Jami'an Tsaron Bahrain Suna Ci Gaba Da Kai Hari Wa Tarurrukan Ashura

Babbar jam’iyyar adawa da kasar Bahrain da kuma wasu kungiyoyin kare hakkokin bil’adama guda biyu na kasar sun zargi gwamnatin kasar da kokarin haifar da fitina ta mazhaba a kasar ta hanyar kai hare-hare kan tarurrukan Ashura da ‘yan Shi’an kasar suke gudanarwa.

 

 

Jam’iyyar Al-Wifaq da kuma Bahrain Center for Human Rights da kuma Bahrain Youth Society for Human Rights sun dauki hotunan da faifai na bidiyo na irin hare-haren da jami’an tsaron kasar ta Bahrain suke kai wa wajajen da ake gudanar da tarurrukan Ashura don tunawa da kisan gillan da aka yi wa jikan Manzo, Imam Husain (a.s) tare da mabiyansa a Karbala.

 

Daga cikin abubuwan da jami’an tsaron suke yi har da yayyaga tutocin Ashura da aka kakkafa bugu da kari kan kai hari wa mutane masu zaman juyayin ashuran bugu da kari kan lalata cibiyoyi da wajajen tarurruka na mabiya tafarkin Ahlulbaitin. Har ila yau kuma gwamnatin ta rufe shafuffukan internet da suke watsa irin wadannan tarurruka kai tsaye.

 

Gwamnatin kasar ta Bahrain wacce take samun goyon bayan gwamnatin Saudiyya ta jima tana kai hare-hare wajajen tarurruka na addini da mabiya tafarkin Ahlulbaiti (a.s) na kasar suke gudanarwa

Ƙara sabon ra'ayi