Turai da Hizbullah

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar da wani bayani da a cikinsa ta bayyana cewa, kudirin tarayyar turai da ya saka ta a cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda hakan ba shi da wata kima, domin kuwa kudiri ne da haramtacciyar kasar Isra'ila ta shirya ta mika wa tarayyar turai, ita kuma ta amince da shi bisa matsin lambar Amurka.   Bayanin ya ce babu wani abu wai shi bangaren soji na kungiyar Hizbullah, domin kuwa kungiya daya ce mai yaki da zaluncin haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummar musulmi, tare da kore duk wata farfaganda da ke cewa kungiyar ta mallaki kamfanoni ko wuraren kasasuwanci ko kudade ko makamai a wasu kasashen ketare, inda bayanin ya ce duk wannan na daga cikin makircin da ake kitsa wa kungiyar, ta hanyar haratacciyar kasar Isra'ila gami da Amurka da kuma hadin baki da wasu gwamnatoci.   Jim kadan bayan amincewa da wannan kudiri da ministocin harkokin wajen kasashen tarayyar turai suka yi a birnin Brussel na kasar Belgium, gwamnatocin Amurka da Isra'ial suka fito suka yi na'am tare da nuna matukar farin cikinsu da hakan.

Ƙara sabon ra'ayi