Kamfanin dillancin labaran SANA ya nakalto daga rundunar sojin kasar ta Syria cewa, a jiya dakarun gwamnatin sun fatattaki daruruwan ‘yan ta’adda da ke samun goyon bayan kasashen Amurka da Saudiyya daga yankuna da dama da ke arewacin Aleppo, tare da kashi wani adadi mai yawa daga cikinsu, wasunsu kuma sun tsre zuwa cikin kasar Turkiya.
A bangare guda kuma wasu rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan ta’adda na Syria sun harba makaman roka a jiya a cikin birnin Aleppo, inda suka kashe fararen hula 9 da suka hada da kananan yara ‘yan makaranta, yayin da wani adadi mai yawa na faraen hula suka samu raunuka.
Ƙara sabon ra'ayi