Amsar soke-soke kan Ismar Ma'asumai - 1

Littafi: Hakikar Shi'anci
Amsar soke-soke kan Ismar Ma'asumai - 1
Wallafar: Sheikh Wa'ili (r)
Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id

Fasali Na Uku
Saboda Me Aka Danganta Shi’a Da Abdullahi dan Saba’
A wajen amsa wannan tambayar ne babbar manufar wannan kissar gabaki dayan ta yake boyuwa, kakika tunanin shi’anci a kan imamanci da abin da yake danfare da ita da kuma matsayan da a ka sajjalawa (bawa) Shi'a a tsakanin bangarorin Musulmai na daga Shi'a da wasun su, idan ka koma zuwa tushen su, daga dalilan sa na Kur’ani da hadidi ta yiwu sama kasa ta koma sama, saboda lamarin wasici da isma da makamancin su sun wuce lamarin shugabancin- a mahangar Shi'a- ga wanda bai cika wadannan sharadan ba kuma wannan ita ce babbar musiba, kuma wane tunani ne yafi hadari fiye da wannan, don me kuwa ba za a gwama tushen Shi'a da na Yahudawa ba, a kuma kirkiro masa mutum-mutumi a matsayin ragon layya, sai a samu damar jefa wa Shi'a zargi, da wadanda suka rika daga gareta, kuma a rika nuna su da cewa su fitattu ne daga Musulumci, wadanda suka bata tatihin al’umma kuma suka dasa akidu sababbi wadanda ba na Musulumci ba a cikin akidun ta, kuma haka Abdullahi dan Saba’ ya aikata, da a ce da gaske ne ya aikata hakan! duk da cewa hankula da ma’aunai ba su yarda da faruwar hakan ba.
Kari a kan abin da muka ambata, akwai wani sababin na daban da ya sa aka halicci Abdullahi dan Saba’ wanda Dakta Ahmad mahmud Subhi ya yi nuni zuwa gare shi, wannan kuwa bayan da ya bijiro da ra’ayin Daha Husain a yayin da ya yi nuni zuwa wahamcin samuwar Abdullahi dan Saba’, Dakta Ahmad Subhi ya ce:
Da alamun cewa lalle kai mutukar malaman tarihi da marubutan mazhabobi a kan hakikanin abubuwan da dan saba’ ya aikata yana komawa ne zuwa wani sababi na daban wanin wanda Dakta Daha Husain ya ambata, kakika abubuwa na siyasa manya- manya sun faru a Musulumci kamar kashe Usman, sannan yakin Jamal, kuma lalle manya- manyan sahabbai sun yi musharaka a cikin su haka matar Manzo (s.a.w) kuma dukkanin su sun rarraba su na yakar juna, kuma dukkanin wadannan fare- faren suna cin karo da (wujdanin) shu’urin ko gamsuwar musulmin da yake biye da tarihin sa na siyasa, ya zama an jarrabci Musulumci irin wannan jarrabar kuma manyan- manyan sahabban da suka yi yaki tare da Manzo (s.a.w) kuma sukayi tarayya a wajen kafa Musulumci, babu makawa zai dora nauyin faruwar wannan abubuwan a kan wuyan wani, kuma baya daga cikin abin da hankali zai karba a dora nauyin wadannan fare-faren ga bakidaya a kan manya- manyan sahabban wadanda suka yi bala’i kyakykyawa. Don haka sai ya zama babu makawa ya dora nauyin wannan lamarin gaba daya a wuyan dan Saba’, don haka ke nan shi ne wanda ya tada fitinar da ta kai ga kashe Usman kuma shi ne ya harzuka rundunoni guda biyu a ranar jamal domin su gamu a lokacin da Ali da Dalhatu da Zubair suke a gafale, amma a cikin tarihin da tunani yake rike da shi, shi ne cewa a wuyan sa ne mafi girma rarrabar akidun Musulumci ya doru ta hanyar bayyanar Shi'a, wannan ita ce fassasrar ta kai mutukar da marubutan firkoki da masu mazhabibi suka yi, musamman ma salafiyyawa da masu tarihi: A bisa hakikanin rawar da Abdullahi dan Saba’ ya taka. Sai dai a she ba abin ban mamaki ba ne, wanda ya sabon-shiga cikin Musulumci ya yi abin da yake so kamar haka ba, ya motsa tarihin Musulumci na siyasa da na akida bisa yanayin da ya tabbata alhali manya- manyan sahabbai suna gani
