Son Ahlul Baiti (a.s)

Son Ahlul Baiti (A.S)

Madaukaki ya ce: “Ka ce ni ba na rokon ku wani lada a kansa sai dai soyayyar dangi na kusa kawai”. Surar Shura: 23. Mun yi imani cewa bayan wajabcin riko da Ahlul Baiti (A.S), wajibi ne a kan kowane musulmi ya dabi’antu da sonsu da kaunarsu domin a ayar da aka ambata an takaita abin da ake nema daga mutane da nuna soyayyar makusantansa (A.S). Ya zo ta hanyoyi masu yawa da cewa; Son su alamar imani ne kin su kuma alamar munafinci ce, kuma duk wanda ya so su ya so Allah da manzonsa, wanda kuma ya ki su, to ya ki Allah da Manzonsa (S.A.W).

Hakika son su wajibi ne daga laruran addini da ba ya karbar jayayya ko kokwanto. Domin dukkan musulmi sun hadu a kan hakan duk da sabanin mazhabobinsu da ra’ayoyinsu, in ban da kadan daga wasu jama’a da aka dauke su a matsayin masu gaba da Zuriyar Manzon Allah wadanda aka sanya musu sunan “Nawasib” wato wadanda suka kulla gaba a kan Zuriyar Annabi (S.A.W), don haka ne ma ake kirga su a cikn masu inkarin abin da yake wajibi na addinin musulunci tabbatattu, wanda kuma yake karyata larurar Addini ana kirga shi a cikin masu karyata ainihin sakon musuluncin koda kuwa a zahiri ya yi furuci da kalmar shahada, saboda haka ne kin Ahlul Baiti (A.S) ya zama daga alamomin munafunci son su kuwa ya zama daga alamomin imani kuma don haka ne kinsu ya zama kin Allah (S.W.T) da manzonsa (S.A.W).

Kuma babu shakka Allah (S.W.T) bai wajabta son su ba sai don su sun cancanci soyayya da biyayya ta bangaren kusancin su da Allah da manzonsa, da tsarkinsu, da nisantar su ga shirka da sabo, da kuma dukkan abin da yake nisantarwa daga karimcin ubangiji da yardarsa. Ba zai taba yiwuwa ba a suranta cewa; Ubangiji ya wajabta son wanda yake aikata sabo ko kuma wanda ba ya bin sa, domin shi ba shi da wata kusanci ko abotaka da wani, mutane a gurinsa ba komai ba ne sai bayi ababan halitta masu matsayi daya, kadai mafificinsu a gurin Allah shi ne mafi tsoronsu gareshi. Duk wanda ya wajabta son su a kan mutane baki daya to babu makawa ya zamanto mafi takawarsu, kuma mafi darajarsu baki daya, ba don haka ba, da waninsa ya fi cancantar wannan soyayyar, kuma da ya kasance kenan Allah yana fifita wasu mutane a kan wasu a wajabcin so da biyayya haka nan kawai ko da wasa ba tare da cancanta ko daraja ba.Matsayin Imamai (A.S)

Mu ba mu yi imani ga Imamanmu (A.S) da abin da ‘Yan gullat[1] da ‘Yan Hululiyya[2] suka yi ba, “Kalmar da take fita daga bakunansu ta girmama”. Surar Kahf 5. Imaninmu game da su shi ne cewa su mutane ne kamarmu, suna da abin da yake garemu, kuma abin da ya hau kanmu ya hau kansu, sai dai kawai su bayin Allah ne ababan girmamawa, Allah ya kebance su da karamarsa, kuma ya so su da soyayyarsa, domin suna da karamarsa, kuma ya ba su wilayarsa, domin su suna kan mafi daukakar daraja da ta dace da dan Adam na daga ilimi, da takawa, da jarumta, da karimci, da kamewa, da dukkan kyawawan dabi’u mafifita, da siffofi abin yabo, kuma babu wani dan Adam da zai yi kusa da su a kan abin da aka kebance su da shi.

