Asalin Larabawa da Mazhabobi - 3
Littafi: Hakikar Shi'anci
Asalin Larabawa da Mazhabobi - 3
Wallafar: Sheikh Wa'ili (r)
Tarjamar Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id
Sunna Da Ilimin Gaibi
Bayan da muka riga muka yi nuni a kan zuwa cewa lalle Shi'a Imamin da yake da cikakken tanadin da Allah madaukaki zai kwararo masa daga hasken sa da ilimin sa saboda idan har aka samu wanda zai iya karba to babu rowa a cikin falalarsa madaukaki, saboda haka ilimin gaibi shi a kan kan sa a ra’ayin Shi'a na Allah ne madaukaki, amma ilimin Ahlul-baiti ko dai ya zamo kwararowa ce ta kai tsaye daga wajen Allah Madaukaki ta hanyar ilhama ko kuma zantarwa ko kuma ta wasidar Annabi, haka ne ba ma musanta samuwar wadanda su ke yin guluwi a kan Ahlul-baiti, amma mukam mun barranta daga wadannan, kuma da sannu zamu shude zuwa wannan sai dai abin da nake so nace shi ne: Lalle Ahlus-sunna suna tabbatar wa shuwagabannin su sanin gaibi kamar yadda `yan’shia suke yi kuma suna ganin ana zantar da su, daga cikin irin wadannan misalsalin, akwai abin da Dabari ya ruwaito a cikin tafsirin sa ga aya ta 25 daga sura haj.
"Kuma ba mu aiko wani Manzo ko Annabi gabanin ka ba…" zuwa karshen ayar. Sai ya ce ya zo daga Ibn Abbas cewa ya kasance yana karata ayar kamar haka ko Annabi ko mai zantarwa. Muslimata dan Kasim dan Abdullah ne ya ambance shi kuma Safiyanu dan Umar dan Dinar ya ruwaito shi daga Ibn Abbas, Muslimata ya ce: Sai muka samu masu ba da hadisi a rike suke kam da annanbta domin sun yi magana akan abubuwa madaukaka fiye da labarin gaibi, kuma sun yi furici da boyayyar hikima kuma suka zama sun dace a cikin abin da suka fadi kuma aka kare su a cikin abin da suka fadi kamar misalin Umar dan Khaddabi a cikin kissar mayaka da kuma abin da ya yi furuci da shi na wanda yake hujja ce madaukakiya. Wannan shi ne abin da Kurdabi ya ruwaito shi , Siyudi ma ya ruwaito wannan kira’ar da aka ambata kuma ya yi magana akan masu zantarwa a cikin tafsirin Durrul Mansur, ka koma can .
Buhari ya ruwaito a cikin littafinsa babin darajojin Umar, ya ce: Manzo (s.a.w) ya ce: Lalla akwai a gabanin ku na daga Banu isr’ila wasu mazaje suna yin magana ba tare da sun zamo annanbawa ba, kuma idan har akwai makamancinsu a cikin al’ummata to Umar ne, kamar yadda muslim ya fitar da shi a cikin sahihinsa a cikin babin falalar Umar daga A’isha daga Manzo (s.a.w) lalle ya kasance akwai wadanda ake yi wa ilhama a gabaninku idan kuwa akwai wani daga cikinsu a cikin al’ummata, to Umar ne .
Kuma lamarin bai tsaya a kan shuwagabanni ba ya kai har ya kai ga Imrana dan Husain, daga Mudrif ya ce: Imrana dan Husain ya ce da ni: Ashe ba na zantar da kai wani hadisi ba ko Allah ya amfanar da kai da shi, lalle Manzo ya hada tsakanin hajji da umra kuma har ya rasu bai hana ba, kuma Kur’ani bai sauka yana mai haramtawa ba, na kasance ina ba da habisi har sai da na gajiya sai na daina, sai kuma na daina kasawa, sai hadisin ya dawo. Haka nan kowanne daga cikin Darumi da Muslim duk sun ruwaito wannan hadisin a sahihansu .
Ban sani ba mene ne alakar kasa magana da guduwar hadisin? Sanin wannan yana wajen Husain, Allah ya rahamshe shi.
Balllantana ma abin da suka ce na Umar dan Abdul’aziz halifan Umawayya cewa Hidhir ya kasance yana tafiya tare da shi, kuma yana zance da shi kamar yadda Ibn Hajar ya ruwaito a Tahzib .
Bayan dukkanin wadannan abubuwan da muka fadi shin zai sa ya zama Ahlul-baiti su zama suma suna daga cikin wadanada ake kwararo musu ilimi ko kuwa? Mafi rinjayen zato shi ne har yanzu ishkalin ba zai gushe ba yana nan, kuma lalle dai Shi'a sune gullawa ko kuma masu cenja addini saboda suna cewa Imamai sun san gaibi.
