Amsar soke-soke kan Ismar Ma'asumai - 4

Littafi: Hakikar Shi'anci
Amsar soke-soke kan Ismar Ma'asumai - 4
Wallafar: Sheikh Wa'ili (r)
Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id

Ra’ayin Dan Taimiyya a Kan Isma
Ibn Taimiyya a yayin da ya ke yi wa Shi'a raddi a kan fadin su: Lalle samuwar Imami ma’asumi abu ne da babu makawa da shi bayan wafatin Manzo (s.a.w) saboda hukunce- hukunce suna sabuntuwa da daidai da yanayi, kuma yanayoyi suna cenjawa, kuma domin kada a samu sabani a cikin fassara Kur’ani da kuma fahimtar Sunna, kuma da a ce ismar Manzo da kuma cika wannan addinin sun isar da ba a samu sabani ba, sai ya tabbata cewa babu makawa da samun Imami ma’asumi wanda zai bayyana mana ma’anonin Kur'ani ya kuma ayyana mana manufoffin shari’a kamar yadda dama wannan ne abin da aka nuface shi da shi, har dai zuwa abin da aka ambata zuwa karshen abin da suka ambata a wannan matsayar.
Ibn Taimiyya ya ce: Ahlus-sunna ba za su sallama a ce Imami ya zama shi ne zai kiyaye shari’a bayan yankewar wahayi ba, domin wannan ya hau kan kowa ne, ka ga shiri’a, idan har mutane da yawa suka ciro ta, hakan yafi fiye da ciratowar mutum daya, ka ga makaranta ma’asumai ne a wajen hardace Kur'ani da kuma isar da shi, kuma masu hadisai ma’asumai ne a wajen kiyaye hadisai da da kuma isar da shi, kuma fakihai ma’asumai ne a wajen yin magana da kuma kafa hujja , kuma Ibn Taimiyya ya saba da Razi a nan, idan har isma a wajen Razi tana tabbata ne da haduwar al’umma, to a wajen Ibn Taimiyya tana tabbata ne ga wasu jama’a ne daga mutane kamar makaranta da fakihai da masu hadisai, kuma a nan IbnTaimiya ya shardanta isma domin tabbatar da kiyaye abin da shari’a ta kunsa kamar dai yadda yake a wajen Shi'a da wasun su, to don me zai halar ta ga wasu sannan ya haramta ta ga wani? Adadin ma’asumai a wajen Shi’a bai wuce goma sha hudu ba, kuma su ne tarayyar zababbun mutanen da Allah ya kebance su da falaloli masu yawa bisa ijma’in bangarorin Musulmai, to don me muke musanta musu isma sannan kuma mu halartata ga wasun su?

