ADDU'O'IN WATAN AZUMI GOMA NA FARKO

ADDU'O'IN WATAN AZUMI GOMA NA FARKO

ÏÚÇÁ Çáíóæã ÇáÃæá
[ Çááøóåõãøó ÇÌúÚóáú ÕöíÇãöí Ýöíúåö ÕöíÇãó ÇáÕøóÇÆöãöíäó¡ æóÞöíÇãöí Ýöíúåö ÞöíÇãó ÇáÞÇÆöãöíäó¡ æóäóÈøöåúäöí Ýöíúåö Úóäú äóæúãóÉö ÇáÛÇÝöáöíäó¡ æóåóÈú áöí ÌõÑúãöí Ýöíåö íÇÅöáåó ÇáÚÇáóãöíäó¡ æóÇÚúÝõ Úóäøöí íÇÚÇÝöíÇ Úóäö ÇáãõÌúÑöãöíäó

Addu'ar ranar Farko:
Ya Ubangiji ka sanya azumina azumin masu yin azumi a cikinsa, tsayuwata kuwa tsayuwar masu tsayuwa, ka kuma fadakar da ni daga baccin masu gafala, ka yafe mini a cikinsa ya Ubangijin talikai, ka yi mini afuwa ya mai yin afuwa ga masu laifi.

ÏÚÇÁ Çáíóæã ÇáËÇäí: [ Çááøóåõãøó ÞóÑøöÈúäöí Ýöíúåö Åöáì ãóÑúÖÇÊößó¡ æóÌóäøöÈúäöí Ýöíúåö ãöäú ÓóÎóØößó æóäóÞöãÇÊößó¡ æóæóÝøöÞúäöí Ýöíúåö áöÞöÑÃóÉö ÂíÇÊößó¡ ÈöÑóÍúãóÊößó íÇÃóÑúÍóãó ÇáÑøóÇÍöãöíäó ].

Addu'ar Rana ta Biyu:
Ya Ubangiji ka kusantar da ni a cikinsa zuwa ga yardarka, ka nisantar da ni fushinka da azabobinka, ka sani mai dacewa da karanta ayoyinka a cikinsa, saboda rahamarka, ya mafi jin kan masu jin kai.

ÏÚÇÁ Çáíóæã ÇáËÇáË: [ Çááøóåõãøó ÇÑúÒõÞúäöí Ýöíúåö ÇáÐøöåúäó æóÇáÊøóäúÈöíåó¡ æóÈÇÚöÏúäöí Ýöíúåö ãöäó ÇáÓøóÝÇåóÉö æóÇáÊøóãúæíåö¡ æóÇÌúÚóáú áöí äóÕöíÈÇ ãöäú ßõáøö ÎóíúÑò ÊõäúÒöáõ Ýöíúåö ÈöÌõæÏößó¡ íÇ ÃóÌúæóÏó ÇáÇóÌúæóÏöíäó ].

Addu'ar Rana ta Uku:
Ya Ubangiji ka arzuta ni tunani da fadaka a cikinsa, ka nisantar da ni daga wauta da gabunta a cikinsa, ka sanya mini rabo daga dukkan alheri a cikinsa saboda baiwarka, ya mafi baiwar masu baiwa.

ÏÚÇÁ Çáíóæã ÇáÑÇÈÚ: [ Çááøóåõãøó Þóæøöäöí Ýöíúåö ÚóáÆ ÅöÞÇãóÉö ÃóãúÑößó¡ æóÃóÐöÞúäöí Ýöíúåö ÍóáÇæóÉó ÐößúÑößó¡ æóÃóæúÒöÚúäöí Ýöíúåö áÇóÏÇÁö ÔõßúÑößó ÈößóÑóãößó¡ æóÇÍúÝóÙúäöí Ýöíúåö ÈöÍöÝúÙößó æóÓóÊÑößó¡ íÇÃóÈúÕóÑó ÇáäøóÇÙöÑöíäó ].

Addu'ar Rana ta Hudu:
Ya Ubangiji ka karfafe ni acikinsa a kan tsayar da umarninka, ka dandana mini zakin ambatonka, ka kuma agaza mini a cikinsa a kan gode maka saboda darajarka, ka kiyaye ni a cikinsa da kiyayewarka da kariyarka, ya kai mafi gamin masu dubawa.

ÏÚÇÁ Çáíóæã ÇáÎÇãÓ: [ Çááøóåõãøó ÇÌúÚóáúäöí Ýöíúåö ãöäú ÇáãõÓúÊóÛúÝöÑöíäó¡ æÇÌúÚóáúäöí Ýöíúåö ãöäú ÚöÈÇÏößó ÇáÕøóÇáöÍíäó¡ æÇÌúÚóáúäöí Ýöíúåö ãöäú ÃóæúáöíÇÆößó ÇáãõÞóÑøóÈöíäó¡ ÈóÑóÃúÝóÊößó íÇ ÃóÑúÍóãó ÇáÑøóÇÍöãöíäó ].