Na hudu: Abin da Ustaz Faragal ya musanta na matsayin Imaman Ahlul-baiti ya zamo ya biyo bayan matsayin Manzo (s.a.w) kai tsaye a wajen Shi'a, kuma wadanda da ake nufi su ne Imamai goma sha biyu kawai banda wasun su, kuma Shi'a ba su ne suka ajiye imamai a wannan matsayin ba, su Shi'a sun bi umarnin sama ne a matsayin su na bayi, Allah Madaukaki yana cewa: "Kadai shugaban ku shi ne Allah da Manzonsa da kuma wadanda suka yi imani wadannan da su ke tsaida salla kuma suke ba da zakka alhali suna cikin ruku’u". 56: Ma’idah. Ruwayoyi sun zo da yawa a kan cewa ta sauka ne a kan Imam Ali kuma ta sanya shi abokin tarayya a cikin shugabanci, kuma kowanne daga Fahrurraz a cikin tafsirin sa da Ibn Jarir Dabari, sun ruwaito wannan a cikin littafinsu, haka ma Baidhawi a cikin tafsirin sa da Ibn hayyan a cikin tafsirin sa da kuma Zamakhshari a cikin tafsirin sa da Ibn kasir a cikin tafsirin sa da kuma makamancin su, sannan bayan Kur'ani mai girma Sunnar Annabi ta ba shi wannan matsayin. Manzo (s.a.w) yana cewa: "Kai a wajena kamar Haruna na a wajen musa sai dai cewa babu Annabi bayana, kuma wannan hadisin yana daga cikin hadisai mutawatirai, kuma ma’abota sahihai sun fitar da shi, daga cikin su akwai Buhari da Muslim da a cikin ingantattun su a cikin babin falalolin Ali na sahih Buhari haka ma a Sahih Muslim.
`Ya`yan Ali ne su ke bin sa a bayan sa, kuma Annabi (s.a.w) ne ya sanya su a wannan matsayin, kuma babu wani abu da yake yin nuni a kan haka sama da sanya su da ya yi a matsayin tagwarorin Kur'ani, a inda yake cewa: Na bar muku masu daraja guda biyu littafin Allah da kuma `ya`yan gida na mutakar kun yi riko da su ba za ku taba bacewa a baya na ba har abada..h.k. , yanzu kuma mu koma zuwa tunani irin na Sunna; zamu samu cewa yana ajiye Imaman sa a irin ainihin wannan matsayin ba tare da musantawa ba, balle ma mahangar ta su tana ganin cewa Annabi (s.a.w) wanda shi da wahayi ake saita shi da zai wadatu daga bukatuwa ba daga wadannan Imaman. Hakim yana fadi a cikin mustadrak da sanadi zuwa Huzaifatu binil Yamani: Na ji Manzo (s.a.w) ya na cewa: "Hakika na himmantu da aika mutane zuwa sasanni su rika koyar da mutane sunnoni da farillai kamar yadda isa dan Maryam ya tura Hawariyyun, sai aka ce da shi to mai ya hana ka tura Ababakar da Umar sai ya ce: Ban wadatu daga gare su ba a cikin addini domin su kamar ji ne da gani . Balle ma Sunna sun ba wa sahabbai matsayin da ya yi daidai da matsayin Annabi ta bangaren kasantuwar zancensu da ayyukansu hujja ne da sanya su matsayin madogarar shari’a. Musa Jarullah yana fadi a cikin Washi’a "Mu ne fakihan Ahlus-sunna wal Jama’a muna sanya sunnar shaikhunnai guda biyu (Abubakar da Umar) a matsayin tushen wanda ya yi daidai da sunnonin mai shari’a annabin rahama wajen tabbatar da hukuncin shari’a cikin rayuwar al’umma da gudanar da daula, kuma lalle halifanci ne shiryayye ma’asumi irin ma’asumancin Manzanci, mai nagarta da zai tabbatar da rukunan addinin Musulumci ". Kaga halifofi kamar yadda Jarullah yake kawo nassi akan su a nan abubuwa ne da suka yi daidai da sunnar Annabi da kuma nassin Kur'ani, kuma halifofi ma’asumai ne kamar dai Annabi (s.a.w) kuma lalle sun yi rabebeniya da Annabi, (s.a.w) su suke rike da rabin hukunce-hukuncen da aka kafa Musulumci a kan su, Annabi (s.a.w) kuma yana dauke da kaso na biyu, kuma Imam gazali yana cewa: Mazhabar Sahabi daya hujja ce kai tsaya .
