ADDU'O'IN WATAN AZUMI RANAKUN GOMA NA BIYU

ADDU'O'IN WATAN AZUMI RANAKUN GOMA NA BIYU

ÏÚÇÁ Çáíóæã ÇáÍÇÏí ÚóÔÑ: [ Çááøóåõãøó ÍóÈøöÈú Åöáóíøó Ýöíúåö ÇáÇöÍúÓÇäó¡ æóßóÑøöåú Åöáóíøó Ýöíúåö ÇáÝõÓõæÞó æóÇáÚöÕúíÇäó¡ æóÍóÑøöãú Úóáóíøó Ýöíúåö ÇáÓøóÎóØó æóÇáäøöíÑÇäó¡ ÈöÚóæúäößó íÇÛöíÇËó ÇáãõÓúÊóÛöíËöíäó ].

Addu'ar Rana ta Sha daya:
Ya Ubangiji ka soyar da kyakkyawa zuwa gareni, ka kyamatar da fasikanci da sabo gareni, ka haramta mini fushi da wuta a cikinsa, da taimakonka, ya mai agazar masu neman agaji.

ÏÚÇÁ Çáíæã ÇáËÇäí æÇáÚöÔÑæä: [ Çááøóåõãøó ÇÝúÊóÍú áöí Ýöíúåö ÃóÈúæÇÈó ÝóÖúáößó¡ æóÃóäúÒöáú Úóáóíøó Ýöíúåö ÈóÑóßÇÊößó¡ æóæóÝøöÞúäöí Ýöíúåö áöãõæÌöÈÇÊö ãóÑúÖÇÊößó¡ æóÃóÓúßöäøöí Ýöíúåö ÈóÍúÈõæÍÇÊö ÌóäøóÇÊößó¡ íÇ ãõÌöíÈó ÏóÚúæóÉö ÇáãõÖúØóÑøöíäó ].

Addu'ar Rana ta Sha Biyu:
Ya Ubangiji ka bude mini kofofin falalarka a cikinsa, ka saukar mini da albaratunka a cikinsa, ka datar da ni ga abubuwan yardarka a cikinsa, ka kuma saukar da ni farfajiyar aljannarka, ya mai amsa addu'ar masu matukar damuwa (matsuwa).

ÏÚÇÁ Çáíæã ÇáËÇáË ÚóÔÑ: [ Çááøóåõãøó ØóåøöÑúäöí Ýöíúåö ãöäó ÇáÏøóäóÓö æóÇáÇóÞúÐÇÑö¡ æóÕóÈøöÑúäöí Ýöíúåö Úóáì ßÇÆöäÇÊö ÇáÇóÞúÏÇÑö¡ æóæóÝøöÞúäöí Ýöíúåö áöáÊøõÞì æóÕõÍúÈóÉö ÇáÇóÈúÑÇÑö¡ ÈöÚóæúäößó íÇÞõÑøóÉó Úóíúäö ÇáãóÓÇßöíäö ].

Addu'ar Rana ta Sha Uku:
Ya Ubangiji ka tsarkake ni daga dauda da kazanta a cikinsa, ka sanya mini hakurin abubuwan kaddara a cikinsa, ka datar da ni ga takawa da abota da nagari a cikinsa, da taimakonka, ya sanyin idaniyar miskinai.

ÃÚãÇá Çáíæã ÇáÑÇÈÚ ÚóÔÑ
ÃÚãÇá Çáíæã ÇáÑÇÈÚ ÚóÔÑ ÏÚÇÁ Çáíæã ÇáÑÇÈÚ ÚóÔÑ: [ Çááøóåõãøó áÇ ÊÄÇÎöÐúäöí Ýöíúåö ÈöÇáÚóËóÑÇÊö¡ æóÃóÞöáúäöí Ýöíúåö ãöäó ÇáÎóØÇíÇ æóÇáåóÝóæÇÊö¡ æóáÇ ÊóÌúÚóáúäöí Ýöíúåö ÛóÑóÖÇ áöáúÈóáÇíÇ æóÇáÂÝÇÊö¡ ÈöÚöÒøóÊößó íÇÚöÒøó ÇáãõÓúáöãöíäó ].

