Jagora Imam Khamenei Ya Halarci Taron Juyayin Ranar Ashura A Husainiyar Imam Khumaini (r.a)

A daren yau Alhamis (14-11-2013) wanda ya yi daidai da ranar Ashura (goma ga watan Muharram) ne aka gudanar da taron zaman makokin shahadar Imam Husaini (a.s) da mabiyansa a Husainiyar Imam Khumaini (r.a) da ke gidan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

A yayin wannan taron wanda ake gudanar da shi don tunawa da yadda iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) da aka kama su a matsayin fursunonin yaki bayan waki'ar Karbala, Jagoran juyin juya halin Musulunci tare da wasu manyan jami'an gwamnati da na soji da suka hada da tsohon shugaban kasar Iran Dakta Mahmud Ahmadinejad bugu da kari kan dubban al'ummomi daban-daban na kasar Iran ne suka halarce shi. Kamar yadda Hujjatul Islam wal muslimin Sheik Aali ne ya gabatar da jawabi inda ya tabo bangarori daban-daban na abin da ya faru a Karbala ga iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a).

Har ila yau a wajen taron, mawakan Ahlulbaiti (a.s), Malam Samawati da Murtadha Tahiri ne suka gabatar da wakokin juyayi da bayanin abubuwan da ya sami Imam Husaini (a.s) da mabiyansa a Karbala.

Za'a ci gaba da gudanar da wadannan tarurruka na juyayin Ashura a Husainiyar ta Imam Khumaini (r.a) har zuwa ranar Juma'a mai zuwa, wacce ta yi daidai ga 11 ga watan Muharram.

Ƙara sabon ra'ayi