Aikin Hajji {2}
Aikin Hajji {2}
A makon da ya gabata mun bayyana bangaren farko ne na aikin hajjin tamattu'i wato umuran tamattu'i wanda ya kunshi wajibai guda biyar:- [1] Ihrami [2] Dawafi sau bakwai [3] Sallar Dawafi raka'a biyu [4] Sa'ayi tsakanin safah da marwa sau bakwai [5] Aske wani abu daga gashin kai ko gemu ko gashin baki ko kuma yanke farce.Kuma mun bayyana cewa idan mutum ya gama gudanar da ayyukan umuran tamattu'i abubuwan da aka haramta masa aikatawa sun halatta gareshi, sai ya tube tufar haraminsa ya jira lokacin daura haramin hajjin tamattu'i. A shirinmu na yau zamu yi takaitaccen bayani ne kan bangare na biyu na aikin hajjin tamattu'i wanda ya kunshi wajibai goma sha uku kamar haka:- [1] Ihrami. [2] Tsayuwan-Arafah. [3] Tsayuwan Muzdalifah. [4] Jifan Shaidan. [5] Hadaya wato yanka ko suka. [6] Rage gashin kai ko askewa. [7] Dawafi. [8] Sallar Dawafi. [9] Sa'ayi wato tafiya tsakanin safah da marwa. [10] Dawafun-Nisa'i. [11] Sallar Dawafin-Nisa'i. [12] Kwana a Minah. [13] Jifan Shaidan a wajaje uku wato Ulah, Wusda da Akbah. Wadannan sune ayyukan aikin hajjin tamattu'i.Yadda ake gudanar da aikin hajjin tamattu'i a aikace:- Wajibi na farko a aikin hajjin tamattu'i shi ne Ihrami: Mahajjaci zai daura harami ne da niyyar yin aikin hajjin tamattu'i daga Makkah a lokacin da ya san zai riski tsayuwar-Arafah kafin gotawar rana wato kafin shigan lokacin sallar azahar a ranar tara ga watan zul-hajji, amma abin da ya fi shi ne, daura haramin aikin hajjin tamattu'i tun bayan sallar azahar din ranar tarwiya wato ranar takwas ga watan zul-hajji, kuma abin da aka fi so shi ne, mahajjaci ya daura haramin daga Masallacin ka'abah, sai ya fara talbiyya wato:
.Da wannan ne mahajjaci ya fara gudanar da wajibin farko na aikin hajjinsa na tamattu'i. Wajibi na biyu daga cikin ayyukan hajjin tamattu'i shi ne hawan-arafah wato tsayiwan arafah a ranar tara ga watan zul-hajji, inda mahajjaci zai kasance a filin arafah tun daga gotawar rana har zuwa faduwarta. Wajibi na uku daga cikin ayyukan hajjin tamattu'i shi ne tsayuwa a Muzdalifah, wato bayan faduwar rana, mahajjaci zai bar filin arafah ya tafi Muzdalifah. Muzdalifah sunan waje ne kuma ana kiran wajen da Mash'arul-haram, inda mahajjaci zai kwana a Muzdalifah, sannan idan ya wayi gari wato a rana ta goma ke nan ga watan zul-hajji kuma ranar sallah, sai ya tsaya a wurin har zuwa lokacin da rana zata fito, sannan ya tafi Minah domin gudanar da ayyukan ranar sallah.Wajibi na hudu daga cikin ayyukan hajjin tamattu'i shi ne Jifan- shaidan. A lokacin da mahajjaci ya bar Mazdalifah ya isa Minah a ranar sallah zai fara ayyukan wannan ranar ce da jifan-shaidan, wanda ake kiran wajen jifan na shaidan da Jamratul-Akbah a larabce, inda mahajjaci zai kudurta niyyar yin jifar, sannan ya gudanar da jifan shaidan da duwatsu guda bakwai, inda zai jefi shaidan da duwatsu bakwai daya bayan daya, wato ba zai hada duwatsun ya watsasu a lokaci daya ba. Wajibi na biyar daga cikin ayyukan hajjin tamattu'i shi ne hadaya wato yanka dabba ko suke rakumi. Wajibi ne yanka ko sukan da mahajjaci zai yi ya kasance bayan jifan shaidan, kuma dabbar da zai yanka ko soke ta kasance lafiyayyiya.Wajibi na shida daga cikin ayyukan hajjin tamattu'i shi ne saisaye ko aski, wato mahajjaci ya rage gashinsa ko yayi aski, amma anfi fifita yin aski musamman idan mahajjaci yana gudanar da aikin hajjinsa na farko ne. Amma hukuncin mace, rage gashinta zata yi kawai ba aski ba.Fadakarwa:-Da zaran mahajjaci ya gama gudanar da ayyukansa na ranar sallah a Minah, wato Jifan shaidan, hadaya da saisaye ko aski, to abubuwan da aka haramta masa sun halatta gareshi, amma ban da kusantar mace da sanya turare. Daga nan mahajjaci yana da zabi, idan ya ga dama a wannan ranar wato ranar goma ga watan zul-hajji ke nan, kuma ranar sallar idin lahiya, sai ya tafi makkah domin gudanar da sauran ayyukan aikin hajjinsa na tamattu'i, idan kuma mahajjaci ya ga dama, sai ya ci gaba da zama a Minah har zuwa ranar goma sha biyu ga watan zul-hajji.A nan Idan mahajjaci ya zabi tafiya zuwa Makkah ne domin