Rashin Sabo; Isma

Rashin Sab'o; Isma

Shin Isma Kyauta Ce Daga Allah Ko Kuwa Kokarin Mutum Ne?
An yi bayanin Isma da cewa; ita ce martaba ta koli ta jin tsoron Allah, ko kuma shi ne ganin girman Allah da daukakarsa, ko kuma da ma'anar sanin ilimi cikakke da sakamakon sabo, ko kuwa ludufin Allah (s.w.t) ne wanda yake kusantar da bawa zuwa ga bautarsa. Muhimmin lamari a nan shi ne me ma'abota ilimin sanin Allah suke ganin isma; shin daga Allah take, ko kuwa kokarin dan Adam ne?
A nan masu ilimin sanin Allah suke ganin cewa; daga Allah ne take, kuma shi ne yake ba bawansa da ya san zai kiyaye amanarsa wannan baiwa. Sharhu Aka’idus Saduk: 61.
Wannan kuwa yana nuna mana ke nan asalinta kyauta ce daga Allah, sai dai bawansa Allah yana iya yin amfani da ita don kiyaye umarnin Allah, kamar yadda yana da zabin kin kiyayewa, sai dai Allah yana bayar da ita ga wanda ya so, kuma ya san ba zai saba masa ba. Wannan kuwa yana nuna mana cewa a fili yake cewa; isma ba ta kawar da zabi ga dan Adam. Allah madaukaki ya halicci ma'asumai daga tabon haske, sannan sai ya shirya musu hankali da ruhi mai karfi, wanda da su ne zasu iya sanin abin da yake sirrin samammu, kuma ya yi musu ludufin karkata da sanin halittun sama da kasa, da badinin samammu, don haka sai rayukansu suka kasance karkashin ikon hankulansu. Allawami’ul Ilahiyya: 169. Sannan muna ganin karfafar wannan lamarin a cikin shari'a yayin da Allah ya yi nuni da cewa; ya tsarkake Ahlul Baiti (a.s) Ahzab: 33, kamar yadda ya nuna yadda ya kebanci wasu annabawa (a.s), Almizan: j 16, shafi: 45-48.
Sai dai wasu mutane suna ganin cewa; Idan dai Allah ya ba wa zababbun bayinsa isma ne, to ashe ke nan ba su cancanci yabo a kanta ba? kuma ba ta kasance abin alfahari da kamala garesu ba?
Idan dai isma ta kasance tana hana zababbun bayi yin sabo a matsayinta na kyautar Allah, to ashe ke nan ba zasu iya sabo ba koda kuwa sun so, kuma ke nan ba su cancanci yabo ko lada ba don sun bar sabo?
A nan muna iya cewa: Isma ba a bayar da ita sai ga mutumin da rayinsa ta kasance ta tsarkaka, kuma tana iya karbar wannan amanar ta kiyaye da ita, don haka ashe ke nan mai isma yana cancantar alfahari, kuma kamala ce gareshi. Kuma wannan tsarkakar ruhin da mai isma yake cancantar wannan baiwar ta Allah da ita, tana iya kasancewa kala biyu: Imma ta hanyar gado; kamar yadda 'ya'yan annabawa (a.s) suke gadon kamalar badini da ta zahiri daga iyayensu, domin a ilmance, da ruwayance ya tabbata cewa; kamalar iyaye tana da tasiri ga 'ya'yansu, don haka ne ma aka karfafi aure da na gari, don haka sai ka ga dan rago, ya taso rago, dan sadauki, ta taso sadauki, mai kaifin kwakwalwa da mai dadaddiyar basira, sai ka ga 'ya'yansu sun yo su.
Don haka muka ga Allah madaukaki yana yabon 'ya'yan annabawa (a.s) da wasiyyansu yana mai kiran su zuriya ce sashensu daga sashe. Aali Imaran: 33. Sai dai wannan ba shi kadai ba ne; domin yana bukatar tarbiyyantarwa, da koyarwa, da kuma halittar Allah da hikimarsa ga 'ya'yan annabawa da salihai na gari, don haka rayuwa a irin wadannan salihan gidaje, da kuma al'umma saliha, da abokai salihai, yana iya sanya tasowa cikin tarbiyya ta gari, sannan kuma sai ludufin Allah da kyautarsa da yake ba wa wanda ya so.
Don haka wani lokaci; kokarin da mutum yake yi nasa na kansa, da kuma al'ummar da ya taso, da yanayinta yana daga cikin abubuwan da suke haifar da salihancin bawa da kamalarsa. Idan Annabi (a.s) ko wani wasiyyin Annabi (a.s) ya yi kokari, ya samu kamalar da ta cancanta a samu wannan baiwa ta Allah (s.w.t), ya yaki ransa mai neman yin sabo, to babu wani abu da zai hana Allah ya yi masa wannan baiwa mai daraja.
Misalin Yusuf (a.s) da kissarsa da Zulaiha babban misali ne a nan; Yusuf: 23. Haka nan ma misalin gudun da Annabi Musa (a.s) ya yi daga mutanensa; Surar Kasas: 23-24, 15-20. Kuma akwai misalai masu yawa da suke nuni ga rayuwar samartakar annabawa (a.s) da kokarinsu tun suna kanana har zuwa girmansu. Wadannan abubuwan da wasu suna samuwa ta hanyar halitta, wasu kuwa ta hanyar zabin dan Adam duk suna taimakawa wurin samun wannan falalar ubangiji mai girma. Don haka idan Allah ya duba zukatan bayinsa da kokarinsu sai ya zabi mafifitansu ya yi musu ludufinsa a cikin bayinsa, ya kuma ba su aiki mai girma na isar da sakonsa, da kasancewarsu ma'auni na shiriyar dan Adam a cikin bayinsa.