Da wannan ne suka cancanci su zamo Imamai masu shiryarwa kuma makoma bayan Annabi a cikin duk abin da yake na addini na bayani da shar’antawa, da kuma abin da ya kebanta da Kur’ani na daga tafsiri da tawili.

Imaminmu Ja’afar Assadik (A.S) Ya ce: “Duk abin da ya zo muku daga gare mu daga abin da ya halatta bayi su siffanta da shi, ba ku kuma san shi ba, ba ku fahimce shi ba, to kada ku yi musun sa, ku mayar da shi gare mu, amma abin da ya zo muku daga garemu wanda bai halatta bayi su siffantu da shi ba, to ku yi musun sa kada ku mayar da shi zuwa gare mu.Imamanci Sai Da Nassi

Mun yi imani cewa lmamanci tamkar Annabci ne ba ya kasancewa sai da nassi daga Allah madaukaki a harshen Manzonsa, ko harshen lmamin da ya aka sanya shi ta hanyar nassi idan yana son ya yi wasiyya da lmamin bayansa, hukuncin lmamanci a nan tamkar hukuncin annabci ne ba tare da wani bambanci ba, mutane ba su da ikon wani hukunci a kan wanda Allah ya ayyana mai shiryarwa ga dukkan mutane, kamar yadda ba su da hakkin ayyana shi, ko kuma kaddamar da shi, ko zabensa, domin mutumin da yake da tsarki da karfin daukar nauyin lmamanci baki daya, da kuma shiryarwa ga ‘yan Adam gaba daya, wajibi ne kada a san shi sai da shelantawar ubangiji, kuma ba a ayyana shi sai da ayyanawarsa.

Mun yi imani cewa Annabi (S.A.W) ya yi wasiyya da halifansa kuma shugaban talikai bayansa, sai ya ayyana dan amminsa Aliyyu Dan Abi Dalib Amiri ga musulmi, kuma amini kan wahayi, lmami ga halittu, ya ayyana shi a gurare da dama, kuma ya nada shi, kuma ya karba masa bai’a a kan shugabancin muminai ranar Gadir yana mai cewa: “A saurara a ji! Duk wanda na kasance shugabansa ne to wannan Ali shugabansa ne, Ya ubangiji! ka so wanda ya so shi, ka ki wanda ya ki shi, Ka taimaki wanda ya taimake shi, ka tozarta wanda ya tozarta shi, kuma Ka juya gaskiya tare da shi duk inda ya juya’’.

Daga cikin wuraren farko da ya yi wasiyya da imamancin-sa akwai fadinsa yayin da ya kira danginsa makusanta ya ce: “Wannan shi ne dan’uwana, kuma wasiyyina, kuma halifana a bayana, ku ji daga gareshi ku bi shi”. A yayin nan kuma shi yana yaro bai balaga ba. Kuma ya maimaita fadinsa da yawa da cewa: “Kai a gare ni tamkar matsayin Haruna ga Musa ne, sai dai babu Annabi a bayana”. Da sauran ruwayoyi da ayoyi masu girma da suke nuni da tabbatar shugabanci na gaba daya gare shi kamar ayar:

"Kadai cewa Allah shi ne majibancinku da Manzonsa da Wadanda suka yi imani wadanda suke ba da zakka suna masu ruku’u". Surar Ma’ida: 55. Wannan ta sauka ne game da shi yayin da ya yi sadaka da zobe yana cikin ruku’u. Wannan dan littafin ba zai iya bin diddigin dukkan abin da ya zo na daga ayoyin Kur’ani da ruwayoyi ko bayaninsu ba game da wannan maudu’i[3].

 Sannan shi ma ya yi wasiyya da Imamancin Imam Hasan da Imam Husain (AS), shi kuma Husain (A.S) ya yi wasiyya da imamancin dansa Aliyyu Zainul Abidin (AS), haka nan dai Imami ke bayar da wasiyyar imamin da zai zo bayansa har zuwa kan na karshensu kamar yadda zai zo.Adadin Imamai

Mun yi imani da cewa Imamai wadanda suke da siffar Imamancin gaskiya su ne makomarmu a cikin hukunce-hukuncen shari’a, wadanda Annabi (S.A.W) ya yi wasiyya da su da sunayensu gaba daya, sannan wanda yake gabata yana wasiyya da mai biye masa.

