa bukatun mutum na zuciya da kuma na hankali. Wannan karfin da addini ya ke da shi ne na amsa bukatun biladama na zuci da kuma hankali ya sa zai ci gaba da dawwawa matukar da akwai rayuwa adoron kasa.

hausa.irib.ir

Ƙara sabon ra'ayi