Abdullahi Bin Saba’ - 2

Littafin: Hakikar Shi'anci
Maudu’i: Abdullahi dan Saba’ - 2
Wallafar: Sheikh Wa'ili (r)
Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id

2- Muhammad Farid Wajdi a Cikin Da’iratul Ma’arif
Saba'iyyawa mabiyan Abdullahi dan Saba’ wanda ya kai mutuka wajen temaka wa Ali kuma ya raya cewa Ali Annabi ne sannan ya wuce mutuka ya raya cewa shi Allah ne, kuma ya kira wasu daga cikin mutanen Kufa zuwa hakan sai labarin su ya isa ga Ali sannan ya yi umarni da a kona wasu daga cikin su, sannan sai ya ji tsoron kada wasu su yi masa tawaye idan ya kona sauran, don haka sai ya kora Abdullah dan Saba’ zuwa Mada’in, yayin da aka kashe Ali sai ya raya cewa ba Ali aka kashe ba, kadai shedan ne ya bayyana a irin kamar sa kuma wadannan jama’un suna ganin cewa Mahdin da ake sauraro Ali ne ba wani ba, kuma dan bakar mace a da cen ya kasance bayahude ne daga cikin mutane Haira, sai ya bayyana musulunci kuma ya so ya zama yana da matsayi da shugabanci a wajen mutanen kufa, sai ya ce musu, lalle ya samu a cikin attaura cewa lalle kowane Annabi yana da wasiyyi kuma lalle Ali ne wasiyin Muhammad (s.a.w) yayin da suka ji hakan sai suka ce da Ali lalle yana daga cikin masoyanka sai Ali ya daga martabar sa, sannan ya zaunar da shi a karkashin darajar mimbari yayin da labrin gullanci sa ya isa zuwa gare shi sai ya yi kokarin kashe shi, sai Abdullah dan Abbas ya hana shi, sai ya kora shi zuwa Mada’in.
A wannan maganar kuma shi dan Hairan ne ba Sana’a ba kuma shi dan Bakar mace ne kuma lalle Imam Ali ya yaudaru da shi, kuma lalle ya yi da'awar Annabta ga Ali sannan kuma ya yi da’awar allantaka a gare shi!.
Daga nan za a iya tattara wannnan cakude mai ban mamaki, sai dai ta yaya ta za a iya hada tsakanin wannan tafarki mai ban mamaki, kuma ta yaya zai yiwu a lokaci guda mu hada cewa yana jingina masa allantaka kuma yana cewa shi wasiyyi ne, zan bar wadannan kaddare- kaddaren ga hankula da kwakwalen da suka gagara kamar su Muhammad Farid Wajdi da makamantan sa na daga cikin wadanda suke jagorantar takunkumin al’umma a cikin mabambantan al'adu, kuma godiya ta tabbata ga Allah wanda ba wanda ake godewa akan wani abin ki in ba shi ba, kuma kada ka yi gaggawa ya kai mai karatu, da sannu zaka ji wasu abubuwan daga cikin maganganu masu zuwa wadanda suka ci karo da abin da ya gabata.

