Tsumi da Kumaji Na Ashu'ra
Tsumi da Kumaji Na Ashu'ra
Tarihi, tamkar madubi ne da ya ke nuna hotunan abubuwa masu dadi da daci da su ka faru a cikinsa. Daga cikin abubuwan da su ka faru a tarihin musulunci, karbala tana da matsayi na musamman. Kumajin Imam Hussaini (A.s.) yana a matsayin fito na fito ne a tsakanin gaskiya da bata da kuma sadaukar da rai domin kare addini. Yunkurin Imam Hussaini (A.s) ba wai wani abu ne kadai da ya faru ba na tarihi yana kuma a matsayin wata al'ada ce rayayya. Al'ada ce wacce ta samo tushe daga cikin musulunci wacce kuma ta taka gagarumar rawa wajen raya addinin musulunci da ci gaba da wanzuwarsa. Wannan yunkurin na Karbala yana a matsayin wata mabubbugar ruwa ce wacce ta ke kosar da masu kishiruwar gaskiya da son shimfida adalci da a tsawon tarihi ta baiwa 'yan gwagwarmaya da dama karfin guiwa. Filin da aka ja daga a cikinsa na wannan kumaji yana a matsayin mai yi wa mutane ma'abota basira da neman adalci shifta a kowane lokaci. Sanannen abu ne cewa mayakan da su ka kasance a tare da Imam Hussani (A.s.) suna da cikakkiyar masaniya akan manufarsu da kuma abinda su ke fuskanta. A wurin Imam Hussaini da sahabbansa, jahilicin mutane ya fi zafi akan mikin da takobi zai yi. Saboda haka kawar da jahilcin da mutane su ke ciki shi ne jihadi mafi muhimmanci a wurinsa. A tarihin Karbala an ambaci cewa sahabban Imam Hussaini (A.s.) sun rika yin jawabai na wayar da kan al'umma akan gaskiya, ta yadda a duk lokacin da za su fita filin daga domin yin fito na fito na gaba da gaba da makiya suna karanta baitocin wake na kumaji da tayar da tsumi wadanda kuma a lokaci guda su ke kunshe da wayar da kan al'umma akan matsayin Imam Hussaini da kuma iyalan gidan annabi. Wannan yana nuni da cewa makiya sun yi parpaganda mai yawa ta bata da bakanta matsayin iyalan gidan annabi. Wannan ne ya sa a duk lokacin da wata dama ta samu a wurin sahabban Imam Hussaini su ke fitowa domin su kare iyalan ma'aiki da bayyana matsayinsu.Imam Hussaini yana a matsayin abin kyakkyawan misali ne na tsoron Allah. Tsarkin ruhinsa da sahabbansa ne ya sa ba za su iya zura idanu suna kallon zalunci da fasadi ba tare da sun kalubalance shi ba. Gagarumin aiki mai hatsari da kuma nauyi wanda sahabban Hussaini Dan Ali su ka yi a Karbala, ba abu ne da zai yiyu ba ba tare da tsarkin zuciya da kuma aiki da kyawawan halaye ba.Sahabban Imam Hussaini suna da imani na koli da kuma narkewa akan tafarkin gaskiya.Daga cikin siffofin da Sahabban Imam Hussaini su ka kebanta da su, da akwai cika alkawalinsu a gare shi da kuma manufofinsa. Hatta a cikin yanayi mafi tsanani ba a shirye su ke ba su karya alkawalin da su ka kulla da Imam Hussaini.Daga cikin sahabban Imam Hussaini da akwai Abul-Fadal Al-Abbas (A.s.) wanda ya ke da matsayi na musamman. Sunansa yana a matsayin alama ce ta cika alkawali.Abbas saurayi ne jarimi wanda ya kebanta a siffofin kwarai da imani da ilimi na musamman a tsakanin sahabbai da kuma dangin Imam Hussaini. Shi Da ne ga Imam Ali (A.s.) mahaifiyarsa kuma ita ce Ummul-Banin wato matar da Imam Ali ya aura bayan rasuwar Fatimatuz-Zahra'a (A.s.) saboda haka shi dan'uwan Imam Hussaini ne. Kyawun halittarsa ne ya sa ake yi masa lakabi da sunan "Farin watan Banu Hashim." A lokacin yunkurin Karbala, Abbas ya kasance kwamandan dakarun Imam Hussaini. Shi ne wanda ya ke dauke da tutarsa kuma shi ne kuma wanda ya ke kula da kare hemar da mata da kananan yara su ke a ciki sannan kuma da samar da ruwan da za su sha. A lokacin Karbala ne Abbas ya nuna kumaji mafi kyawu a rayuwarsa. A karbala sojojin Yazidu Dan Mu'awiyya sun hana Imam Hussaini da Sahabbansa isa ga ruwa saboda su matsa lamaba akansu da tilasta su mika wuya tun da wuri. A lokaci da kishiruwa ta buwayi 'ya'yan Imam Hussaini da sahabbansa da kananan yara da mata makiya sun sake rufe duk wasu hanyoyin isa zuwa ga inda ruwa ya ke. Abbas ya sadaukar da kai domin ya debo ruwa. A cikin jarunta wacce kwatankwacinta ya karanta, ya keta sahun makiya da su ka killace su har ya isa inda ruwa ya ke. Abbas ya kamfato ruwa da hannuwansa saboda ya sha domin kuwa kishiruwa tana cinsa, amma kuma ya fasa saboda ya tunano da kishiruwar da mata da kananan yara da Imam Hussaini su ke ciki. Ya cika goran da ya ke rike da shi da ruwa sannan ya kama hanyar komawa sansani. Yana cikin tafiya ne makiya su ka harbi hannunsa na dama da ke rike da goran ruwa sanann su ka sare shi. Abbas ya maida goran ruwan zuwa hannunsa na hagu ya rike goran da shi, amma makiyan su ka sare wannan hannun nashi da tsige shi daga kafadarsa. Wannan bai hana Abbas yin duk wani abu da zai iya yi ba domin dai ya isa da goran ruwa zuwa ga kananan yara mabukata saboda haka ya rike goran ruwan da bakinsa. Wani daga cikin dakarun bata ya harba kibiya akan goran da Abbas ya ke rike da shi a bakinsa ruwan da ke cikinsa ya zube. Sai dai makiya ba su kyale shi ba sun ci gaba da yi masa ruwan kibau da ya sa shi faduwa kasa. A nan ne Abbas wanda ya ke dauke da tutar Imam Hussaini ya yi shahada. Wannan shahadar ta Abbas ce ta kashe zuciyar Hussaini kamar yadda ya fada a lokacin da ya zo ya tsaya a kan dan'uwansa yana ban kwana da shi.Karbala ta ga jarunta mara tamka ta iyalai da sahabban Imam Hussaini (A.s.). Jarumai irin su Ali Akbar wanda Da ne ga Imam Hussaini. Matashi ne mai jarunta wanda ta fuskar kirar halitta da halaye ya dauko dukkan kamannin annabi muhammadu (s.aw.a.) A loakacin da zai fita yin fito na fito da makiya, mahafinsa Imam Hussaini ya bashi dama duk da irin kaunar da ya ke yi masa. A lokacin da Imam Hussaini ya ke kallon dansa yana shirin fita zuwa yin kwami da makiya ya daga hannunsa sana yana fadin cewa:" Ya Ubangiji kai ne shaida akan cewa wannan saurayin da zai fita yin fito na fito yana da kyawawan halaye da kamanni na halitta irin na manzon Allah. A duk lokacin da mu ke shaukin kewar annabi shi ne mu ke kallo."Ali Akbar ya yi yaki cikin jarunta ya kuma kashe makiya da dama. Mayakan Yazidu Dan Mua'wiyya sun shammace shi su ka sare shi daga baya-wanda alama