Addu'ar Rana ta Biyar:
Ya Ubangiji, ka sanya ni daga masu neman gafara a cikinsa, ka sanya ni daga bayinka na gari a cikinsa, ka sanya ni daga masoyanka makusanta a cikinsa, saboda tausasawarka, ya mafi jin kan masu jin kai.

ÏÚÇÁ Çáíóæã ÇáÓÇÏÓ: [ Çááøóåõãøó áÇÊóÎúÐõáúäöí Ýöíúåö áöÊóÚóÑøõÖö ãóÚúÕöíóÊößó¡ æóáÇ ÊóÖúÑöÈúäöí ÈöÓöíÇØö äóÞúãóÊößó¡ æóÒóÍúÒöÍúäöíö Ýöíúåö ãöäú ãõæÌöÈÇÊö ÓóÎóØößó¡ Èöãóäøößó æóÃóíÇÏöíßó íÇãõäúÊóåì ÑóÛúÈóÉö ÇáÑøóÇÛöÈöíäó ].

Addu'ar Rana ta Shida:
Ya Ubangiji kada ka kyale ni in fada cikin sabonka a cikinsa, kuma kada ka doke ni da bulaliyar azabarka, ka kawar da ni daga sabonka a cikinsa, da baiwarka da karfinka, ya matukar kololuwar burin masu buri.

ÏÚÇÁ Çáíóæã ÇáÓÇÈÚ: [ Çááøóåõãøó ÃóÚöäøöí Ýöíúåö Úóáì ÕöíÇãöåö æóÞöíÇãöåö¡ æóÌóäøöÈúäöí Ýöíúåö ãöäú åóÝóæÇÊöåö æóÂËÇãöåö¡ æóÇÑúÒõÞúäöí Ýöíúåö ÐößúÑóßó ÈöÏóæÇãöåö¡ ÈöÊóæúÝöíÞößó íÇ åÇÏöíó ÇáãõÖöáøöíäó ].

Addu'ar Rana ta Bakwai:
Ya Ubangiji ka taimaka mini a kan azuminsa da tsayuwarsa a cikinsa, ka nisantar da ni daga laifuffukansa da sabonsa, ka arzuta ni ambatonka da dawwamarsa a cikinsa, da dacewarka, ya mai shiryar da batattu.

ÏÚÇÁ Çáíóæã ÇáËÇãöä: [ Çááøóåõãøó ÇÑúÒõÞúäöí Ýöíúåö ÑóÍúãóÉó ÇáÇóíúÊÇãö¡ æóÅöØúÚÇãó ÇáØøóÚÇãö¡ æóÅöÝúÔÇÁó ÇáÓøóáÇãõ¡ æóÕõÍúÈóÉó ÇáßöÑÇãö¡ ÈöØóæúáößó íÇãóáúÌóÃó ÇáÇãöáöíäó ].

Addu'ar Rana ta Takwas:
Ya Ubangiji ka arzuta ni rahama a cikinsa, ka ciyar da ni abinci, da ya da sallama, da abotar masu daraja, da karfinka ya mafakar masu guri.

ÏÚÇÁ Çáíóæã ÇáÊÇÓÚ: [ Çááøóåõãøó ÇÌúÚóáú áöí Ýöíúåö äóÕöíÈÇ ãöäú ÑóÍúãóÊößó ÇáæÇÓöÚóÉö¡ æóÇåúÏöäöí Ýöíúåö áöÈóÑÇåöíäößó ÇáÓøóÇØöÚóÉö¡ æóÎõÐú ÈöäÇÕöíóÊöí Åöáì ãóÑúÖÇÊößó ÇáÌÇãöÚóÉö¡ ÈöãóÍóÈøóÊößó íÇ Ãóãóáó ÇáãõÔúÊÇÞöíäó ].

Addu'ar Rana ta Tara:
Ya Ubangiji ka sanya mini rabo daga rahamarka mai yalwa a cikinsa , ka shiryar da ni ga hujjojinka masu karfi a cikinsa, ka riki makwankwadar kaina zuwa ga yardarka matattariya, da sonka, ya guri masu bege.

ÏÚÇÁ Çáíóæã ÇáÚÇÔÑ: [ Çááøóåõãøó ÇÝúÊóÍú áöí Ýöíúåö ÃóÈúæÇÈó ÇáÌöäÇäö¡ æóÃóÛúáöÞú Úóäøöí Ýöíúåö ÃóÈúæÇÈó ÇáäøöíúÑÇäö¡ æóæóÝøöÞúäöí Ýöíúåö áöÊöáÇæóÉö ÇáÞõÑúÂäö¡ íÇ ãõäúÒöáó ÇáÓøóßöíäóÉö Ýöí ÞõáõæÈö ÇáãõÄúãöäöíäó ].

Addu'ar Rana ta Goma:
Ya Ubangiji ka bude mini kofofin aljanna a cikinsa, ka kulle mini kofofin wuta a cikinsa, ka sani mai dacewa da karanta kur'ani a cikinsa, ya mai saukar da nutsuwa a zukatan muminai.

Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation
Friday, 21 August 2009

Ƙara sabon ra'ayi