Bayan wannan masaninyar a kan rudanin lamarin Abdullahi dan Saba’ wanda muka kare gama a kai, bari mu yi gaba domin mukamo zaren ta daya bangaren bisa ga abin da muke tsammanin, wanda shi ne danganta akidar Shi'a da Abdullahi dan Saba’ da kuma abin da suka jingina izuwz gare shi na daga akidun Shi'a domin mu nemi sanin asalinta a musulunci, da haka ne zamu magance dagewa a kan samuwar dan Saba’ ko kuma rashin samuwar sa domin ya tabbata cewa lalle wannan akidar asalin ta daga Musulumci ne, sai ya zama babu wata kima bayan haka da zata yi saura a kan rashin samuwar dan Saba’ ko samuwar sa, bari mu fara tabbatar da hakan daga maudu’in wasiyya.
1- Imam Ali Wasiyyin Annbi Ne:
Mun riga mun fadi a abin da ya gabata cewa yana daga cikin hukunce- hukuncen Musulumci mutum ya yi wasici kafin mutuwar sa da abin da yake son yin tasarrufi a cikin sa bayan mutuwar sa a cikin abin da ya mallaka na daga kayayyakinn rayuwa, kuma mun ambaci cewa lalle a rayuwar Manzo (s.a.w) ya kasance ba ya fita daga madina domin yin wata tafiya koda ta kwana daya ce, face sai ya sanya halifa a madina. Ta yaya zai bar lamarin wannan al’ummar kara zube a bayan sa, ya sanya ta a cikin rudani ba tare da ya yi wasici ko ya zabi mutumin da zai tafiyar da lamari a bayan sa ba, gama cewa lalle wannan matsalar tuni alkaluman marubuta suka gamsar ta ita daga mabanbantabn bangarori bana so in dawo zuwa abin da ya gudana a kan ta abin da ya ke gaban mu a nan shi ne mu bayyana cewa mas’alar wasiyya ta samo asali ne daga Kur'ani da Sunna. Amma Kur'ani ya sanya Ali abokin tarayya a cikin lamarin shugabanci na baki daya kuma ya sanya imamancinsa ci gaba ga isar da sakon Allah tun da an riga an kulle annabtaka daga lokacin da Manzo ya rasu.
Allah Madaukaki ya ce: "Kadai waliyyin (shugaban ku shi ne Allah da Manzonsa da wadanda suka yi imani wadannan da suke tsaida salla kuma suke bada zakka alhali suna cikin ruku’u". Kuma lalle mun ambaci yadda wannan ayar ta sauka akan Ali da kuma abin da yake damfare da ita na daga lazimce-lazimce a wani wajen a cikin wannan littafin. Amma Sunna madaukakiya kuwa akwai ruwayoyi managarta masu yawa da suka bayyana cewa lalle Manzo (s.a.w) ya yi nassi da wasicin Ali a mafi yawan warare, daga cikin wuraren akwai:
Yayin da ayar "Ka gargadi `yan’uwan ka makusanta" shura’a /214 ta sauka, sai ya tara makusantansa, su arbain ya tanadar musu cinyar akuya sannan ya nemi su wazirce shi a kan lamarin kira zuwa ga Allah, alokacin ba wanda ya tashi sai Ali, sai ya riki wuyan sa ya ce wannan ne dan’uwana kuma wasiyyi na kuma halifa na a cikin ku, ku ji daga gare shi ku bi. Sai mutanen suka ta shi suna dariya suna cewa da Abi Dalib: Ya umarce ka, ka ji daga danka kuma ka bi.