Addu'ar Ranar Sha Hudu:
Ya Ubangiji kada ka rike ni da laifuffuka, ka yaye mini kurakurai da gafala a cikinsa, kada ka sanya ni mazubar bala'i da aibobi a cikinsa, da buwayarka ya buwayar musulmi.

ÏÚÇÁ Çáíóæã ÇáÎÇãÓ ÚóÔÑ: [ Çááøóåõãøó ÇÑúÒõÞúäöí Ýöíúåö ØÇÚóÉó ÇáÎÇÔöÚöíäó¡ æóÇÔúÑóÍú Ýöíúåö ÕóÏúÑöí ÈöÅäÇÈóÉö ÇáãõÎúÈöÊöíäó¡ ÈöÃóãÇäößó íÇ ÃóãÇäó ÇáÎÇÆöÝöíäó ].

Addu'ar Rana ta Sha Biyar:
Ya Ubangiji ka arzuta ni biyayyar masu kaskan da kai a cikinsa, ka yalwata mini kirjina da komawar nan ta masu kaskan da kai gareka a cikinsa, da amincinka, ya amincin masu jin tsoro.

ÏÚÇÁ íæã ÇáÓÇÏÓ ÚÔÑ
Çáíæã ÇáÕÇÏÓ ÚÔÑ ÃÓÃáß Çááøåõãøó áÇ Åáå ÅáÇø ÃäÊó ÈÇÓãß ÇáøÐí ÚóÒóãÊ Èå Úóáì ÇáÓøãÇæÇÊ ÇáÓÈÚ æÇáÇÑóÖíä ÇáÓøÈÚö ¡ æãÇ ÎóáÞóÊó ÈíäõåãÇ æÝíåöãÇ ãä ÔóíÁò æÃÓÊÌíÑõ ÈÐáßó ÇáÇÓãö ¡ Çáøáåõãøó áÇ Åáå ÅáÇø ÃäÊó ÇáÌÃõ Åáíßó ÈÐáß ÇáÇÓãö ¡ Çááøåõãøó áÇ Åáå ÅáÇø ÃäÊó Ãõæãä ÈÐáßö ÇáÇÓã ¡ Çááøåõãøó áÇ Åáåó ÅáÇø ÃäÊó ÃÓÊÛíËõ ÈÐáß ÇáÇÓãó ¡ Çááøåõãøó áÇ Åáå ÅáÇø ÃäÊó ÃÊÖÑøÚõ ÈöÐöáßó ÇáÇÓãö ¡ Çááøåõãøó áÇÅáåó ÅáÇø ÃäÊó ÃÓÃáßõ ÈãöÇ ÏÚæÊßó ÈÐáöß ÇáÇÓãö ¡ Çááøåõãøó áÇ Åáå ÅáÇø ÃäÊó ÃÓÃáõßó ÈãÇ ÏóÚæÊßó ÈÐáßö ÇáÇÓãö ¡ Çááøåõãøó áÇ Åáåó ÅáÇø ÃäÊó íÇ Çááå íÇ Çááå íÇ Çááå ¡ ÃäÊó æÍÏßó áÇ ÔóÑíßó áßó ¡ ÃÓÃáõßó íÇ ßÑíãõ íÇ ßÑíãõ íÇ ßÑíãõ ÈÌÏøßó æÌæÏößó æÝóÖáßó æóãäøß æÑÃÝÊößó æÑÍãÊößó æãÛÝÑÊößó