Amsar soke-soke kan Ismar Ma'asumai - 3

Littafi: Hakikar Shi'anci
Amsar soke-soke kan Ismar Ma'asumai - 3
Wallafar: Sheikh Wa'ili (r)
Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id

Matsayar Sunna a kan Isma
Kafin mu shiga cikin maudu’in namu zan dan waiwayar da mu zuwa wata kissa wacce ta ke ita ma tana dauke da ta ta manuniyar a kan wannan maudu’in, ita ce: An kai wani mutum da ake bin sa bashi wajen alkali, sai alkalinn ya tambaye shi: Shin wannan mutumin da ya kawo karar ka yana binka bashi ? sai ya ce a yanan bi na bashi amma ban yarda da yana bi na ba, wannan kissar ta yi kama da wanda yake musanta mana isma kuma a lokaci guda sai kuma ka ga ya na da’awarta.
Tare da cewa muna sanya sharadin isma ne ga Imami domin tabbatar da cikakken tsaro da kariya domin isuwar hukunce- hukunce da akidu zuwa hannun mu ingantattu. Kuma da tabbatar da nisanta daga rarraba wacce take faruwa saboda kasantuwar shagaba ba ma’asumi ba ne, ba muna so isma ta zama wani daukaka ce da muke dorawa a kan wuyan imamai ba ne, suna da falalolin da sun ishe su daga wannan, kamar yadda ba mu kasance masu yin linkaya a cikin kogin jin fifici da jin cewa mun tsira ba, sam-sam domin kawai muna son yin ko wani abu bisa yadda yake, mu kuma raya duniyar dare da dukkanin bambamce-bambancen ta, lalle a kan maganar imamanci mun barranta da mu zamo wadanda su ke ganin kasantuwar Imami daga cikin wadanda muke ganin su daga mutane kawai, domin idan suka zamo da irn wannan yanayin da tsarin, to mene ne bambancin kuma da me suka zama zababbu har sa zamo masu yin hukunci a kan mutane, alhali a cikin mutanen akwai wadanda suka fi su tsayuwa da dagewa da cencneta. Wadannan su ne abubuwan da muke nufatan abayan isma, ba wai isma wata aba ce ta daban ba wacce ba ta dan Adamtaka ba, kamar yadda wasu su ke surantawa. Isma a mahangar mu nagarta ce da ke sawa a kiyaye shari’ar Allah Madaukaki nazarce da kuma kiyaye ta daga wasanni a aikace, kuma manya-manyan malaman Sunna sun tafi a kan haka, a lokaci guda kuma suna musanta mana yin riko da ita, kuma ga ma wasu misalsali daga maganganun su domin ma kasan ingancin abin da muka nasabta musu.
Arrazi: Yayin da Razi zo yi wa Shi'a raddi a kan ismar Imamai, sai ya tafi a kan cewa: Babu bukata zuwa Imami ma’asumi, domin al’umma yayin da ta hadu zata zama abar tsarewa (ma’sumiya) saboda dafifi da haduwar al’umma a kan kuskure, bisa fadin Manzon Allah (s.a.w) abu ne mai yiwuwa . "Al’umma ta ba zata hadu a kan bata ba".
Idan muka rufe idon mu daga kallon ingancin wannan hadisin ko rashin ingancin sa, sai mu yi tambaya, shin irin wannan ijma’in abu ne mai yiwuwa ta yadda zamu game dukkanin musulmi na gabas da na kudu? Ta yiwu a ce musulmin da suke kamantawa wannan ijma’in sune ma’abota warwarewa da kullawa ne, sai mu yi tambaya su wane ne kuma nawa ne adadinsu, kuma shin an taskace su a wani wuri ne? Kuma meye dalili a bisa hakan? Sannan mu kuma yi tambaya: Ashe ba komai ake nufi da haduwar ta su face sai hada su daya bayan dayan ba, idan har zai yiwu dayan su ya yi kuskure, zai yiwu dukkanin wadanda suka hadu a daidaikunsu su yi kuskure. Lalle Ibn Taimiyya ya amsa wannan tambayar da cewa, bai zama lazimi gaba dayansu su yi kuskure ba domin tarayya tana kebance- kebancen da ba a samu a daidaiku.
Kuma misalin wannan kamar misalin loma daya ce wacce ba ta kosarwa a yayin da da waya suke kosarwa, kuma sanda daya tana karyuwa a yayin da da yawa ba sa karyuwa har dai zuwa inda ya ce Manzo (s.a.w) ya ce: Shaidan yana tare da mutum daya kuma yafi nisanta daga mutum biyu , ban sani ba ta wace fuska za a kamanta tsakanin kasantuwar lomomi suna kosarwa da kuma kasantuwar daya bata kosarwa da kuma tsakanin kasancewar tarayya tana kaiwa ga isma da kuma rashin tsaruwar mutun daya, domin loma tana dauke da yiwuwar ta kosar da wani bangare ayyanan ne ta yadda idan ka kara wata a kan ta sai tarayyar wadannan daidaikun lomomin su hadu su bada koshi cikakke, haka ma sanda tana dauke da wani gwargwado na karfi, idan ta hadu da wasunta sai ta ba da cikakken karfi, miye alakar wannan da mutum daya wanda yake iya yin kuskure? Ba zai iya zama wani bangare na inganci ba ta yadda idan a kan hada shi da wasun sa zai zama ciko na inganci ba, balle ma zai ba da akasin sakamakon da ake bukata ne, domin mutum daya a nan yana kamanta rinjayen masu kuskure ne, ta yadda idan aka hada shi da misalin sa, sai kuskuren ya rubanya sai ya zama babban kuskure, lalle wannan kiyasi ne tare da mararrabiya a tsakani, wannan ta wani bangaren ke nan.
Ta wani bangaren kuma, lalle Ibn Taimiyya bai kore tunanin imamanci ba kadai, ya kore kasantuwar ta a kan mutum daya ne kawai, kai ka ce yana jin haushin ta kasance ga mutum daya ne, amma da za a danganta ta ga wasu mutane to ba komai, ta bangare na uku kuma, kadai an shardanta isma ne ga al’umma domin a sami sikka da kuma tabbatar da amintar hukunce-hukunce wanda shi ne ainihin hadafin da Shi'a suka tafi a kan sa, kuma yanzu zan cirato maka ra’ayin sa dalla-dalla:

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.comwww.hikima.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center

Ƙara sabon ra'ayi