Kuma Ibn Abil Hadid a cikin littafinsa sharhin Nahjul balaga ya yi fasali guda gamsasshe a kan lamarin wasicin Imam Ali (a.s) daga Annabi (S.AW.) kuma ya kosar da wannan maudu’in, kuma mai karatu zai iya komawa gare shi. A yanzu dai ka riga ka ji cewa wasiyya ta gudana ta harshen Manzo (s.a.w) bisa lafazin ta da ma’anar ta, tare da haka zaka ga wadannan mutanen suna cewa lalle maudu’in wasiyya Abdullahi dan Saba’ ne ya kirkiro shi, kuma da sannnan zaka ji- da zaka ce musu lalle wasiyya tana da masdarin ta (asalin ta) a Sunna- wanda zai ce maka wadannan hadisai ne da Shi'a suka dasa su ta harshen Sunna.
2- Isma (Rashin yin Sabo da Kuskure)
Lamarin isma lamari ne mai mihimmancin gaske musamman a mahangar Shi'a, dama Musulumci baki daya, don haka ya zame mini larura in tsawaita a kan sa saboda tana damfare da abubuwa masu mihimmancin da babu makawa da mu yi bayanin su (a sansu).
Isma dai a luga: Ita ce tsaruwa, daga wannan ne fadinsa madaukaki "Da sannu zan fake zuwa dutse, zai tsare ni daga ruwa" surar hudu/43. Amma a isdilahi malaman akida: kuma, ludufi ce da Allah Madaukaki yake ba da shi ga baligi ta yadda zai zama bashi da wata dama ta barin bin Allah da kuma yin sabo tare da ikon sa a kan hakan.
Mafi fitowa sarari daga wannan ta’arifin shi ne cewa lalle isma babu jingino a cikin ta, ba komai ba ce face sai kama hannu daga wajen Allah da kuma tanadi daga bawa. Don haka tafi kama da a ce malami ya kula da dalibin sa saboda ya sami shi wanda yake da cikakken iko wajen karbar ilimi sama da waninsa.
Kuma lalle al’umma ta hadu a kan ismar Annabawa daga ganganta karya a cikin abin da suke isarwa daga Allah Madaukaki bayan haka kuma sun saba akan yiwuwar ya aikata abin da ya ke kore isma bisa rabkanuwa ko mantuwa, daidai ne dalilan su a cikin wannan sn kasance na ji da kunne ko kuma na hankali, a bisa zuwa ko rashin zuwa da abin da yake kore isma, sashin malaman Ahlus-sunna sun tafi a kan halaccin faruwar kowane zunubi daga gare su, karami ne ya kasance ko babba kai har ma kafirci, kuma mai karatu zai iya komawa zuwa ra’ayiyin Bakalani da Razi da Gazali a kan ra’ayin imamanci dalla-dalla, a yayin da wasu kuma suka yi fasali a kan hakan amma ba su kai zuwa ga wannan iyakar ba, a wajen wofintar da su daga isma.
Amma Shi'a sun tafi a kan ismar Annabawa kai tsaye kafin aiko su da bauann sa, kuma sun zo da dalilai masu yawa a kan hakan. Fakhrur Razi a cikin littafinsa Ismatul Anbiya’i, ya bijiro da lamarin, haka ma Shekh Majlisi a cikin Biharu ya zo da shi dalla-dalla, abin da ya ke gaba na anan ismar Imamai domin shi ne mahallin bahasi na, lalle ismar annabawa abu ne wanda yake tabbatacce a wajen Shi'a kuma Shi'a sun tabbatar da ita ga Imami da dalilai na hankali da na ruwaya zan takaita wajen ambatar wasun su kuma wanda yake neman kari zai iya komawa zuwa litattafai da kuma manya- manyan litattafai da suke magana a kan wannan.

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.comwww.hikima.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center

Ƙara sabon ra'ayi