æÌãÇáßó æÌáÇáößó æÚÒøÊßó ¡ áãÇ ÃæÌÈÊó áí Úáì äóÝÓßó ÇáÊí ßóÊÈúÊó ÚóáíåÇ ÇáÑøÍãÉó Ãä ÊóÞæáõ ÞóÏ ÂÊíúÊõßó íÇ ÚóÈÏí ãóåãÇ ÓÃáóÊäí Ýí ÚÇÝíóÉò Åáì ÑöÖæÇäí ¡ æÃä ÊóÈÚËäí ãöäó ÇáÔøÇßÑíäó . ÃÓÊÌíÑõ æÃáæõÐõ ÈÐáöß ÇáÇÓãö ¡ Çááøåõãøó ÈáÇ Åáåó ÅáÇø ÃäÊó ¡ æÈßõáø ÞóÓóãò ÃÞÓãóÊó Èå Ýí Ãõã ÇáßöÊÇÈö Çáãßäæäö Ýí ÒõÈÑõ ÇáÇæøáíäó ¡ æÝí ÇáÕõÍõÝ æÝí ÇáÒóÈõæÑ æÝí ÇáÕõÍõÝö æÇáÃáæÇÍö æÝí ÇáÊæÑÇÉö æÇáÅäÌíáö æÝí ÇáßÊÇÈö ÇáãõÈíä æÝí ÇáÞõÑÂä ÇáÚÙíãö ¡ æÃÊæÌøå Åáíßó ÈãõÍãøÏò äÈí ÇáÑøÍãÉö Úáíå æÂáå ÇáÓøáÇãõ æÇáÕøáæÇÊõ æÇáÈóÑßÇÊõ ¡ íÇ ãõÍøãÏõ ÈÃÈí ÃäÊó æÇõãí ¡ ÃÊóæÌøåõ Èßó Ýí ÍÇÌÊí åÐå æÌóãíÚö ÍóæÇÆÌí Çáì ÑóÈøßó æóÑÈí ¡ áÇ Åáåó ÅáÇø åõæ ÇáÑÍøãäõ ÇáÑÍíãõ . Çááøåõãøó ÇÌÚóáäí ãä ÃÝÖóá ÚÈÇÏßó äÕíÈÇð Ýí ßõáø ÎíÑò ÊÞÓãå Ýí åÐå ÇáÛóÏÇÉ ¡ ãä äæÑò ÊåÏí Èå ¡ Ãæ ÑóÍãÉò ÊóäÔÑõåÇ ¡ Ãæ ÚÇÝíÉò ÊÌááåÇ ¡ Ãæ ÑÒÞò ÊóÈÓØñåñ ¡ Çæ ÐóäÈò ÊÛÝÑõåõ ¡ Ãæ Úóãáò ÕÇáÍò ÊõæÝøÞõ áå ¡ Ãæ ÚÏæò ÊÞãÚå¡ Ãæ ÈóáÇÁò ÊÕÑöÝõåõ ¡ Ãæ äÍÓò ÊõÍæøáõåõ Åáì ÓÚÇÏÉò . íÇ ÃÑÍóãó ÇáÑøÇÍãíäó ÃÓÃáß ÈÇÓãößó ÇáæÇÍöÏö ÇáÃÍÏö ¡ ÇáÝóÑÏ ÇáÕøãÏ ¡ ÇáæöÊÑ ÇáãõÊÚóÇá ¡ ÑÈø ÇáäøÈíøíäó ¡ æóÑÈø ÅÈÑÇåíãó ¡ æÑÈø ãõÍãøÏò ¡ ÝÇäí Çõæãäõ Èßó æÈÃäÈíÇÆßó æÑõÓõáß ¡ æÌóäøÊß æäÇÑßó ¡ æÈóÚËß æäõÔæÑßõ ¡ æõæÚÏßõ ææÚíÏßõ ¡ ÝÇÌäõÈäí íÇ Åáåí ããøÇ ÊßÑåõ Çáì ãÇ ÊõÍöÈ ¡ æÇÞÖö áí ÈÇáÍÓäì Ýí ÇáÂÎÑöÉö æÇáÇæáì ¡ Åäøß æáíøõ ÇáÎíÑö æÇáãæÝÞõ æÃäÊó ÃÑÍã ÇáÑøÇÍãíäó.

