Hakikanin Sufanci

Hak'ik'anin Sufanci

Sufanci ilimi ne na sanin Allah da aiki da wannan sanin domin samun k'ololuwar yardar Allah, shi ba shi ne ilimin kyawawan halaye ba, ba kuma ilimin mand'ik' ko falsafa ba ne. Sau da yawa wasu mutane sukan ga sufanci kamar wani mummunan abu domin ba su san shi ba, ko kuma sun ga masu da'awar sufanci suna da wasu halaye da ba su dace ba.
Mu sani mafi yawan masu da'awar hanyar sufanci ba su dace masa ba, domin shi yana gabas amma sai suka yi yamma nemansa. Sun kauce masa ne ta hanyoyi mabambanta; wani lokacin ta hanyar haramta wa kai halal, ko kuma akasin hakan wanda yake abu ne mai muni, ko kuma ta hanyar fad'in wasu kalmomin da manyan masana Allah suka fad'a su ma sai suka rik'a maimaitawa ba tare da sun san ma’anar abin da wad'ancan bayin Allah ma'abotan wad'annan maganganun suke fad'a ba.
Don haka ne wasu lokutan ka kan samu sufaye suna yin wasu abubuwan da suka sab'a wa shari'a da sunan sufanci sai wanda bai san shi ba ya d'auka wannan ne sufanci, ko kuma ya ji shad'ahiyyat (na maganganun da a zahiri sun sab'a wa shari’a) ba tare su masu fad'in sun san me ake nufi ba, kamar yadda sukan fassara wasu tawiloli na ayyukan bayin Allah ta hanyar son rai, duk sai wanda bai san mene ne sufanci ba ya yi tsammanin duk wannan yana daga cikinsa.
Mu sani sufanci wani abu ne da ya k'unshi aiki da abin da ya zo daga shari’a, ma’abocinsa yana tafiya ne zuwa ga Allah mad'aukaki, tun daga matakan halaye, da darajoji, da muk'amai, da manziloli.
A halaye yakan samu kansa a kan wani mataki na neman haske da kusancin Allah da narkewa cikin zatinsa, kamar misali ya yi tarbiyyar kansa a kan yin hak'uri da juriya kan barin sab'o, sai ya kasance wani lokaci shed'an da gafala suna fizgarsa zuwa ga sab'on Allah, amma idan ya tuna sai ya koma kan hanyar daidai, har sai barin wannan sab'on ya zama masa jiki, mu k'addara giba ce yake son ya bari ta hanyar tarbiyyar kansa, sai ya kasance wani lokaci yana gafala ya yi giba, amma idan ya samu mallakar kansa ta yadda ba yadda za a yi kuma ya yi giba, sai ya kasance barin wannan sab'on na giba ya kasance masa mallaka, ta yadda duk yadda aka juya kuma ba yadda za a yi ya yi giba, to a nan sai ya taka matakin wannan daraja ta wad'anda ba sa yin giba, kuma ya kasance cikin masu muk'amin wannan haske na barin wannan mummunan sab'o, kuma tun da ya kasance masa mallaka ya zama masa jiki, to a nan sai mu ce yana cikin manzila ta wad'anda ba sa giba.
Kana iya kwatanta wannan da duk wanda ba ya son ya bar wani sab'o, ko kuma yake son ya tabbata a kan wani matsayi na gari kamar matsayin masu hak'uri, da matsayin masu gaskiya, da matsayin masu ambaton Allah, da matsayin masu godiya ga Allah, da sauransu.

Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation
Wednesday, August 05, 2009

Ƙara sabon ra'ayi