3- Ahmad Adiyya
Ibn saba’ shi ne shugaban gungun saba`iyyawa daga cikin Shi'a kuma shi ne Abdullah dan Saba’ ya kasance daga cikin yahudawan San’a' kuma ya bayyana musuluncinsa a lalokacin halifancin Usman, kuma ana kiran sa dan bakar mace ya ciratu zuwa madina kuma ya yada wasu maganganu da ra’ayoyi wadanda suka saba da hakikanin musulunci kuma wadanda suka samo asali daga yahudanci da akidar farisawa, wacce ta yadu a yamen, ya bayyana a matsayin wanda yake temakawa Ali kuma ya yi da’awar cewa lalle kowane Annabi yan da wasiyyi kuma lalle Ali ne wasiyin Muhammad kumar yadda ya yi da,awar cewa a cikin Ali akwai wani bangare na Allantaka ya kewaya sasannin Irak yana mai yada manufar sa sai Abdullah dan Amir ya kore shi daga basra sai ya sauka a kufa sannan ya cusawa mutane kin Usman, sannan ya ciratu zuwa Damashaka a lokaci Ma’awuya a cen ne ya hadu da Abi Zarrul Giffafi ya kwadaitar da shi a kan yin tawaye yana mai da’awar cewa mawadata ba su da hakkin tara dukiya, sai aka fitar da shi daga Sham sai ya sauka a Misra sai masu kin Usman suka taru a gefen sa, daga cikin su akwai Muhammad dan Abubakar da Abu Huzaifa, kuma ya kirkiri maganganu da sunan Ali wadanda shi bai fadi ba, kamar da’awar sanin gaibu, bayan shahadar Ali sai ya ce sam ba a kashe shi ba kuma da sannu zai dawo, ta haka ne ya kirkiri tunanin raja’a a cikin Shi'a.
A cikin wannan maganar da Adiyyatullah ya ruwaito akwai abubuwa masu zuwa,
Daga ciki akwai cewa dan Saba’ ya hada wasu akidu daga akidun Yahudawa sai ya cirato su zuwa shi’anci, sannan daga cikin su akwai raja’a (dawowa), sai dai raja’ar a nan ga Ali take, ba ga muhammad ba, kamar yadda yake a wajen abu Zuhra. Daga ciki akwai cewa ya jinginawa Ali wani bangare na alantaka, ba dukkanin ta ba, ta yadda zai iya yiyuwa a hada tsakanin kasancewar sa Allah ta wani bangare da kuma kasancewar sa wasiyin Manzo (s.a.w) ta wani bangaren daban ke nan, daga ciki akwai gano kwazo da iko na banmamaki irin na Abdullahi bin Saba’ ta yadda ya zama dukkanin twayen da a ka yi wa Usman da Ma’awiyah sakamakon aikinsa ne.
4- Da irin wannan salon mai cin karo da juna, kowanne daga cikin Ahmad Amin a cikin Fajril islam da kuma Muhammad Bin Yahya a cikin Attamhid wal bayan fi maktali Usman da kuma Zirkali a cikin A’alam, suka yi bayani.
Ba ina so in tsawaita maka ba ne, domin kowane na baya yana dauka daga wanda ya gabace shi, ba tare da tantancewa ba, al’amarin da ya kai ga samun tsakudedeniya da cin karo a cikin ruwayoyi, zaka same shi a cikin wadannan labaran wani lokaci daga cikin mutanen Haira wani lokacin kuma daga matanen San’a'. A wajen sa Ibn Hazam da Shaharustani da makamancin su kuma, shi dan baker mace ne, a yayin da Ibn Dahir Babagdade a cikin Alfarku bainal furuk da Attabsiratu fiddini yana ganin cewa, dan baka wani mutum ne daban, ba Abdullahi dan Saba’ ba ne.
Kuma a wasu ruwayoyin yana yin da’awar raja’a ga Manzo a yayin da kuma a wasu ruwayoyin yana yin da’awar ne ga Imam Ali kuma awani lokaci yana yin da’awar cewa Ali yana dauke da wani bangare na allantaka, a wata ruwayar kuma shi cikakken ubangiji ne, a wadannan ruwayoyin zamu samu cewa Ali ya kona gullat ba tare da yana jin tsoro ba, a wata ruwayar kuma yana jin tsoron ya kona dan baka, tare da cewa shi Bayahude ne mutumin gari ba wanda lura da ghi, haka muke samun kanmu a cikin wannan tsakudedeniya mai rudani, mafi mihimmanci wannan lamarin a mahangar mu shi ne cewa wani lokaci zaka ga an bayyana shi a matsayin mai yin kira domin bayyana falalar Ali kawai, wani lokaci kuma sai kaga an bayyana shi a mastayin mai harzuka mutane a kan Usman, kuma wanda ya kirkiri mihimman akidojin Shi'a na daga abin da ya shafi wasiyya da sanin gaibun Imamai da kuma ra’ayin raja’a, kuma wadannan al’amuran guda biyu su ne kwaunduwar madui’n. lalle wanda ya kagi abin kunyar Abdullah dan Sa’ba a ya jefi tsuntsu biu da hage daya, kuma wadannan abubwan duga biyu ya nufata:

Na daya: Usman an kashe shi ne sakamakon harzukawar saba’iyyawa ba wai ya yi wasu abubuwan da ya sa mutane suka kyamace shi kuma suka hadu a kan kashe shi ba, alhali a cikin su akwai sahabban Annabi, kamar yadda tarihi ya ambata dalla-dalla. Abin da ake so a ce shi ne wani bayahude ne da ya ke tsananin kin musulunci ya motsa musulmai sai suka bi shi saboda wauta ba tare da wani tunani ba, har sai da suka yi wannan aika-aikar har suka kashe halifa ba tare da ya yi wani laifi ba.
Na biyu: Fadin cewa Akidar Shi'a ba ta da alaka da musulunci ta samo asali ne kawai daga wannan gagararran bayahuden Abdullah dan Saba’, ka ga ke nan Shi'a Yahudawa ne da ba su da sila da musulmai. A bisa kowane hali, wannan rudanin ta hanyar wannan tsararran yanayin na Abdullah dan Saba’ ya sa masu bincike sun fadaka kuma ya kai su ga su idanuwansu a kan wannan tatsuniyyen mutumin, sai suka fitar da ra’ayoyinsu kuma suka karairaya wannan alkadarin sannan suka shelanta wa mutane karyar wannan labarin na kire wanda babu wata hanya da za a iya hada tsakanin abin da sasannin labarin ya kunsa, sai ga hakika ta fara bayyana a hankali a hankali kuma hadafofin aka boye a bayan wannan tatsuniyar suka bayyana a sarari, kuma da sannu zan fada maka ra’ayoyin da yawa daga cikin masu warwara, bayan na gaya maka nawa ra’ayin a kan wannan masa’alar domin mu isa zuwa zuwa bayyanar sura a kan wannan lamarin ko maudu’in.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.comwww.hikima.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center

Ƙara sabon ra'ayi