Addu'ar Rana ta Sha Shida:
Ya Ubangiji babu wani abin bauta sai kai, ina rokonka da sunanka wanda da shi ne ka karfafa a kan sammai bakwai da kassai bakwai, da abin da ka halitta a tsakaninsu da cikinsa na daga wnai abu, kuma ina neman kariyarka da wannan sunan, Ya Ubangiji babu wani abin bauta sai kai, ina dogara da kai zuwa gareka da wannan sunan, Ya Ubangiji babu wani abin bauta sai kai, ina imani da wannan sunan, Ya Ubangiji babu wani abin bauta sai kai, ina neman taimako da wannan sunan, Ya Ubangiji babu wani abin bauta sai kai, ina kaskantar da kai da wannan sunan.
Ya Ubangiji babu wani abin bauta sai kai, ina rokonka da abin da na kira ka da wannan sunan, Ya Ubangiji babu wani abin bauta sai kai, ya Allah, ya Allah, ya Allah, kai kadai kake ba kada wani abokin tarayya gareka, ina rokonka ya mai girma, ya mai girma, ya mai girma, da baiwarka, da falalarka, da burinka, da tausayinka, da rahamarka, da gafararka, da kyawunkak, da girmanka, da buwayarka, tun da ka wajabta wa kanka wacce ka wajbata mata yi mini rahama da ka ce hakika na zo maka ya bawana da dukkan abin da ka roke ni zuwa ga yardata a cikin lafiya, kuma ka tashe ni cikin masu godiya.
Ina neman mafaka da dogaro da wannan suna, Ya Ubangiji da babu wani abin bauta sai kai, da kuma dukkan wani roba da ka yi a cikin uwar littafi mai daraja a cikin littattafai magabata na farko, a cikin suhufi, da zabur, da suhufi da alluna, da attaura, da injila da cikin littafi mabayyani da kur'ani mai girma, kuma ina fuskata zuwa ga Muhammad annabin rahama (a.s) ma'abocin tsira da albarka, ya Muhammad ina fansarka da uwata da ubana, ina fuskantar bukatuna wannan da kai, da kuma a cikin dukkan bukatuna zuwa ga Ubangijinka kuma Ubangijina, babu wani abin bauta sai shi mai rahama mai jin kai. Ya Ubangiji ka sanya ni daga mafifitan bayinka rabo a cikin dukkan wani alheri da kake rabawa a wannan rana, na daga haske da kake shiryarawa da shi, ko wata rahama da kake yada ta, ko lafiya da kake bayar da ita, ko wani arziki da kake shimfida shi, ko zunubi da kake gafarta shi, ko wani aiki na gari da kake datarwa gareshi, ko kuma wani makiyi da kake lallasa shi, ko wani bala'I da kake kawar da shi, ko wani shu'umi da kake mayar da shi rabauta, ya kai mafi jin kan masu jin kai. Ina rokonka da sunanka makadaici, tilo, daya abin nufi, tak makadaici, Ubangijin annabawa, kuma Ubangijin ibrahim, kuma Ubangijin Muhammad, hakika ni na yi imani da kai da annabawanka da manzanninka, da aljannarka da wutarka, da tashinka da yadawarka, da alkawarinka da narkonka, to ka nisanta ni daga abin da kake ki zuwa ga abin da kake so ya Ubangiji, ka biya mini kyakkyawa a lahira da duniya, hakika kai ne masoyin alheri mai datarwa, kuma kai ne mafi tausayin masu tausayi.