Kuma Ibn Kayyim Jauziyya yana cewa: Lalle fatawoyin sahabbai su suka fi cencenta da a yi riko da su ko da kuwa sun yi sabani idan kuma halifofi hudu suka kasance a wani bangare to babu makawa shi ne daidai, idan kuma mafi yawan su suka kasance a wani bangare to abin da yake daidai yana tare da mafiya rinjaye daga cikin su, idan kuma suka zamo mutum biyu- biyu, to bangaren da Umar da Abubakar suke shi yafi kusa da daidai, idan kuma Abubakar da Umar suka saba to gaskiya tana tare da Abubakar, don lokacin da ya fi kusa da na Manzo to shi ya fi kusa da daidai . Ban san me dan Taimiyya yake nufi da kusancin zamani da na Manzo ba, idan har ya kasance yana nufin kusanci na zamani to dukkaninsu sun kasance a zamani daya tare da Annabi (s.a.w) idan kuma yana nufin kusanci na wajen zama kari a kan abin da ya gabata to Imam Ali shi ya fi lazimtar Annabi fiye da inuwarsa, saboda haka bisa dalilin Ibn Taimiyya ya wajaba a gabatar da maganarsa idan ta ci karo da maganar waninsa.
Bari in ba ka labarin abin da yafi wadannan dadin ji baki daya: Maganar sashin malaman Ahlus-sunna ta zama ma’auni wajen gyara Kur'ani da hadisan Annabi (s.a.w) idan Kur'ani da Sunna suka sabo da fadin wannan imamin: Karkhi daga cikin Imaman hanafiyyawa yana cewa:
Asali shi ne wajabcin yin aiki da maganar Abuhanifa, idan ya dace da fadin Kur’ani da Sunna to shi ke nan idan kuma ba haka ba, to ya wajaba a yi tawilin Kur’ani da Sunna daidai da fadin Abuhanifa. Ustaz Rashid Ridha ya ambaci wannan a ciki tafsirul manar a yayin da yake fassara ayar: "Akwai daga cikin mutane wadanda suke rikar wasu kishiyoyi ba Allah ba" aya ta 165/ Bakara . Sai kuma ga Kushaji shi ma yazo da kwatankwacinta, idan har shi Karkhi ya sanya fikihu hanafiya ma’aunin da za a riga gwada littafi da Sunna da shi, to shi kuma Kushaji halifa Umar ya ba wa hakkin yin ijtihadi alhalin ga maganar Annabi! Ka saurare shi a cikin bahasinsa a kan Imamanci a cikin littafin Sharhin Tajrid a inda yake cewa: Lalle Umar a yayin da yake kan mimbari ya ce: Ya ku mutane abubuwa uku sun kasance a lokacin Manzo kuma lalle na yi hani a kan su kuma ina haramta su sannan kuma zan yi ukuba a kan su, mutu’ar mata da mutuar hajji da kuma hayya ala khairul amal. Sannan Kushaji ya ci gaba da cewa: Lalle wannan bayanin na daga cikin abin da za a yi suka a kansa, sabawa mujtahidi ga waninsa a cikin mas’alolin na rassa ba bidi’a ba ne .
Bayan wannan kuma sai muce da ustaz Faragal: Muna sanya imamanci bayan annabci kuma muna daukar wannan a matsayin abin da Allah ya saukar ne cewa; Allah ya bawa Imami irin cancantar da ya ba wa Annabi, amma dai mu ba ma daukar Imami a matsayin ma’aunin da za a rika auna Kur'ani da Sunnan da maganganunsa, mu mun tafi a kan akasin hakan. Ma’auni shi ne Kur'ani da Sunna, kuma duk abin da ya saba musu nana shi muke da bango, kamar yadda ba ma halarta yin ijtihadi alhali ga Kur'ani a gefe, kamar yadda Kushaji yake ganin Manzo a matsayin wanda yake yin ijtihadi, kuma lalle wannan ya saba da fadinsa madaukaki: "Baya yin furuci da son zuciya face sai in wahayi aka yi masa" ayoyi na 3.4/ Najmi. Duk da haka kimantawa da ba wa Imamai matsayi da muka yi abin mamaki ne a wajensu, a yayin da wasunmu kuma da bakunansu suke ba wa Imamansu matsayin da muka ambata, tare da haka ba a samu wanda zai yi musu nakadi ba, ya a ka yi haka ta faru ya kai Ustaz Faragal? Shin kuwa ka taba yin wata hobbasa kai da makamancinka domin ku tambayi kanku a kan ingancin akidojinku ko kuma ku yi musu nakadi kamar yadda kuke yi wa wasunku? ko kuma ku ne matanen Allah zababbu wadanda ya halatta a gare ku abin da bai halatta ga wasunku ba.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center
Ƙara sabon ra'ayi