Ra’ayin malaman Sunna a Kan Isma
Za mu iya cewa jamhurun malaman sannan sun tafi a kan ingancin hadisin da aka ruwaito daga Manzo (s.a.w) "sahabbai na kamar taurari ne duk wanda ku ka yi koyi da shi kun shiriya " kuma wannan hadisin ya lazimtar da ismar sahabai kamar yadda wannan bayanin zai zo daga sashin su, domin ingancin yin koyi da su da kuma yi masa biyayya a cikin zalunci da zai faru saboda kasancewar sa wanda yake aikata zunubai kuma wannan shi ne abin da ya faru saboda kasantuwar su ba ma’asumai ba ne, wannan yana nufin ke nan Allah ya yi umarni da abi mai sabo da kuma yin zalunci ko da kuwa a kan sa ne, idan kuma bai yi aiki da abin da Manzo ya ce ba, wannan yana nufin ya saba wa Kur'ani ke nan: "Abin da Manzo yazo muku da shi ku yi riko da shi" .
A nan kuma sahabi yana cirato umarnin Manzo idan ka ce lalle Allah Madaukaki ya umarce mu, ida ka ce lalle Manzo ya yi umarni da mukarbi hadisi daga adali sikka saboda fadinsa madaukakin: "Ya ku wadanda suka yi imani idan fasiki ya zo muku da labari ku yi bincike don kada ku auka wa mutane bisa jahilci". Hujurat: 6. Wacce bisa abin da a ke fahimta daga wannan ayar cewa labarin (adali) amintacce hujja ne kuma mu ba ma karbar umarni sai daga adali daga cikin su. Sai na ce :Lalle wannan yana yin nuni a bisa cewa a cikin su akwai wanda ba adali ba kuma wannan ne abin da muke son tabbatarwa.
A dunkule lalle lazimin wannan hadisin da aka ambata shi ne ismar sahabbai, kuma ba mu ji wanda yake musawa wadannan ba, to don me idan Shi'a sun ce imamai ma’asumai ne ake yi musu nakadi?.
Tafatazani Da Isma
Tafazani wanda yana daga cikin manyan malamai yana cewa a cikin littafinsa Sharhil Makasid: Mutanenmu sun kafa hujja a kan rashin wajabcin isma bisa ijma’i a kan imamancin Abubakar da Umar da Usman, tare da ijma’i a kan cewa bai zama wajibi su zama ma’asumai ba, duk da cewa sun kasance ma’asumai a bisa ma’anar cewa tun lokacin da suka yi imani sun kasance suna da dabi'ar nisantar sabo tare da ikon yin su !.
1- A nan Tafazani yana tabbatar da ismar halifofi guda uku
2- Yana cewa: Lalle ismar su ba wajiba ba ce, da nufin cewa ba a tilasta musu a kan ta ba in ba haka ba ba zai yiwu ba a sauwara ratayar hukunce- hukunce da lamurrann halitta ba, kadai an halicce su da cikkken zabi da tanadi na su zam ma’asumai a fagen hukunce- hukuncen ayyyuka da motsin yau da na gobe.
3- Abin da yake nufi da cewa isma malaka ce da take hana mai ita yin zunubi, ba bisa yanayin kwace zabi ba, kuma wannan shi ne ainihin abin da Shi'a suke fadi a cikin imamai kuma duk wanda yake so ya koma litattafan Shi'a na akida a kan bahasin isma, bayan wannan kuma don me a ke ta wannan iface-ifacen yak u masaumai.

Shamsuddin Al’isfahani Da Nur Muhammad A kan Isma
Hafiz Nur Muhammad da Shamsudddin al’isfahani na farko a cikin tarihin maziyarta madaukakiya, na biyu kuma kamar yadda algadir ya nakalto daga gare shi cewa: Lalle halifa Usman ma’asumi ne , kuma ya nakalto shi ne daga littafinsa madali’il Anzar kuma wadanann mutanen biyu daga malaman Ahlus-sunna ne.
Sheikh Iji Da Isma
Adurrahmanil ijabi ma’abocin littafin almawakif a cikin shi wannan littafin ya tafi a kan cewa ismar halifofi bisa yanayin da tafzazi ya fadi a cikin abin da muka ambata a kan sa na cewa lalle ita mallaka ce a gare su wacce bata tabbatar da sance zabi , kuma shi ma yana daga cikin malaman Sunna, kuma lalle wannan zagayen (jaular) ta bayyana mana cewa ba su ne kadai suka tafi a kan isma ba, ballatana ma malaman Sunna ma sun tafi a kan hakan, in haka ne ta wace fuska za a jingina ta Abdullahi dan Saba’, kuma ta wane bangaren za a yi wa shia’a nakadi a kan yin riko da ita.
Ba ina so in sokarwa mai karatu litattafa da wallafe-wallafen Ahlus-sunna ba ne, kakika litattafan su cike suke da wannan, amma zan dan bijiro da ra’ayin wani marubucin karni na ishirin kuma a cikin wannan lokacin da duniya ta zama gari daya, shi kam na rantse da Allah yana daga cikin mafi yawa yin adalci wajen yin rubutu a kan Shi'a, amma duk da haka abubuwan da aka kafa a cikin zukata sai da suka yi saura suna ta yin aikin su.
Na yi imani cewa wannan mutumin ya yi bincike a cikin litattafan Shi'a da ma na wasun su kafin ya rubuta wannan littafin nasa wannan kuwa saboda abin da na gani a tatter da shi n masdarori masu yawa, tare da kaddara cewa ya leka ra’ayoyin Ahlus-sunna a kan a wadannan maudu’an, to don me za a musantawa Shi'a su kadai banda wasun su, idan kuma har bai karanta ba (leka ba), -kuma wannan ne abin da nake kore faruwarsa-, don me zai yi rubutu a kai?.

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.comwww.hikima.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center

Ƙara sabon ra'ayi