Yan Bindiga Sun Sace Wani Malamin Kirista Dan Faransa A Arewacin Camaroo

Wasu yan bindiga a arewacin Camaroo sun sace wani malamin kirista dan kasar faransa a jiya Alhamis.

 

Kamfanin dillancin labarai na Reuters daga yahunde ya ce yan bindiga kimani 15 sun shiga cucin PARISH da ke garin Nguetchewe, suka kama priest Georges Vandenbeusch sun kuma tafi da shi.

priest Georges, ya sami damar yin waya da ofishin jakadancin kasar Faransa kafin yan bindigan su shiga dakinsa a cikin cucin.

Reuters ya kara da cewa daga baya an gano jakarsa dauke da cheque Book dinsa a kan hanyar da ta kai kan iyaka da tarayyar Nigeria kilomita 10 daga garin.

Watani 11 da suka gabata ma, yan bindiga wadanda ake dangatawa da kungiyan nan ta Boko Haram sun sace iyalan wasu faransawa a yankin.

Wasu jami’an gwamnatin kasar Camaroo sun bayyanawa reuters cewa, mai yuwa yan bindigan sun kama shi ne don taimakon da yake bawa yan gudun hijiran da suka fito daga tarayyar Nigeria saboda rikicn da ke faruwa a can.

Ƙara sabon ra'ayi