ÏÚÇÁ Çáíæã ÇáÓÇÈÚ ÚóÔÑ: [Çááøóåõãøó ÇåúÏöäöí Ýöíúåö áöÕÇáöÍö ÇáÇóÚúãÇáö¡ æóÇÞúÖö áöí Ýöíúåö ÇáÍóæÇÆöÌó æóÇáÇãÇáö íÇãóäú áÇ íóÍúÊÇÌõ Åöáì ÇáÊøóÝúÓöíÑö æóÇáÓøõÄÇáö¡ íÇ ÚÇáöãÇð ÈöãÇ Ýöí ÕõÏõæÑö ÇáÚÇáóãöíäó Õóáøö Úóáì ãõÍóãøóÏò æóÂáöåö ÇáØøöÇåöÑöíäó ].

Addu'ar Rana ta Sha Bakwai:
Ya Ubangiji ka shiryar da ni ga kyawawan ayyuka a cikinsa, ka biya mini bukatu da buri a cikinsa, ya wanda ba ya bukatar fassara da tambaya, ya masani da abin da yake cikin zukatan talikai, ka yi tsira da aminci ga Muhammad da alayensa tsarkaka.

ÏÚÇÁÇáíæã ÇáËÇãöä ÚóÔÑ: [ Çááøóåõãøó äóÈøöåúäöí Ýöíúåö áöÈóÑóßÇÊö ÃóÓúÍÇÑöåö¡ æóäóæøöÑú Ýöíúåö ÞóáúÈöí ÈöÖöíÇÁö ÃóäúæÇÑöåö¡ æóÎõÐú Èößõáøö ÃóÚúÖÇÆöí Åöáì ÇÊøöÈÇÚö ÂËÇÑöåö¡ ÈöäõæÑößó íÇãõäøöæÑó ÞõáõæÈö ÇáÚÇÑöÝöíä ]ó.

Addu'ar Rana ta Sha Takwas:
Ya Ubangiji ka fadarka da ni ga albarkatun lokacin sahur a cikinsa, ka haskaka zuciyata da hasken haskakanka a cikinsa, kuma ka riki kowacce daga gabobina zuwa ga bin tafarkinsa, da haskenka, ya mai haskaka zukatan masana.

ÏÚÇÁ Çáíæã ÇáÊÇÓÚ ÚóÔÑ: [ Çááøóåõãøó æóÝøöÑú Ýöíúåö ÍóÙøöí ãöäú ÈóÑóßÇÊöåö¡ æóÓóåøöáú ÓóÈöíáöí Åöáì ÎóíúÑÇÊöåö¡ æóáÇ ÊóÍúÑöãúäöí ÞóÈõæáó ÍóÓóäÇÊöåö¡ íÇåÇÏöíÇ Åöáì ÇáÍóÞøö ÇáãõÈöíäö ].

Addu'ar Rana ta Sha Tara:
Ya Ubangiji ka tanadar mini da rabona daga albarkarsa a cikinsa, ka saukaka mini tafarkina zuwa ga alheransa, kada ka haramta mini karbar kyawawansa, ya mai shiryarwa zuwa ga gaskiya mabayyaniya.

ÏÚÇÁ Çáíóæã ÇáÚÔÑæä: [ Çááøóåõãøó ÇÝúÊóÍú áöí Ýöíúåö ÃóÈúæÇÈó ÇáÌöäÇäö¡ æóÃóÛúáöÞú Úóäøöí Ýöíúåö ÃóÈúæÇÈó ÇáäøöíúÑÇäö¡ æóæóÝøöÞúäöí Ýöíúåö áöÊöáÇæóÉö ÇáÞõÑúÂäö¡ íÇ ãõäúÒöáó ÇáÓøóßöíäóÉö Ýöí ÞõáõæÈö ÇáãõÄúãöäöíäó ].

Addu'ar Rana ta Ishirin:
Ya Ubangiji ka bude mini kofofin aljannarka a cikinsa, ka kulle mini kofofin wuta a cikinsa, kuma ka datar da ni a cikinsa ga karatun kur'ani, ya mai saukar da nutsuwa a cikin zukatan muminai.

Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation
Friday, 21 August 2009

Ƙara sabon ra'ayi