gudanar da sauran ayyukan hajjinsa na tamattu'i, to ga yadda ake gudanar da ayyukan kamar haka:-Lokacin da mahajjaci ya isa Makkah zai gudanar da wajibi na bakwai daga cikin ayyukansa na hajjin tamattu'i, wato dawafin aikin hajjin tamattu'i. Inda zai kudurta niyyar gudanar da dawafin, wato zagaya dakin ka'aba sau bakwai, wanda zai fara dawafin ne daga wajen hajrul-aswad, dakin ka'aba yana hannunsa na hagun kamar yadda muka yi bayani a dawafin umuran tamattu'i. Wajibi na takwas daga cikin ayyukan hajjin tamattu'i shi ne sallar dawafi raka'a biyu a bayan maqama-Ibrahima idan akwai yiyuwar hakan, saboda cinkoson mutane.Wajibi na tara daga cikin ayyukan hajjin tamattu'i shi ne sa'ayi wato tafiya tsakanin Safah da Marwa sau bakwai, wanda mahajjaci zai fara gudanar da tafiyar daga Safah ya kare da Marwa.Fadakarwa:-Da zarar mahajjaci ya gudanar da dawafin hajjin tamattu'i da Sa'ayinsa wato tafiya tsakanin Safah da Marwa, sanya turare da ya haramta gareshi ya halatta. Wajibi na goma daga cikin ayyukan hajjin tamattu'i shi ne gudanar da dawafun-nisa'i, wato bayan mahajjaci ya kudurta niyya sai ya zaga dakin ka'aba sau bakwai, kamar yadda ake gudanar da sauran dawafi. Wajibi na goma sha daya daga cikin ayyukan hajjin tamattu'i shi ne sallar dawafun-Nasa'i raka'a biyu, wato bayan mahajjaci ya gama dawafun-Nasa'i, sai ya kudurta niyya yayi sallah raka'a biyu a bayan maqama-Ibrahima, amma ya isar masa ya gudanar da sallar a duk wajen da ya samu sarari a kusa da maqama-Ibrahima saboda gujewa cinkoson jama'a.Fadakarwa:-Dawafun-Nisa'i da sallarsa raka'a biyu ba su daga cikin rukunin aikin hajjin tamattu'i, wato idan mahajjaci ya bar su da gangan aikin hajjinsa bai baci ba, sai dai ya haramta a gareshi ya kusanci matarsa misalin saduwa da ita ko shafan jikinta ko kallonta da sha'awa, kamar yadda ita ma mahajjaciya data bar dawafun-Nisa'i da gangan wadannan abubuwa da muka ambata suka haramta gareta.Don haka da zarar mahajjaci ya gudanar da dawafun-Nisa'i da sallarsa kusantar matarsa ya halatta gareshi, kamar yadda ya halatta ga mahajjaciya ta kusanci mijinta. Saboda haka ne ake kirar dawafin da dawafun-Nisa'i, wato dawafin mata. Bayan mahajjaci ya gama gudanar da ayyukan hajjinsa na tamattu'i da suke Makkah a ranar sallar idi, wato ranar goma ga watan zul-hajji, to wajibi ne ya koma Minah a wannan ranar domin kwana a can.Wajibi na goma sha biyu daga cikin ayyukan hajjin tamattu'i shi ne kwana a Minah a daren ranar goma sha daya da goma sha biyu ga watan zul-hajji.Abin da ake nufi da kwana a Minah shi ne akalla mahajjaci ya kasance a Minah tsawon rabin dare, wato idan aka raba dare kashi biyu daga lokacin faduwar rana zuwa fitowar alfijir na gaskiya, to kasancewar mahajjaci a daya daga cikin kashi biyun ya gamsar, wato ko dai mahajjaci ya zauna a Minah daga faduwar rana zuwa tsakiyar dare ko daga tsakiyar dare zuwa fitowan alfijir.Wajibi na goma sha uku kuma na karshe daga cikin ayyukan hajjin tamattu'i shi ne gudanar da jifan-shaidan a wajaje guda uku wato Jamratul-Ulah, Jamratul-Wusdah da Jamratul-Aqbah, wanda ake kiransu da Jamra'tus-Salasa a larabce.Mahajjaci zai gudanar da jifan-shaidan ne a ranakun goma sha daya da goma sha biyu ga watan zul-hajji, kuma zai gudanar da jifar ce kafin lokacin sallar Azahar ko bayansa.Amma idan mahajjaci ya gama gudanar da jifar shaidan ta ranar goma sha biyu ga watan zul-hajji kafin gotawar rana, wato kafin shigan lokacin sallar Azahar, to ba zai fice daga Minah ba sai bayan gotawar rana.Wajibi ne mahajjaci ya fara gudanar da jifan na shaidan a Jamratul-Ulah sau bakwai, sannan Jamratul-Wusdah sau bakwai, sannan Jamratul-Aqbah sau bakwai. Dole ne jifar ta shaidan ta kasance da duwatsu guda bakwai, inda zai gudanar da jifar da dutse daya bayan daya, wato mahajjaci ba zai hada duwatsu ya watsasu a lokaci daya ba. Wannan shi ne takaitaccen bayani kan bangare na biyu na aikin hajjin tamattu'i, aikin hajjin da shi ne wajibin da ya hau kan mutumin da yake zaune nesa da garin makkah, nisan da ya kai kilometer tamanin da takwas.
hausa.irib.ir
Ƙara sabon ra'ayi