Zanga-Zangar Masar

Wasu majiyoyi a Masar sun ce fiye da mutane 120 ne suka rasa rayukansu sakamakon taho-mu-gama da aka yi tsakanin masu adawa da hambararren shugaban kasar Mohammad Morsi, da kuma 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi da ke neman a dawo da shi kan karagar shugabancin kasar.   A sanarwar da ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Masar ta bayar ta bayyana cewa mutane 20 ne suka rasa rayukansu sakamakon arangamar da bangarorin biyu suka yi, sai wasu majiyoyin sun ce adadin yah aura haka, yayin da majiyoyin kungiyar 'yan uwa musulmi ta Muhammad Morsi ta ce adadin ya haura mutane 120, kuma akasarinsu 'ya'yan kungiyar ne.   Miliyoyin mutane ne dai suke ci gaba da gudanar da zanga-zanga a Masar tun daga jiya Juma'a, inda masu goyon bayan Morsi suka taru a masallacin Rabi'at Adwiyyah a birnin Alkahira, masu adawa da shi kuma suka cikin dandalin Tahrir, da Ittihadiyya, kamar yadda aka gudanar da irin wannan gangami na bangarorin biyu a biranan kasar.

Ƙara sabon ra'ayi