Amma batun mai cewa: Idan dai isma ta kasance tana hana zababbun bayi yin sabo a matsayinta na kyautar Allah, to ashe ke nan ba zasu iya sabo ba koda kuwa sun so, kuma ke nan ba su cancanci yabo ko lada ba, don sun bar sabo?
Muna iya cewa; Isma ba ta cire musu zabi, kuma duk sa'adda suka so suna iya sabawa, kamar dai hankali ne da Allah ya yi wa bayinsa ludufi da shi, wanda suna iya sanin mummuna da kyakkyawa da shi. Masu hankula sun san cewa zalunci yana da daci, da zafi, kuma ba sa son a yi musu zalunci, amma kuma sai su zalunci wani, suna iya sanin cewa wani abu zai kai su ga cutuwa amma kuma su aikata shi, wannan kuwa yana nuni da cewa wannan ilimi da suke da shi bai hana su zabin kansu ba.
Haka nan ma lamarin annabawa (a.s) ilimin da aka ba su ba ya hana su zabin kansu, kuma ba ya cire musu ikon sabawa, sai dai su suna kokarin ganin ba su saba ba fiye da kowane mutum, kuma Allah madaukaki ya san haka garesu, don haka sai ya zabe su da wannan falalar tasa. Muna iya kawo misalai domin kusanto da tunani ne kawai, misalin wannan a fili yake a kasashe, ta yadda an san ministoci sun san maras kyau, amma ba kowa ake zaba ba sai wanda aka san ba zai ci amana ba a bisa ilimin zahiri, sai dai wannan ba ya hana shi cin amana idan ya so ya ci.
Da shugaba ya san wadanda ba zasu ci amana ba a bisa badini da hakika to da su zai kawo a matsayin ministocinsa, sai dai ilimin mutane takaitacce ne, don haka sai su dogara da zahiri. Amma Allah mahaliccin kowa ya san wanda zai kiyaye har a badini, don haka ba ya zabar mutum sai wanda ya san yana da kiyayewa a zahirinsa da badininsa, sannan sai ya zabe shi a matsayinsa jakadansa, kuma ya ba shi baiwa da falala da ilimi maras iyaka.
Da wannan ne zamu ga cewa a fili yake babu wata isma da take hana zabi ga ma'asumi, kuma babu ismar da take kara zube ba tare da sanin tsarkin ruhin zababbun bayi ma'asumai ba. Don haka sun cancanci a girgiza musu, kuma a yaba musu, da wannan ne ma muka ga Allah madaukaki a cikin ayoyin Kur’ani mai girma yana girmama su girmamawa! Yana nuna kimar ayyukansu sakamakon dagewarsu kan biyayya gareshi dagewa!.

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation
Sunday, September 13, 2009

Ƙara sabon ra'ayi