Rayuwar Al'umma

RAYUWAR AL'UMMA -1
Da sunan Allah mai Rahama mai Jin Kai
Aminci ya tabbata ga annabinsa da alayensa tsarkaka

Gabatarwa
Haka nan ne Allah ya halicci mutum daga yunbu, sai ya ba shi kyautar tunani da hankali, ya sanya wannan hankalin ya zama hujja a kansa domin ya gudanar da rayuwarsa bisa yadda ya dace, ya zama yana da sakamakon alheri a lahira saboda amfani da wannan hankali. Al'ummu suna da yawa tun da har yanzu, kuma rayuwarsu tana cike da darussa masu yawan gaske da tajribar da suka kutsa ta cikintsa suna masu gano abubuwa na ilimi da rayuwa a fagage masu yawan gaske, kuma suka hayayyafa sai 'ya'yansu suka maye gurbinsu, wannan mayewar tana nan tana gudana har zuwa karshen zamani.
Wannan hankalin da Allah ya yi wa mutum yana iya kasancewa na tunani (theory) kamar mantik (logic), ko na Falsafa (philosophy), ko ya kasance na hankalin aiki (practical) kamar na Al'ada (culture), ko na kyawawan halaye (ethics) sai dai dukkansa ana kiran sa hankali.
Amma rayuwar al'umma tana tafiya ne bisa hankalin al'adu da suka doru a kansu, kuma duk wani tunani da ya ci karo da al'ada to yana iya faduwa kasa warwas a wurin al'ummar don ba zai samu karbuwa ba. Sai dai maimaita wannan tunani da yawan kawo shi, da samun wasu mutane da zasu fara riko da shi a cikin al'umma yana iya kawo canji da karbuwarsa. Canji yana samuwa ne sannu-sannu har su samu shiga, idan suka samu karbuwa a wurin wasu bangare na al'umma sai su rika fadada har sai sun mamaye ta.
Sau da yawa fikirorin addinai suka fuskanci gaba mai tsanani matukar gaske, tarihin yaduwar kiristanci a daular Roma, da musulunci a sauran kasashe, da kuma mazhabobi a wasu wurare, dukkan wannan yana nuni da wannan lamarin mai cike da bayanai. Al'adu suna da karfin gaske matuka, don haka ne idan aka canja Falsafa (philosophya), manitk (logic), da halaye (ethics) suka koma wasu bangarori na rayuwa da al'adun al'umma, to wannan al'ummar ta gama samun ci gaba, kuma a yi mata albishir da kaiwa ga matakin kafa daular fifiko da zata samun jagorancin mafifita da alherai.
Don haka ne duk wani juyi da al'umma zata samu matukar ya tsaya a matsayin siyasa (politics), ko tattalin arziki (economy), ko karfin soja (defence), matukar ba ta samu juyi a wadancan fagage ba, to babu alherai masu yawa da zasu mamaye wannan al'ummar, kuma juyinta zai kasance na wani dan lokaci ne kawai. Tsarin gurguzu babban misali a wannan fage, domin duk da ya samu canji a wuraren da muka kawo, sai dai bai samu canji a wadancan fagage ba, don haka ne ya fuskanci rushewa. Don haka sanya wadancan fagagen a cikin al'adun mutane ta yadda zasu kasance sun shiga jikinsu sun zama jiki da tsoka, yana da muhimmancin gaske.
Sau da yawa idan zan yi rubutu nakan so in sanya alaka tsakanin fikirar da ake son isarwa da halayen mutane da abin da ya shafi rayuwarsu don ya kasance mai amfani gare su, don haka a wannan fagen na rubutun ilimin rayuwar al'umma abin da zan yi ke nan. Rashin kiyaye wannan lamarin ne ya sanya nisantar mutane daga wasu ilimomin ta yadda zasu ga ba da su a ke magana ba. A irin wannan ne zamu ga yadda Nietzsche jagoran 'yan edistentialism yake matukar sukan Arasto dalibin Aplato, yana ganin ya karkatar da falsafa ya fitar da ita daga cikin rayuwar mutane (duniyar kasa) ya mayar da ita rayuwar sama (tunanin kwakwalwa) ta yadda mutane zasu ji bahasosinta ba su shafi rayuwarsu ba. A lokaci guda zamu ga yadda Nietzsche yake yabon Sacrotics malamin Aplato saboda shi a zamaninsa ya sanya falsafa a cikin rayuwar mutane ne, bai yi mata makaranta ta musamman ba, bai sanya mata istilahohi masu wuyar ganewa gun mutane ba.
Wannan ita ce kuma mahangar sayyid khamna'i yayin da yake ganin dole ne falsafa, irfani, fikihu, halaye, da sauran fagagen ilimi su kasance zasu iya tafiya tare da rayuwar mutane, dole ne su nisanci kebantuwa da istilahohin tunanin dan 'adam kawai ba tare da sun kalli rayuwarsa ba kai tsaye. Don haka ne lallai ne a rubuce-rubucenmu mu sanya wannan lamari ya zama abin lura.
Idan muna son yin bahasi kan rayuwar al'umma to dole ne ke nan mu taba alakokin da suke tsakanin mutane, da jama'u, daidaiku, manya, kanana, masu mulki, mabiya, talakawa, mayalwata, alakar da take tsakaninsu, alakarsu da zamaninsu da wanda ya gabata da mai zuwa, alkarsu da wasunsu, alakarsu da wurin da suke rayuwa. Sannan kuma dole sai an taba bayani kan tunani, fikirori, addinai, da jam'iyyu, da sauran abubuwan da suke da alaka da wannan al'umma.
Da wannan ne zamu san cewa bahasin rayuwar al'umma bahasi ne mai yawa da fadin gaske, sai dai duk wani abu da za a tabo dole ne ya kasance yana da alaka da shi ta wani janibi don ka da ya fita daga bahasin.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation

Ƙara sabon ra'ayi