Mushafin Fadima
Mushafin Fadima
Mece Ce Gaskiyar Mushafin Fadima (a.s)
Akwai maganganu masu yawa da ake yi game da abin da ake kira da mushafin Fadima (a.s) wanda ya zo a cikin ruwayoyi, kuma makiyan Shi'a sun yi amfani da wannan wurin ganin sun bata sunan su ta hanyar tuhumar su da cewa; suna da wani Kur'ani mai suna mushafu Fadima. Sai dai wannan tuhuma ce ta bata suna, maras wata kima da tushe da ba ta da asasi, domin da zarar mai bincike ya koma wa ruwayoyin Ahlul Baiti (a.s), to zai samu abin da yake karyata wannan kagen cikin sauri, sai dai duk da haka an samu wasu masu taurin kai da ba sa iya barin nuna kiyayyarsu ga tafarkin alayen manzon Allah har abada da suka ci gaba da wannan kagen.
Mushafi a lugga yana nufin: Tattararrun takardu, kamar yadda farra'u ya kawo; Islahul Mandik: 354, da kuma Sihah: 4/1384, Jauhari. Abul Hilal yana cewa: Banbanci tsakanin littafi da mushafi shi littafi yana iya kasancewa da takarda daya rak, amma mushafi ba ya yiwuwa sai da takardu masu yawa.
Mushafin Fadima (a.s) wani lallashi ne da ta'aziya da sayyidina Jibril (a.s) yake yi wa Fadima (a.s) da ta kasance tana jin maganarsa bayan wafatin manzon Allah (s.a.w), kuma imam Ali (a.s) yana rubutawa, sai aka ambaci wannan tattararrun maganganun da take ji da Mushafin Fadima (a.s). Kuma wasiyyan manzon rahama (a.s) kuma halifofinsa sha biyu tun daga kan imam Ali (a.s) har zuwa imam Mahadi (a.s) sun kasance suna gadon wannan mushafin, sannan yana daga cikin alamar Imami (a.s) ya nuna wannan mushafin daga cikin abubuwan da suke gunsa masu nuni da gadon mushafin ga Imami (a.s), Alkhisal: 528.
Kuma shi ne littafin da musulmi suka rubuta na farko bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) domin sayyida zahara (a.s) ta rasu 3 Jimada Ulam 11, H, kuma ba a rubuta wani littafi ba a cikin wannan dan tsakanin sai mushafinta, kuma wannan yana nuna mana a fili cewa; lamarin ba shi da wata alaka da Kur'ani kamar yadda masu gaba da gidan Annabi (s.a.w) suke neman likawa.
Sannan babu mamaki don Jibril (a.s) ya yi mata magana kamar yadda yake yi wa Maryam, domin ita ma Muhaddisa ce, ba Annabi ba, Biharul Anwar: j 39; 55, da kuma 39; 79. Mala'ikun Allah sukan yi wa bayinsa magana kamar yadda suka yi wa babar Musa (a.s) da matar Annabi Ibrahim Sara, da makamantansu. Don haka babu mamaki ga mai basira don sun yi wa shugabar matan talikai magana wacce ta fi wadancan matan duka kima da matsayi wurin Allah madaukaki, Ilmuddiraya: Subhani; 20.
Mushafin Fadima (a.s) ya kasance ne kamar yadda ruwayoyi suka zo cewa; Fadima (a.s) ta samu kanta cikin matukar damuwa bayan wafatin babanta, sai Allah ya umarci mala'ika Jibril da ya rika yi mata ta'aziyya, yana ba ta labarin inda babanta yake, da matsayin da ya samu, da kuma makomarta da ta 'ya'yanta har zuwa ranar kiyama. Sai ta gaya wa imam Ali (a.s), sai ya ce: Idan kika sake jin wannan maganganu ki sanar da ni. Sai ta sanar da shi yayin da ta ji, sai ya kasance yana rubuta wannan zancen. Babu wani abu na haram, ko halal, a cikinsa, abin da yake cikinsa labari ne na abubuwan da zasu wakana kan zuriyarta har kiyama ta tashi, da kuma halin da babanta yake ciki, wannan shi ne mushafin Fadima (a.s). Kafi: j 1, s: 241, da 240. Basa’irud Darajat: 177. Ruwayoyi masu yawa sun zo suna nuna siffofin wannan mushafin Fadima kamar haka:
1- Ya ninka Kur'ani sau uku yawa
2-Babu ko aya daya ta Kur'ani a cikinsa
3-Babu ko harafi daya na Kur'ani a cikinsa
4-Shi ba Kur'ani ba ne
5-A cikinsa akwai dukkan labarun abubuwan da zasu faru har zuwa kiyama ta tashi
6-Yana hannun imamai daga zuriyar (a.s) Fadima 'yar manzon Allah (a.s)
Wadannan bayanai masu yawa da makamantansu sun zo a cikin littattafai kamar haka; Basa’irud Darajat: 152, 156, 158, 161, 159, 160, 177, 173, da A’alamul Wara: 285.
Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation
Thursday, September 24, 2009
Ƙara sabon ra'ayi