...Rahotanni daga kasar Syria sun ce dakarun
Rahotanni daga kasar Syria sun ce dakarun gwamnatin kasar sun hallaka wasu manyan kwamandojin kungiyar Alka’ida biyu a yammacin jiya a kusa da garin Latakia da ke yammacin kasar. Mai aiko ma gidan talabijin din PressTV rahotanni daga yankin na Latakia ya ya habarta cewa, sojojin na Syria sun yi wa gungun ‘yan alkaida kwantan bauna a wani wuri da suka kafa tungarsu, inda suka bude musu wutar bindiga, a nan take suka hallaka wani adadi daga cikinsu, daga cikin wadanda suka mutu a wurin har da Abu Aiman Al-Iraki da kuma Abu Hamza Al-sa’udi, wadanda manyan jagororin kungiyar Alkaida ne da suka shiga kasar Syria suna yaki da gwamnatin kasar. Wannan farmaki na dakarun Syria ya zo ne kawana daya rak bayan wani makamancinsa da suka kai kan wani gungun na ‘yan alkaida a kusa da garin Latakia, wadanda suka shigo cikin kasar ta Syria daga kasashen duniya daban-daban domin yaki da gwamnatin shugaba Assad, inda a nan ma suka hallak 32 daga cikin mayakan na Alkaida, aka kuma kame wasu.
Ƙara sabon ra'ayi