Rikicin Siyasar Tunisiya

Gwamnatin kasar Tunisia ta zargi yan salafiyya masu tsakanin kishin addini a kasar da laifin bindige
shugaban wata jam’iyyar adawa ta kasar a jiya .
Kamfanin dillancin Labaran DPA na kasar Jamus ya nakalto ministan cikin gida na kasar ta Tunisia Lotfi Ben Jeddu yana fadar haka a yau jumma’a.
Jeddu ya kara da cewa Bubakar Hakim wani dan salafiya na da hannu wajen kisan Mohammad Brahmi a jiya, kamar yadda yake da hannu wajen kisan Chokri Bel’eed watanni 6 da suka gabata.
Ministan ya ce a binciken da suka gudanar a gidan Hakim sun gano makamai sun kuma gano cewa an kashe Mohammad Brahmi ne da irin bindigan da aka kashe Chokri Bel’eem da shi, wato bindiga mai fadin milimita 9 wanda kuma yake kamar bindiga mai sarrafa kansa da kansa.
Ben Jiddu ya ce kafin haka ana tuhumar Bubakar Hakim da shigo da makamai daga kasar Libya. Akwai wadanda aka zargi da aka kama, amma shi Hakim ya arce daga kasar tun da dadewa.
Ministan yana bada wannan sanarwan ne a dai dai lokacinda dubban masu zanga zanga suka taru a kofar ma’aikatar cikin gidan kasar a birnin Tunis, inda suke zargin Jam’iyyar Annahda ta masu kishin addini kuma mai iko da kasar da kashe Mohammad Brahmi.
Banda wannan kungiyar kwadagon kasar ta Tunisia ta yi kira ga ma’aikata da su shiga yajin aiki kan kisan dan adawar.

Ƙara sabon ra'ayi