ce ta tsoro da yaudara a yaki irin na gaba da gaba. Ali Akbar ya yi shahada a wannan lokacin.Daga cikin sahabban Imam Hussaini da akwai tsofaffi wadanda su ka manyanta a shekaru. Daga cikinsu da akwai Habib Bin Muzahir wanda ya rayu tare da annabi da kuma Imam Ali ya kuma yi yake-yake na musulunci a tare da su. A lokacin Karbala ya yi yaki cikin jarunta har yayi shahada.Muslim Bin Ausaja tare da Habin Bin Muzahir sun isa cikin rundunar Imam Hussaini daga birnin Kufa. Shi ma ya yi shahada jim kadan bayan Habib Bin Muzahir. Daga cikin maganganunsa a lokacin Karbala, ya fadawa Imam Hussaini cewa:"Idan da za a kashe ni sau saba'in sannan in sake dawowa a raye, to ba zan daina taimaka maka ba."Wahab wani matashi ne mabiyin addini Kirista mazaunin birnin kufa wanda jin sakon Imam Hussaini ya sa shi nufar inda ya ke shi da matarsa da mahaifiyasa. Kin jinin zalunci ne ya fisge shi ya shiga cikin rundunar Imam Hussaini ya kuma shiga cikin addini Musulunci. Ya shiga cikin kwami a Karbala inda ya kashe makiya 19 sanann daga baya ya yi shahada. Makiya sun sare kansa sannan su ka jefa shi zuwa cikin rundunar Imam Hussaini (A.s.). Mahaifiyar Wahab ta rungume kan danta ta sumbace shi sannan ta sake jefa shi cikin sojojin makiya tana mai fadin cewa:"Abinda mu ka bayar akan tafarkin Allah ba mu sake karbarsa."Wahab ya yi shahada yana dan shekaru ashirin da biyar.Daga cikin jaruman Ashur'a da akwai Qasim Dan Imam Hassan (A.s.). A daren Ashura da Imam Hussaini ya ke baiwa sahabbansa labarin za su yi shahada, Qasim ya tambayi kawunsa ko shi ma zai sami wannan baiwa ta shahada?Imam Hussaini da ya tasirantu daga maganar Dan danuwansa Imam Hassan ya tambaya shi cewa:"Ya kai Dana, mutuwa wane irin dandano ta ke da shi a wurinka?Qasim ya masa masa da cewa: Mutuwa akan tafarkin gaskiya tana da dandadon irin na zuma a wurina."Qasim da ya ke dan shekaru goma sha uku ya yi shahada.Hur Bin Yazid al-Riyahi wani ne daga cikin jaruman Karbala wanda labarinsa ya ke a matsayin darasi mai girma. Da fari Hur ya kasance a cikin rundunar makiya, kuma daya daga cikin kwakandojin sojojin Yazidu. Shi ne wanda raundunarsa ta fara isa filin Karbala ta tsare rundunar Imam Hussaini. Sai dai saboda ganin yadda Imam Hussaini ya ke yin kyakkyawar mu'amala da shi, ya samu tasiri mai girma. Imam Hussaini ya baiwa Hur da rundunarsa da kuma dawakansu ruwan da za su sha. Wannan ne ya sa Hur ya fahimci gaskiya sannan ya mika kai a gare ta ya yi watsi da shugabancin rundunar da ya ke yi ta makiya ya shiga cikin rundunar Imam Hussaini. Ya yi yaki na jarunta har ya yi shahada a ranar Ashur'a.Wadannan labaran wani yanki ne kadan na jaruntar da iayalai da kuma sahabban Imam Hussaini su ka nuna a ranar Ashura. Sun yi yakin kare gaskiya cikin tsumai da kumaji. Hakan ya maida su zama wasu taurari masu haske ga duk wanda ya ke son riko da tafarkin gaskiya da fada da zalunci da shimfida adalci.Amincin Allah ya tabbata ga Hussaini da iyalansa da kuma sahabbansa
hausa.irib.ir
Ƙara sabon ra'ayi