Imam Al-Mahadi (AS) Shi ne Hujja a zamaninmu kuma boyayyen da ake sauraro, Allah ya gaggauta bayyanarsa ya saukaka mafitarsa, zai zo domin ya cika duniya da adalci bayan an cike ta da zalunci.Imam Mahadi (A.S)

Hakika albishir da bayyanar imam Mahadi (A.S) daga ‘ya’yan Fadima (A.S) a karshen zamani domin ya cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci ya tabbata daga Annabi (S.A.W) ta ruwayoyi masu yawa, kuma dukkan musulmi duk da sabanin mazahabobinsu sun ruwaito hadisai game da shi.

Fikirar samuwar imam mahadi (A.S) ba wani sabon abu ba ne da Shi’a suka kago shi saboda iza su da yaduwar zalunci ya yi zuwa gare shi, har suka yi mafarkin bayyanar wani wanda zai zo ya tsarkake kasa daga daudar zalunci, kamar yadda wasu masu neman kawo rikici da rudani marasa adalci suka raya. Ba don tabbatar akidar Mahadi (A.S) daga Annabi (S.A.W) ba, ta yadda dukkan musulmi suka san ta kuma ta kafu a zukatansu suka yi imani da ita, da masu da’awar mahadiyyanci a karnonin farko kamar kaisaniyya, da Abbasawa, da wasu daga Alawiyyawa, da sauransu, ba su iya yaudarar mutane ba ta hanyar samun dama da amfani da wannan akida wajen neman mulki da shugabaci, domin sun sanya da’awar mahadiyyancinsu ta karya ta zama hanyar tasiri a kan jama’a gaba daya da kuma shiga rayukan jama’a.

Mu tare da Imaninmu da ingancin Addinin musulunci, kuma cewa shi ne cikamakon addinan Ubangiji, kuma ba ma sauraron wani Addini da zai zo domin gyara dan Adam, hada da abin da muke gani na yaduwar zalunci da yawaitar fasadi a duniya, ta yadda ba zaka iya samun masakar tsinke ba ga adalci da gyara a kasashen duniya, tare da kuma abin da muke gani a fili na nesantar musulmi daga addininsu, da kuma ajiye hukunce-hukuncen musulunci da dokokinsa a gefe guda a dukkan kasashen musulmi, da kuma rashin lizimtuwarsu da koda daya daga dubban hukunce-hukuncensa, amma duk da haka ba makawa mu saurari budi da farin ciki da dawowar Addinin musulunci da karfinsa da iyawarsa wajan gyara wannan duniyar da ta dulmiya cikin takurawar zalunci da fasadi.

Sannan kuma ba zai yiwu ba musulunci ya dawo da karfinsa da jagorancinsa a kan dan Adam baki daya ba, alhalin yana kan wannan halin da yake ciki a yau da gabanin yau na daga sabanin mabiyansa a dokokinsa da hukunce-hukuncensa da ra’ayoyinsa game da shi, tare da wannan hali da suka samu kansu a ciki a yau da ma kafin yau na bidi’o’i da canje-canje a dokokinsa, da bata a cikin da’awoyinsu.

Na’am ba zai yiwu ba Addini ya koma ga karfinsa sai dai idan mai gyara babba ya jagorance shi, yana hada kansu, yana kuma rushe abin da aka raba masa na daga bidi’o’i da bata, tare da taimakon Ubangiji da ya sanya shi shiryayye mai shiryarwa, wanda yake da matsayi mai girma na Shugabanci na gaba daya, da kuma iko mai sabawa al’ada, domin ya cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci.

A takaice; Dabi’ar yanayin fasadi a duniyar dan Adam ta kai matuka a baci da kuma zalunci, duk da kuwa imani da ingancin wannan addini da cewa shi ne cikamakon addinai, wannan al’amari ya hukumta sauraron mai wannan gyara domin tseratar da duniya daga abin da take ciki. Saboda haka ne dukkan bangarorin musulmi suka yi imani da wannan sauraron, kai har da ma wadanda ba musulmi ba, sai dai kawai bambancin da yake tsakanin mazhabar Imamiyya da waninta shi ne, ita mazhabar imamiyya ta yi imani cewa wannan mai gyaran mutum ne ayyananne wanda aka haife shi a shekarar hijira ta 256, kuma bai gushe ba yana raye, kuma shi dan imam Hasan Askari ne mai suna “Muhammad” (A.S). Wannan kuwa saboda abin da ya tabbata daga Annabi (S.A.W) da kuma imamai (A.S) game da alkawarin zuwansa, da haihuwarsa, da boyuwarsa. Bai halatta ba Imamanci ya yanke a wani zamani daga zamuna koda kuwa Imami ya kasance boyayye ne, domin ya bayyana a ranar da Allah ya yi alkawari, wanda kuma wannan yana daga cikin asiran Ubangiji da babu wanda ya san su sai shi.

Kuma rayuwarsa da wanzuwarsa ba komai ba ne sai mu’ujiza ce da Allah ya sanya domin ba ta fi mu’ujizar kasancewarsa imami ga mutane yana dan shekara biyar ba a ranar da mahaifinsa ya koma zuwa ga Ubangiji Madaukaki, kuma ba ta fi Mu’ujizar Annabi Isa (A.S) girma ba da ya yi magana da mutane yana cikin shimfida yana jariri, kuma aka aike shi Annabi ga mutane.

Tsawon rayuwa fiye da dabi’a fannin likitanci bai musanta shi ba, kuma ba ya ganinsa mustahili, sai dai shi likitanci bai kai matsayin da zai iya kara tsawon rayuwar mutum ba. Idan kuwa likitanci ya gajiya a kan haka to Allah mai iko ne a kan komai. Kuma tsawaita rayuwar Annabi Nuhu (AS) da wanzuwar Annabi Isa (AS) ya faru kamar yadda Kur’ani ya bayar da labari, idan kuwa mai shakka ya yi shakku game da abin da Kur’ani ya ba da Iabari game da shi, to sun yi hannun riga da Musulunci.

Yana daga abin mamaki musulmi ya tsaya yana tambaya game da yiwuwar haka alhalin yana da’awar imani da Littafi Mabuwayi.

Daga cikin abin da ya zama dole mu ambace shi a nan shi ne cewa; sauraron ba yana nufin musulmi su nade hannayensu game da al’amuran da suka shafi Addininsu ba ne, da kuma abin da ya wajaba na taimakonsa, da jihadi a tafarkinsa, da riko da hunkunce-hukuncensa, da yin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna. Musulmi har abada abin kallafawa ne da aiki da abin da ya sauka na daga hukunce-hukuncen Shari’a, kuma ya wajaba a kansa ya yi kokarin sanin su ta fuska ingantacciya, kuma wajibi ne a kansa ya yi umarni da kyakkyawa, kuma ya yi hani da mummuna gwargwadon daidai yadda zai iya “Dukkanku makiyaya ne kuma kowannenku abin tambaya ne game da abin kiwonsa.” Saboda haka bai halatta gareshi ba ya takaita wajibansa don yana jiran mai kawo gyara Imam Mahadi (A.S), wanda yake mai shiryarwa da aka yi albishir da shi, domin wannan ba ya saryar da takalifin da aka kallafa, ba ya jinkirta aiki, ba ya sa mutane su zama karazube kamar dabbobi.

[1] - Masu fadin cewa imamai ubangizai ne ko kuma su ba ma mutane ba ne.

[2] - Masu imani da shigar Ruhin Ubangiji madaukaki jikin imamai.

[3] - Koma wa Littafin Sakifa na mawallafin wannan littafin domin karin bayani da sharhi ga wasu ayoyin kur’ani.

 

Hafiz Muhammad Sa'id

hfazah@yahoo.com

Haidar Center For Islamic Propagation

Ƙara sabon ra'ayi